Sashe 31
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:27 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Manzan Allah S A W yace"idan kaga wani bawa da Allah ya jarabceshi da wata cuta ko lalura ko nakasa,ka godewa Allah ka karanta(alhamdulillahil lazai Aafaani mimmabtalaka bihi,wa faddalani ala kasirin mimman khalaqa tafdilaa)"*
_______________________
*Babi na ashirin da hudu*
Cikin kwana biyu rak gidan ya zama sai masu shi,dukkansu kowa ya samu kansa,idan ka cire raihana dake jinyar zuciyarta wadda kullum take cikin ciwo da radadi,sau tari takan tsinci kanta cikin wani yanayi maras dadi duk lokacin da idanunta suja gane mata rumana da rayyan jone da juna,ta sake abinta sosai da mijinta,duk shagwabar nan ta dawo,takan bata lokaci tana yuwa zuciyarta gargadi kan kada ta shiga hurumin da ba nata ba,tana shafe tsawon awanni tana tunasar da kanta wace rumana a gurinta?,meye matsayin rumana da rayyan a yanzu,sosai take takawa kanta da burki don batq fatan bawa zuciyarta dama balle har ta samu taci galaba a kanta.
Ta jima da sanin cewa zuciya bata da qashi,hakanan babu abinda shaidan keso irin ya samu kafar da zai ruguza duk wata alaqa ko DANGANTAKA da aka ginata saboda Allah kuma cikin tsarki da tsafta kwatankwacin DANGANTAKAR dake tsakaninsu da rumananta.
Takanyi qoqarin kauce masu duk lokacin da suka kadaita su ukun ta basu guri shi da rumanan,musamman cikin da yaketa shirye shiryen tafiyarsa cikin wannan satin,kusan kullum suna tare tana zuba shagwaba ko tayashi wasu shirye shiryen,abu guda ke damunta idan ummu ta hadasu tare kan suje dakin rayyan din da ita,batasan manufar ummun ba,amma ita tana hakan ne duk don qoqarin hana wani abu faruwa ga rumanan har sai rayyan din yaje ya dawo anyi biki an kai masa ita,takanji kamar ta zura da gudu ta bar gidan idan ummu ta hanata barosu su kadai sai tace tare zasu je tare zasu dawo,wani lokaci takan fito falon rayyan din ta kunna t.v ta barosu cikin dakin,don tanajin bai cancanci a addinance a hanasu kadaicewa ba tunda halalin juna suke ga junansu,bugu da qari kuma hakan yana zamar mata wani makami fa take yaqar zuciyarta da shi,don matuqar suna zaune da rayyan din bai bari zuciyarta ta huta,da gayya yake yin duk wani abu da zai sanya dole ya tsaya mata a rai.
*************
Kwance take saman doguwar kujerar dake cikin dakin baccinsu,fuskarta na kallon saman dakin wayarta kife kan qirjinta,yayin da hannunta ke riqe da wani littafin tarihin masarautu tana karantawa,batafi awa guda da raka rumana part din rayyan ba ta samu ta gudo ta barsu.
Qarar wayar tata ya sanya kife littafin kan ruwan cikinta ta daga wayar,amir ke kiranta,a sanyaye ta daga don cikin kwanakin nan ta sakar masa jiki sosai tana bashi dama,don ta riga data sani cewa babu wata mafita gareta da ta wuce wannan,hakanan kulawar da bawan Allahn ke nuna mata ya cancanci ta bashi lokacinta,ta kara wayar a kunnenta tayi masa sallama,cike da farinciki da zumudi ya amsa mata bayan sun gaisavya soma janta da hira ita kuma ta biye masa,kusan minti ashirin sannan yace mata
"Ina sa ran gobe in sha Allahu zan shigo kano" tadan ware ido kamar yana gabanta
"Ka shigo kayi me?"
