Sashe 44
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuni har ta kammala hada kayanta cikin jakarta,rumana ta kama hannunta tana dubanta
"Haba sisi,kinsan fa halin ya rayyan sarai tun ba yau ba,kada ki bari a ganmu a rana ayi mana dariya haba sisi na" murmushin qarfin hali tayi
"Wallahi ko a jikina,dama ai na gaya miki tun safe yau zan tafi bayan magariba,ina da abubuwan yi da yawa a gida,ya rayyan kuma kada ki damu ko saka wani abu,tunda na fito daga gida na yakejin haushina,qila ya aza laifi na ne" ta fadi haka ne don ta kawar da hankalin rumanan daga zargin wani abu,babu yadda bata kada ba tace sam itama hankalinta yayi gida tana so taje taga ummu,hakanan ta daukar mata jakar
"A'ah sisi ajjiye,har yanzu fa patiente ce ke" harara ta watsa matq
"Kada ki sake cewa komai idan baso kike na sake tunzura ba" dariya tayi
"Allah ya baki haquri tawan", babu kowa cikin falon,da alama ya gama cin abincinsa ya dauke diyarsa sun haura sama,haurawa saman itama rumanan tayi bayan ta ajjiye kayan tana fadin" ina zuwa"mintina kusan biyar sai gata ta dawo dauke da key din motar rayyan din
"Muje parking space na bude miki ku zauna kan ya sauko,shike bata islaha wallahi,yanzun sai ya lallabata tayi bqcci sannan zai fito"
"Idan bai shagwabata ba ke kuwa wa kike so ya shagwaba,nikam ina goyon baya wallahi"
"Eh dama ai jirginku daya ke da shi,kun samu aiki kam,indai islaha ce dama
Haka take so ai" da wannan hirar suka qarasa wajen motar ta bude matq,tare suka shige sannan rumana ta kunna musu a.c,sanyinta ya fara ratsa mitar tare da qamshin daddadan turaren take manne da motar gauraye da qamshin turaren mamallakin motar,hira suka ci gaba da tabawa rumanan najin kamar ta daure qafafun raihanan ta hanata tafiyar.
Sai da ya bata kusan minti talatin sannan ya fito,jallabiya ce a jikinsa ruwan toka mai turuwa,da alama har wanka ya sauya ya barsu zaune cikin mota,fita tayi daga motar tana duban raihanan
"Sisi ki gaida gida Allah ya qara zumunci,amma fa ki sani,Allah sai na rama duk randa kikayi aure" murmushi tayi
"Dadin abun islaha na nan ai" hararta tayi
"Au,ai dama na sani tuni faadaata ta koma hannun ta ai,ni bansan ya zamu qarke da ita ba idan ta tashi taga baki nan,ki gaida min ummuna da abba"
"Zasuji" ta fada itama tana jin kewarsu,ta dubi rayyan dake gyara zamansa yana qoqarin kunna motar
"Dear,sai ka dawo,a tuqamin sisi na a hankali" wani dan qaramin murmushi ya sakar mata sannan yayi kissing hannunta dake kan window din qofar,sannan tayi baya ya tada motar suka fice.
