Sashe 17
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raihana ce a gaba don haka ita ta tura qofar falon,sanyin ac gauraye da qamshin turarensa da air freshner ta gauraye falon,kida ne ke tashi a hankali can qasa,waqar hamisu breaker ce mai taken a duniya ke kikazam farincikina,yana zaune qasan carfet bayanshi jingine da kujerar falon,sanye yake da wani irin yadi mai kyau na maza ruwan toka,wanda aka yiwa dinkin riga three quater mai dogon hannu da dogon wando,qafafunsa a miqe suke harde da juna,yayin da ya tallafe qeyarsa da duka hannayensa biyu da ya sarqesu cikin juna,qarar bude qofar ta sanyashi bude lumsassun idanunsa ya saukesu fes a kansu su duk biyun,raihana ta janye idonta a hakali tana jin wani nauyi,rumana dake kallonsa tana ganin ya sake sauya mata ya sake wani kyau tare da yin fresh ta matso bayan raihana ta rada mata
"Don Allah kallemin ya rayyan,ya saki zama wani handsome ko sisi" murmushi tayi har fararen haqoranta suka bayyana,idanunta suka sake sauka kan rayyan wanda har yanzu su yake duba,sai ta sake dauke idon nata tana gyadawa rumanan kai
"Idan kun kammala gulmar ku shigo kada ku gayyatomin sauro ya cikan daki" ya fada a hankali sannan ya maida idonshi ya sake rufewa tamkar bashi yayi maganar ba.
Mintina biyu kafin waqar ta qare ya bude idon nasa,yasa hannunshi ya dauki wayarsa ya kashe,rumana da waqar ta tsumata,ji take tamkar rayyan din ke mata ta dubeshi tana dariya
"Yaya,a ina ka samo wannan waqar?,kai da bansanka da jinsu ba"
"Nima ji nayi ana ji nace a turan ko nayi laifi?" Kai ta kada"a'ah,dama don dai basu dameka bane,amma akwai kalamai masu tayar da tsumin qauna cikin waqoqin"
"Na yadda da wannan" ya fadi yana duban idanunta wanda hakan ya sake haifar mata da wata iriyar qauna tasa.
"Gashi ku dubamin wannan" ya fada yana tura musu wasu takardu tare da duban raihana wadda tunda suka shigo bayan ta samu gu ta zauna ta dauki daya daga cikin litattafanshi da suke zuwa daukar karatu da daddare gun wani malamin addini ta soma dubawa,ajjiye littafin tayi sannan ta dauki takarda daya,yayin da rumana ma ta dauki daya tana dubawa,raihana ce ta soma dago kai,sai suka hada ido,wani nauyi taji ya saukar mata,ta yaada kanta gefe tana cewa cikin sassanyar muryarta
"Kamar takardar kamfani ko ta neman kazo kayi aiki tare da su?"
"Eh nima ta hannuna haka ne" inji rumana tana sake jujjuya takardar dake hannunta.
Qafafunsa ya janye ya tanqwashesu sannan ya zauna sosai
"Bayan dawowata na samu aike daga kamfanini daban daban da suke so nayi aiki da su,to duka a ture tasu,cikin guda biyun nan nakeso na zabi daya don sunfi kwanta min" shiru sukayi na dan sakwanni kowacce da kalar nata tunanin,rumana ce ta fara magana bayan ta duba takardar dake hannun raihana ta duba itama ta karbi tata ta duba
"Nikam yaya inaga ka dauki wannan kafanin na alj suraj dauda,naga albashin da suka ce zasu baka yafi na wannan kamfanin yawa ko?" Ta qarashe maganar tana dubanshi
"Yayi my angel,to kefa raiha?,bakice komai ba" murmushi tayi don shi kadai ke kiranta da sunan,tilas sai ya maida ta 'yar qauye dai
"Nidai inaga yaya da farko ka fara yin istihara kamar yadda annabi ya fada mana yayin da duk ka tunkari wami lamari da kake neman zabin daya daga ciki ya faru gareka,idan yaso ko zuwa kwanaki uku ko hudu idan Allah ya kimsa maka saika zabi daya daga ciki din,ko kuwa sisi?" Ta fadi tana duban rumana,dariya rumanan keyi
"Yes my sisi,kinga fa kinyi hange mai kyau,hakan yayi yaya rayyan,shine daidai" inji rumana,sosai shawarar tata ta burgeshi,ya dinga kada kai yana lumshe ido,wani abu ya dinga masa tasiri da yawo tsakiyar kanshi,hakan ya sanya ya basu damar tafiya.
Kan gado yayi watsi da takardun kamar wasu marasa amfani kana ya fada saman gadon da ruf da ciki sai kuma ya juya ya koma rigingine yana kallon p.o.p din saman dakin
_irin matan da suke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu_
Daya daga cikin maganganun suka fado masa,sai ya mirgina ya koma barin hannun damanshi tare da yin ta'awizi wai ko shedan ke son ribatarsa
_don bazanyi saken da zata subucemin ba,ina tunanin da wuya in samu kamarta idan na rasata_
Ya sake jin maganar cikin kunnensa kamar a lokacim amir din ke fada
"Don me zaka bari wani ya dauke kadara mai tsada din daga gabanka kana kallo?,don me zaka bari wani ya dauke ta bayan irinsu ne ke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu?,idonka ne a rufe rayyan?" Yaji zuciyarsa na karanta masa,rintse idonsa yayi yana son hanawa zancan samun gurbi a zuciyarsa balle yaci gaba da yi masa tasiri,tura kansa tayi qasan filo yana girgiza kansa,amma zuciyarsa bata ci gaba da yi masa kuwwa da magiya ba.