"Naga gimbiyata mana" sai ta saki ajiyar zuciya,tausayinsa ya kamata,babu shakka son maso wani bala'i ne,ba zata hanashi zuwa ba amma tana tausayin yadda amir ke dawainiya da sonta
"Amma duka duka yaufa kwananka biyar da barin kanon,kana ganin baiyi wuri ba ace ka sake dawowa ba amir" dariya yayi wadda ta jiyo sautinta sannna yace
"Ke kike ganin hakan raihana,amma kin manta salon zancan hausawa garin masoyi baya nisa?,duka bama wannan ba,kin zarta duk yadda kika dauki matsayinki a gurina raihana,koda ace kullum zanzo kano ganinki bazan taba gajiya ba,saboda ke din ta daban ce cikin mata kamar yadda kike ta daban cikin zuciyata" murmushi ta saki tana jin dadin yadda yake yabonta
"To shikenan,Allah ya kaimu da rai da lafiya,Allah ya kawoka lafiya"
"Amin ya Allah,amin sarauniyata" daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar tana tunanin amir din kamar ba yanzu suka rabu ba,tana ganin qimarsa hakanan tana respecting dinsa ko don wanda ya kawoshi,bama haka ba yana da managartan halaye wadanda su kadai abun yabawa ne.
Zaren tunaninta ya katse lokacin da gogon dakin ya kada alarm ya nuna mata qarfe goma na dareda azama ta miqe don komawa gunsu rumana gudun kada ummu tazo ta taddata anan ta barsu a can,don tasan bata bari su wuce goma da 'yan mintina basu dawo dakinsu ba,ta rasa hikimar yin hakan iya tunaninta,murmushi kawai tayi kamar kullum cikin ranta tace
"Koma dai menene abinda babba ya hango yaro bazai hangoshi ba koda ya hau dala da gauron dutse" ta janyo hijabinta dake hannun kujera ta sanya ta fice
.
Ta tura qofar falon ba tare da tayi tunanin suna ciki ba,don a abedroom ta barsu dazun suna shirya kaya cikin trolly,suna zaune ne kamar zasu shiga jikin juna rumana nata 'yan koke kokenta saboda jibi iwar haka rayyan din ya huce gajiya a england din,kamar ta juya sai kuma ta dake ta qarasa
"Ke ganta ko ya rayyan,yanzu sai tace zuwa tayi tafiya da ni fa" inji rumanan ta fada tana dubansa,murmushi raihanan tayi sannan ta ware hannayenta
"Kwantar da hankalinki ni mai iya tafiya ce ta barku,amma ki tabbatar idan ummu ta biyo sahunki ki cire suna na a ciki" sai ta miqe tana lalubar mayafinta
"Ai duk kece,me yasa ba zakiyi zamanki ba kema idan tazo taga mu biyun ne ai ba zata matsanta ba,ni gaskiya ban gaji da ganin yaya na ba"
"Au ehhh,zaman gadinku zan tqyi kenan sai kun gama abinda kuke,gaskiya ne,to ai nima akwai mai buqatar jina malama" raihanan ta fada tana yima rumana harar wasa,rayyan dake zaune yana kallonsu suna sake burgeshi,yana jin inama ace duka mallakinsa ne,yana jin ua zama dole daya dawo koda yardar raihana ko babu ayi duk wacce za'ayi,don yaci alwashin da duka su biyun zai tare cikin gidansa a matsayin matansa da yardar Allah.
Maganar da raihanan tayi ita ta tabashi,sai ya sanya idonsa cikin nata,yana kallo ta wani cije da dauke kai,wanda hakan ke tabbatar masa cewa tana sane ta furta abinda ta furta din,sai ma tayi gaba ta coge bakin qofar falon qeyarta na kallon cikin falon fuskarta na kallon waje ta tsaya a nan tana jiran rumanan ta fito.
