← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 66

Sashe 66

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin mota ta kasa tsaida hawayenta,mutum ce mai tausayi tun asali,tana tsoratarwa ammar haduwarsa da Allah da irin wannan tarin manya manyan zunuban,sam sai hankalin rayyan yaqi kwanciya saboda mutum ne shi da baison damuwar iyalinsa,hakanne yasa ya ajjiyesu cikin wani dan lambun shaqatawa dake nasarawar sannan suka kebe don yaji meye damuwarta,bata boye masa komai ba aranar ta fayyace masa zaman aurenta da ammar da dukkan wasu abubuwa da suka biyo baya,ta kuma dora da roqarsa alfarmar tana so a yau don Allah basai gobe ba taje ta samu hajjaju saboda ragewa ammar nauyin dake kansa,koba komai dan uwansu ne musulmi wani babban taimako me zasuyi,ya lumshe idonsa,tausayinta na ratsashi na irin zaman da tayi shekara wajen hudu,ashe ba'a banza ba rumana ta jajirce kan ganin sunyi aure?,tabbas ba qaramar qauna ce a tsakaninsu ba,baice komai ba face "Allah ya kiyaye hanya,ki rage wannan kukan kuma bani son ganin zubar hawayenki"ya fidda maqullan motar ya miqa mata ya kira rumana wadda ta iso cike da damuwa ga zatonta wani abu ya samu sisin nata ya gaya mata inda zasuje,suka wuce shi kuma ya zauna da yaran suna dakon dawowarsu.

Sosai hajjaju ta dinga murna da ganin raihanan,aun aha wuya kafin au sauketa daga dokin naqin data hau,amma cikin qwalla da takaicin rayuwar da yaron nata ya fada tace ta yafe masa kuma zata ci gaba da addu'ar Allah ya bashi lafiya,tamkar kada raihana ta tafi haka suka rabu.

Koda suka koma ya sake dibansu bai zarce ko ina da su ba sai PIZZA AND GURASA,ya juyo yana dubansu bayan yayi parking fuskarsa qunshe da murmushi
" nasan dai an gaji ga yunwa,so babu batun dora girki idan an koma gida,muje kowa ya zabi abincin da yake so yaci"tuni yaran suka cika motar da hayaniyan murna kafin su balle qofar motar su firfito,tuni ma su riga iyayen nasu yin gaba.

Tsakiyan matan nashi ya shiga ya kama hannun kowaccensu suka dinga takawa a hankali,har yau ya fuskanci damuwar dayansu itace ta dayan,tunda raihana tayi kuka dazu jikinta yayi sanyi haka ma jikin rumana yake,to shi dinma sai yaji duka yanayin bai masa saboda rashin cikakkiyar walwalarsu,a hankali cikin sassanyar sautinsa yace da su
"Gaskiya a sauya yanayi,wannan yanayin naku sam baimin ba" rumana ta daga kai ta dubeshi
"Kamar yaya daddy" tamkar wani qaramin yaro ya narke murya
"To don kawai mai glass tayi kuka ke kuma 'yar tsalle sai ki tayata ku zama duka baku da kuzari?(ya kirasu da sunayensu tun na quruciya),yaya kukeson ya rayyan dinku yayi?,bayan komai tare kukeyi,AMINAN JUNA MUKE FA" dariya suka qyalqyale da ita sosai har taja hankalin wadanda ke zaune gun suna cin abinci saboda yanayin da yayi maganar tasa tilas ta baka dariya
"Ayi mana afuwa yaya rayyan mun tuba" inji raihana,yadan karasu a kafadarsa yayi qasa da murya cikin rada yace
"Ina sonku,ina alfahari da ku"
kowaccensu maganar tayi mata dadi,yaci gaba da riqe hannayensu har zuwa gun zama.

Ganin ana dab da kiran sallar magariba gashi ba hanyar gida ya sake nufa da su ba ya sanya raihana kallonsa
"Nikam yau ya rayyan sai mu zagaye garin kano ne?,ko ka manta sisi na ba ita daya bace?"
"Barshi,ai yau idan na sashi tausa bazan tausaya masa ba har sai gari ya waye" rumanan ta rada musu,dariya raihana ta saka
"Kinmin daidai" baice musu komai ba baya ga murmushi da yayi.

Ana qwala kiran sallah suka qarasa qofar gidan,gidane mai azabar kyau da tsari wanda ke dauke da sassa biyu,duk sashe daya ya isa gida na alfarma ga mutum mai iyali kuma a wadace,bangare daya ya bude suka shige baki daya yaran nata surutun kyawun gidan,suna shiga bai barsu sun zauna ba ya nuna musu toilet yace duk suje suyi alwala,qatuwaf dardumar dake motar tasu wadda da ita dama suke yawo saboda fita irin wannan ya dauko ya shimfida musu cikin qawataccen falon ya jasi jam'in salla,addu'a sukayi sosai bayan sun idar ya dubi islaha
"Anty babba maza kuje ke da qannenki kuga cikin gidan sosai,sagir ka tayata kula da su banda barna banda fitina" cikin zumudi suka miqe kana suka fice gaba dayansu.