Tsit cikin motar tayi har suka isa gidan,ya samu gefe ya ajjiye motar,ita ta fara ficewa wanda shima cikin zafin nama ta bude murfin ya fito ya sha gabanta,wanda ba don Allah yasa tayi baya da hanzari ba da gware zasuyi,cike da qasaita ya fara cewa
"Mun gode da zuwan da kika mana,amma ina son shawartarki,don Allah ki sake nesanta kanki da iyali na hakanan,saboda ci gaba da shaquwarku ba alkhairi bane,ba zaki iya musu maganin komai ba,a bala'i kike jefa mu,bamu buqatar ki cikin mu kinji?" Wani irin duba take masa,rainin wayonsa ya fara isarta haka,tanajin ya zama dole yau suyi wadda zasuyi
"Wai me kake nufi da ni ne?,mutuwar aure hauka ne?,a kaina aka fara?,tunda na fito daga gida na na fuskanci wani duba kake min,ya isheni haka,naji....naji zan nisanci iyalinka kamar yadda ka buqata,idan na sake taka gidanka ko na mu'amalanci diyarka ni raihana ba 'yar halak bace" ta fada hawaye na qoqarin kufce mata tare da qoqarin kewayeshi ta fice,baisan sanda ya sanya hannunshi ya damqi hannunta ba tare da jawota ta dawo gabansa,ba haka yake nufi ba,ba haka yakeson ce mata ba,yana son gaya mata yadda kullum kwanan duniya yake tashi cike da masifar qaunarta,yana son gaya mata ne yadda yake shiga bala'i a duk sanda ta qara taqi na kusanci a tsakaninsu,yana son ya gaya mata me yake ji,wacce azaba yake fuskanta aduk sanda ya tuna ta taba auren wani,wanin kuma ya kasa riqeta da daraja har ya sakota ba tare da ta aikata masa laifin komai ba,bawai yana son mata gori wulaqanci ko cin fuska ba ne
"Ka sakeni yaya rayyan,sakar min hannu" ta fada idonta cikin nashi hawaye na sintiri
"Naqi na sakekin raihana,dole ne na gaya miki yadda kike azabtar da zuciyata,tunda na fara sonki har yau zuciyata bata taba hutawa ba,kin janyo min abubuwa masu dama,na rasa dukkan wata nutsuwa da kwanciyar hankali na,sai kice kuma bazan gaya miki ba?,a dakeni a hanani kuma kuka?,sam bazai yiwu ba" sai da zuciyarta ta buga jin abinda ya fadi,duk da dama tana zargin hakan ke yawo a zuciyarsa,duk da ta qaryata ganin abubuwan da yake mata
"Nasha gaya maka bana sonka ko?,nasha gaya maka cewa babu wannan maganar tsakanina da kai,har yau rumana 'yar uwata kake aure,so pls na roqeka kabar wannan maganar ni bana sonka baki daya bare akai ga wani batu ma na daban" ta fada tana daga masa hannu fuskarta na kallon qasa zuciyarta na daka.
Tuni idanunsa suka kada sukayi ja,idan da abunda yafi tsana shine yaji tace bata sonshi,bayan yasan ita din tantiriyar maqaryaciya ce ta wannan fanninin,baisan sanda ya matse mata hannu sosai ba yana son rage zafin da yake ji cikin zuciyarsa,kai da zaya iya ma mari zai dauke ta da shi don ya nuna mata yadda ya tsani tace bata sonsa,wata iriyar zuciya ce ta dinga ciyoshi ransa ya dinga tafasa,sai ya sake fincikota ta sake matsowa dab da shi
"Me kika dauki kanki ne raiha?,me kike zaton kanki?,saboda rayyan na sonki kike masa haka?,kina zaton rayyan wani abun banza ne?,to bari na gaya miki" yayi maganar yana daidaita tsahonshi da nata tare da sake matsowa dab da ita har suna musayar numfashin juna
"Daga yau ki saka aranki rayyan bai taba sonki ba,ki saka aranki babu wani abu makamancin haka da ya taba shiga tsakaninku,sai meye ne raihana idan hakan ya faru,zaki gani zan fasa yin rai?" Ya fada yana sakinta tare da yin baya,da idanuwa ta dinga binsa har ya juya ya koma cikin motarsa,wani daci da bala'in qunci da zugi ta dinga ji na zagayata,ashe haka kalmar qiyayya take da daci?,ashe haka take dafa masa zuciya duk sanda tace bata qaunarsa,babu shakka yau ya dandana mata irin abinda yake ji,babu dadi sam babi dadi,sai taji wasu hawaye na bin kuncinta,kai ta shiga girgizawa tana goge hawayen
"Bai kamata kiyi kuka ba raihana,bai kamata ba,abinda ya dace kenan,abinda ya kamata kenan,rayyan ya rabu dake kema ki rabu da shi"haka ta dinga gayawa kanta da kanta,sai ta kasa barin gurin har aka dage masa get ya fice.