Cikin qanqanin lokaci ya wani firgice,tamkar ba sadaukin namijin nan ba rayyan,wani irin rudani ya shiga lokaci guda,bai taba jin abun ya ta'azzarar masa ba irin yau,bai taba daukar haka zuciyarsa ta dauki lamarin ba sai yau da zuciyarsa ke neman jigatashi,wanda a qarshe saman carfet yayi barci a maimakon kan gadonsa,ko sallar nafilar daya sabayi kafin ya kwanta bai samu damar yi ba balle a kai ga sanya kayan bacci
************
Wani iri ya tashi washegari,abinka da wanda bai saba saka abu cikin ranshi ba balle ya sashi damuwa,tunda yake bai taba shiga wata damuwa ba,ko yaushe rayuwa na tafiyar masa daidai ba tare da cin karo da wata matsala ba.
Qarfe tara yunwa ta addabeshi don jiya bai samu yaci wani abincin kirki ba,jallabiya ya zura ya saka silifas dinsa ya biyo ta zauren gidan ya wuce tsakar gidan kai tsaye inda kitchen dinsu yake.
Daidai lokacin tana tsaye cikin kitchen din tana soya qosai bayan ta gama dama kunun tsamiya ta juye a flask wanda tun qarfe takwas almajirinsu yazo ya kai mata markaden qosan saboda rana daidai ne bata yiwa abba,kasancewarsa mutum mai son kunu da qosai,da wuya ka ganshi yasha tea,tea sai su,don ko rayyan sai dare idan zai kwanta yakesha black tea,wanda ya zame masa qa'ida tunda yaje england ya dawo,daga gefan gas din littafinta ne ajjiye tana suyar tana bitar karatun nata saboda qarfe goma takeson fita don sha daya suna da test,hakan ne yasa kan ta fara aikin ma ta gama shirinta cikin riga da skert ta dora afron akai,wanda indai ta sanyasu to sai ta dora musu after dress.
Tun kafin ya qaraso ya gane ita ce,sai ya tsaya daga nesa ya goye hannayensa a qirji yana monitoring duk wani movements dinta,tana gama saka qosai sai ta dawo kan littafin,wani lokaci idan wani abun ya kakare mata takan dan tsaya ta bubbuga qafafu tare da yarfe hannu kota dafe goshinta,murmushi ya saki ganin tana abu kamar yadda rumana keyi sometimes,ashe itama shagwababbiyar ce,lallai dabi'a naso take.
A hankali ya qaraso bakin qofar kitchen din yayi tsaye yana qare mata kallo,komai nata natural ba artificial ba,tun daga yanayin fatarta kawai ya isa ka gane hakan,wanda sau da yawa wasu Allah na musu baiwar fata irin nata wato chaculet colour black beauty sai su bata ta,su butulcewa Allah su dauki kururuwar iblis su dinga bleeching suna dashewa,wanda duk mai wannan dabi'ar Allah yayi fushi da ita,kuma burin shaidan da yaci a kanta ya cika kenan,don dama alqawari yayi sai ya samu munyi hakan.
"Alhamdulillah" ta fada a hankali tana rufe littafin bayan da ta tabbatar karatun ya zauna yadda takeso,har ta kammala suyar yana tsaye ba tare data sani ba,don ta juyawa qofa baya ne,sai da ta kashe gas din ta juyo da niyyar daukar flask da zata zubawa abba nasa taga mutum wanda bata tantance ko wane ba ta saki ihu tare da ja baya da sauri jikinta na rawa,ga zatonta ma rumana ce da salon taikanarta sai taga rayyan ne,kunya da tsoro suka rufar mata
"Matsoraciya kawai,idan abun tsoron ne ma wannan ihun naki ai ya isa yasa ya cinyeki baki daya"
"Ina kwana ya rayyan" ta gayas da shi duk da har yanzu qirjinta bai daina bugawa ba kanta a qasa
"Lafiya raihana naji ihunki?" Cewar ummu data nufo kitchen din,ya dan kauce ya bata hanya
"Waifa daga gani na ta saki wannan ihun"
"A'ah.....hala dai bakayi mata sallama ba" sai ya dan sosa kanshi sannan yace
"Eh"
"Atoh,kaga laifinka ne kenan,kada ka sake haka kaji ko?"
"To ummu" itadai bata ce komai ba tana ta hidimar zubawa abba qosanshi ta kammala ta miqawa ummun,tasa hannu ta amsa tana sanya mata albarka sannan ta juya ta fice daga kitchen din ta barsu nan.
*mrs muhammad*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Manzan Allah S A W yace"kada ku hana bayin Allah (mata)zuwa masallacin Allah*
____________________
*Babi na sha bakwai*
Kafin ya kai ga tallafa mata tuni ta tallafi kanta ta hanyar riqe handle din qofar ta tsaya qam,sai ya qaraso gabanta ya ja birki yana dubanta,kasa tsaiwar tayi kawai tabi jikin bango ta sulale ta zauna dirshan,kai ta hada da gwiwa sannan ta saki wani kuka mai dauke da siririn sauti
"Ya ilahal alamina,shin ko dai laifinta ne?,ko tayi wani abu ne daya fallasata,wanda ya janyo rayyan ke mata wannan maganar mai barazanar tarwatsa mata qwaqwalwa,wannan wace iriyar magana ce mara makama?" Take zancan cikin zuciyarta,tsayawa kawai yayi harde da hannayensa yana kallonta,duk da cikin zuciyarsa yana jin babu dadi amma baya jin zai iya haqura ta subuce masa,saboda muddin hakan ta faru ya tafka asarar da har abada zai dade yana jinta cikin zuciya da gangar jikinsa,asarar da baya fatan ace ta sameshi,duk wannan kukan tashin hankalin da bore na dan lokaci ne kuma mai wucewa ne,amma kuma rashinta fa?.