Tare suka jero da rumanan suna hirarsu kadan kadan,suna gab da shiga dakin nasu gajeran saqo ya fado wayarta
_ki kiyaye ni raihana ki fita ido na,bawai kasawa ko gazawa nayi ba da na zuba miki ido ba,dama na baki,amma ina gab da baki mamaki_
Gogr saqon tayi don bata barin dukka saqonshi cikin wayarta,cikin zuciyarta ta saki murmushi,tana sane tayi masa haka,tanajin qila da shine ita da tuni ya dade da barin kishi ya yagalgala zuciyarsa kenan,babu kulawa ta miji da mata da baya bawa rumana gabanta,saidai tana yiwa kanta waigi tunda tasan halas ne duk wani abu da zasuyi
"Ina roqon Allah ya bani damar baka mamaki kafin kai ka bani rayyan" tayi furucin cikin zuciyarta
*************
Kasancewar tana da lacture washegari ranar da amir din zaizo,hakan ya sanya tilas ta shirya zuwa makaranta tunda duka duka qarfe sha biyu ta fito,tasan kuma zai iya kaiwa azahar bai qaraso ba,tunda bauchi da kano akwai tazara,bata barwa rumana saqon tayi mata komai ba tunda tasan bata da time,duk da idan ta fada din zata yin,amma bata son takura don tasan suna tare da rayyan.
Tana dawowar ko zama bata yi ba ta shiga kitchen ta fara shirya masa abinda zata taryeshi da shi,qarfe biyu ta kammala komai ta killace guri guda,tana shirin fita rayyan ya shigo,yau kam sun dan sake don ummun bata nan ta fita bikin 'yar qawarta,sanye yake da farin t.shirt mai gajeran hannu da farin wandonta
Gashinsa ya kwanta luf sai qyalli yake,hakan ya qarawa fuskarsa kyau
"Hmmm,hala an fara qyallin angwanci ne" raihana ta raya cikin zuciyarta tana tabe baki,bake bake yayi ta rasa hanyar da zata wuce,gashi ya rutsata da idanu,ya numfasa a hanakali sannan yace
"Me aka dafa mana?"
"Me na dafawa baqo na dai,saidai ko na kira maka rumana ka tambayeta" ta fada tana ware dankwalinta ta yafa saboda yanayin rigar dake jikinta,wani dan qaramin murmushi ya saki bayan ya harde hannayensa a qirji
"Da alama kishi kike kenan ko?" A razane ta waigo ta dubeshi,take idanunta suka tara qwalla
"Allah ya sawwaqe ya kiyaye,cewa akayi kowa ma irinka ne?"
"Da zaki zama kamar ni din ai da naji dadi,any way,a bani abinci yunwa nake ji"
"Ban dafa da kai ba" ta fada tana hade rai
"Wannan kuma baki isa ba yarinya wallahi" ya fada kai tsaye yana durfafar flask din abinciccikan data shirya yana cewa
"An haramta min soyayyar na daga qafa kuma abincin ma sai ace min na wani ne" ya dauki plate yana diban abincin aciki,baki ta saka galala tana dubansa cike da takaici,don duk adon da ta yiwa abincin ya kwashe ko ajikinsa ma tuni ya soma kaiwa cikinsa.
Rumana ce tayi sallama ta shigo kitchen din,kai tsaye idanunta kan rayyan
"Kai kai,yaya kace min kai dinner ka samu ina can ina nemanka" kasa magana yayi sabida dadin abincin har sai daya hadiye na bakinsa
"Abincin ma da ake mana rowa har ma da gori" ya fada yana sake diban wani zaikai baki,tasan sarai da wa yake don haka ta dubi raihana tana qunshe dariya
"Garin yaya sisi?" Raihana da wani irin baqinciki ya tokarewa wuya ta buda baki da qyar
"Haba sisi,abincin da na shiryawa amir ne fa,duba yadda ya bata min tsarin baki daya" cikin boye dariyar tace
"Ah....gaskiya miji baifi miji ba,ci kayanka yaya na,amma fa....gsky baka kyautawa sisi na ba" sai kawai kuka ya qwace ma raihana ta juya da sauri ta fice,binta sukayi da kallo baki daya,rumana na mamakin daga dan wannan abu?,ta yunqura zata bita rayyan ya hanata ya tsaidata suka cinye abincin tare don yasan meke mintsinin zuciyarta.