Kasa kaiwa qarshen layin yayi ya kashe motar tsakiyar hanya ya jingina kansa da makarin kujerar,wani irin motsi yaji zuciyarsa nayi tana gaua masa bai kyautu ya furta kalaman da yayi ba,bai kamata su fita abakinsa ba,sai ya dinga girgiza kai,a hankali yaji danshi kan fuskaraa yasa hannunshi ya shafo su,hawaye ne,da gaske hawaye kake rayyan?,ta shiga tambayar kansa,sai ya kasa hana kansa,ya basu mintina biyu suka zuba son ransu sannaj ya ja handkherchief yana gogesu,saidai babu wani radadi da yaji ya ragu,da sauri ya ja motar yana fatan isa gida yasha maganinsa ko zasu taimakeshi ya kashe 'yar qaramar gobarar da ta taso masa a qirji.
Kusan dukkaninsu kwana sukayi cikin wani irin mawuyacin hali,damuwoyinsu suka tsananta,hatta da rumana adaren taha wani muhimmin sauyi da bata taba gani ba agun rayyan din,damuwar data gani ta sanyata itama dakuwa,tilas yayi cooling kansa ya sanyata ajikinsa ya takurata yace suyi bacci,ba don taso ba ta rufe idanun ta cikin qanqanin lokaci baccin ya saceta
.
Washegari ya qarfafa kansa da zuciyarsa,ya tashi cike da qwarin gwiwa da jarumta duk don ya kwantar mata da hankali,ta biye mishi ne kawai don ta nuna masa ta gamsu,saidai ko daya tunanin meye damuwarsa bai bar qwaqwalwarta ba
*****************
Ranar da suka kammala jarrabawa washegari ta debi takardun dukka dalibai da zatayi marking sai maiduguri,garine da yakan mantar da ita dukka wata damuwa tata,musamman idan ta ganta gefan ammanta,ta samu nutsuwa sosai duk da cewa ba yadda taso ba,sabida abu biyu da suma suka taso suka so hade mata,na farko sultan da ya fara matsantawa kan zai turo magabatansa,ya bata dukkan wani information a kansa yace suje suyi bincike a kansa,ta sani abun zaizo musu da sauqi tunda ba boyayyun mutane bane,na biyu kuma baaba gana wanda shima ya taso wwnnan karon haiqan da qarfinsa,kwatsam kuma saiga sultan din ya biyo jirgi takanas yazo maidugurin,baima nemeta ba sai da ta gama kusan gaisawa da duk wani na sama da ita,ya samu tarba ta mutunci saidai dukkansu babu mai ikon aurar da ita idan ba abba ba,sunce shine ubanta,randa ya nemetan suna gidan amma suna hira saiga baba gana a birkice,labari ya iskeshi na zuwan sultan sai kuma ya sake zuwa ya iskesu tare da raihanan
.
Kowannensu hankalinsa a tashe yake kada ya rasa raihanan,sai ta rasa inda zata sanya kanta,wa ya kamata ta tausayawa?,kanta?,sultan?,ko baba gana?,wannan rikici ya sanyata kwana biyu ta sake qarawa kan kwanakin da tayi ta hada ya nata ya nata ta fara shirin dawowa,tana ganin gwara kano din tunda atleast ko sultan yazo bazaya hadu da baba gana ba,haka nan ko da baba ganan yazo bazai hadu da sultan ba.
Sauyin fuska ta gani sosai gun amminta sanda zata taho wanda ya saka jefata adamuwa,abu na qarshe data gaya mata shine
"Ki tsaida hankalinki guri guda raihanah ki fidda miji,ba mutuncin diya mace bane tara manema,mutuncinta dakin mijinta" haka ammi tace da ita,ko a cikin mota ma babu abinda ta tsinana illa zallar tunani har suka sauka a kano,sai yanzu tsoro ke shigarta,tsoron kada ta sake komawa 'yar gidan jiya,sultan ko baba gana wanne ya kamata ta dauka,a zahiri kowanne da irin nashi qualityn,amma a badini fa?,babu wanda tasan badininsa.
***************