Sai da yaga fitarsu sannan ya dawo da dubansa wajensu raihana,ya sakar musu murmushi kana ya miqa hannayensa duka biyun yana cewa
"Ku matso kusa dani 'yan aljanna" kowacce cike da qauna da alfahari da mijin nata ta matso kusa da shi sosai,ya zira hannunshi cikin aljihu ya fiddo maqulli ya miqawa kowacce,ido suka sa masa suna buqatar qarin bayani
"Maqullin wannan gidan da muke ciki ne,naku ne halak malak" rasa bakin magana sukayi,sai kuma suka rude da godiya cike da farinciki da yabawa mai tarin yawa,ya ya dora kan lebansa alamar suyi shiru,ya miqa hannunsa ya riqe hannun kowaccensu,cikin shauqi yace da su
"Wallahi kunfi qarfin hakan,kungi qarfin komai a gurina,haqiqa ku aljannar duniyata ne,kun yimin komai a rayuwata,kun aureni kun zauna da ni,kun haifa min yara wadanda mallakina ne ni rayyan jina ne,uwa uba kun hada kanku kun bani kwanciyar hankali da nutsuwar da nakejin labari maza masu tarin yawa wadanda ke da mata biyu sun rasata,kun hana wani ko wata ya sauya DANGANTAKAR ZUCIYARKU,me zance muku umm?,meye bazan iya yi muku ko baku shi ba,matsayinku a azuciyata ya zarta duka inda kuke tunani,a taqaice kune rayuwata" sai jikinsu duka yayi sanyi,kowacce qaunar mijin nata na zagaya jikinta,raihana ta dora kanta saman kafadarsa yayin da rumana taci gaba da murza hannunsa dake cikin tafin hannunta ta kasa furta komai itama tamkar 'yar uwarta.

Rumana ce ta fara sakin ajiyar zuciya sannan tace
"Insha Allahu banu abinda ya isa ya sauya DANGANTAKAR ZUCIYARMU har ABADAN"
raihana ta dago a hankali fuskantar qunshe da murmushi
"Zamu ci gaba da SADAUKAR maka da farincikinmu,SOYAYYAR MU QAUNARMU DA ABOTARMU har lahira bi'iznillah" farinciki ya sake mamayeshi,sai ya hadasu baki daya ya rungumesu cikin ingarman qirjinsa cikin wani salo da siga ta jan hankali ya furta
"Ta tabbata mu AMINAN JUNA NE na har ABADA,rayyan raiha mai glass da rumana 'yar tsalle" dariya suka saka baki dayansu zuciyarsu cike fal da farinciki da qarin godiya ga Allah bisa ga adalin miji da Allah ya basu.

*ALHAMDULILLAHI RABBIL AALAMIN*

_INA MIQA SAQON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA MASU BIBIYAR RUBUTU NA_

_INA MAI NEMAN ALFARMA GA DUK WANDA YA TABA KARANTA RUBUTUNA KODA LAYI GUDA NE DA YAMIN ADDU'A,KODA IYA YANZU NE DA KAKE KARANTA WANNAN SAQO ZANJI DADI KUMA ZANYI ALFAHARI DA HAKAN_

_SANNAN INA YABAWA DUKKAN JAMA'AR DAKE QAUNATA,WADANDA NA SANI DAMA WADANDA BAN SANI BA,KUNYI YAWA HANNUN HUGUMA BAZAI IYA LISSAFO DUKKA SUNAYENKU BA,AMMA KU SANI INA JI DA KU INA SONKU KAMAR YADDA KUKE SONA,INA ROQAR MANA UBANGIJI YASA SOYAYYAR DA MUKEWA JUNA TA AMFANEMU_

_FATAN ALKHAIRI GA DUK WATA MACE DA AKE SHIRIN KAWOWA ABOKIYAR ZAMA,INA MATA KYAKKYAWAN FATAN SAMUN KYAKKYAWAR ZAMANTAKEWA FIYE DA YADDA YAKE FARUWA GA WANNAN IYALI NA RAYYAN,DUK DA CEWA LABARINA QIRQIRARREN LABARI NE AMMA INA MAI FATAN ZAI RAGE KASO MAFI YAWA DAGA ZAZZAFAN KISHIN DAKE DAMUN DA YAWA DAGA CIKIN 'YAN UWA NA MATA,SU DAUKI AURE IBADA,DUNIYA KUMA GIDAN JARRABAWA CE,LAHIRA ITA CE GIDAN SAKAMAKO_

_BAZAN WUCE BA SAI NA MIQA GODIYA TA DA JINJINATA GA DUKKAN MARUBUTAN DAKE CIKIN GIDAN HUGUMA,ALLAH YA QARA DAUKAKA_

_FATAN ALKHAIRI GA HASKE WRITERS,UBANGIJI YA QARA HADA KANMU YA QARA MANA QAUNAR JUNA_

*ANAN NE NAKE SALLAMA DA KU MAKARANTA NAKE CEWA ALLAH YA QADDARA SADUWARMU,WANDA NA BATAWA INA NEMAN YAFIYA DA AFUWA DAGA GARESHI*🤝🏽

*MRS MUHAMMAD CE*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Chapter 66 · 0% Book details