← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 66

Sashe 12

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kimanin awarsa biyu kenan da shigowarsa cikin gidan,banda wanka da ya sake da abinci da yaci babu abinda ya iya tsinanawa,damuwar da take danqare qasan zuciyarsa ita tayi tasiri har gangar jikinsa ta haifar masa da kasala,bai son damuwa sam a rayuwarsa saboda bai tashi cikinta.

Daya daga cikin littattafansa da yakan duba lokuta irin wannan da yakeson kautarwa kansa da tunani ya dauka ya soma duba shafi bayan shafi,wanda hakan ya daukeshi mintina kusan arba'in da biyar.

A hankali ya sauke littafin,halayyar tauraruwar ciki sai ta burgeshi,ya dinga bitar dabi'un cikin kwanyarsa daya bayan daya,damuwar dake ciki ta kwaso a guje ta tsinke zaran tunanin nasa,tsaki ya ja bayan daya gama tuna abinda ya farun dazu gami da ajjiye littafin a gefansa,wayarsa ya dauka ya lalubo lambarta ya kira.

Tana tsakiyar dakin nasu wanda ta baje littattafanta na makaranta tana daidaita kansu saboda cikin satin zasu koma,sanye take da mutuniyar tata wato duguwar riga amma ta atamfa ce mai shan umbrella,kanta babu dankwali ta cireshi gefe saboda zafin da takeji,sakamakon tsefe kan da tayi gashi da cika,don haka bata fiya tsifa ba indai tasan ba wankin kai ko kitso zata ba saboda damunta da yakeyi.

Lokaci lokaci takan daga kai ta dubi rumana dake kwance rigingine kan gadonta,tun dazun ta lura akwai damuwa sosai kan fuskarta,amma ganin bata ce da ita komai ba ya sanya itama tayi shiru,bata da aqidar shishshigi da son sanin halin da mutum yake ciki,mawuyacine tabi qwaqwqwafin abinda bakai ka gaya mata ko ka nemi ta sani ba.

Ringing din wayar tata ne ya dan ja hankalinta,da fari qin dubawa tayi ga zatonta farouq ne ko al'amin,sai da ajjiye littafan hannaun nata sannan ta duba,ganin me kiran ya sanyata daga wayar ta kara a kunnenta,magana yayi da bata wuce sakan biyar ba duka suka ajjiye wayar,ta juya tana duban rumana dake kwance tana charting amma damuwa kwance kan fuskarta
"Ya rayyan ke kirana rumana" ajjiye wayar tayi da sauri ta miqe daga kwanciyar tana dubanta
"Ya shigo gidan kenan?"
"Eh tunda gashi yace yana daki.....ko zaki tashi muje tare,tsoron fitar nake ni kadai"
Kai ta girgiza tana tabe baki
"Jeki kawai,ba inda zani.....bakisan fada mukayi dazun ba?" Cikin zare ido raihana data soma nada mayafinta aka ta dubeta tace
"Fada kuma?,me ya hadaku?" Ajiyar zuciya ta saki sannan tace
"Sadiq yaga ya kirani,kuma fa bawai wani hira bace,kawai gaisawa mukayi,ya gayan ya dawo daga tafiyar da yayi japan,shikenan fa" kai raihana ta shihga girgizawa
"Bakiyi daidai ba rumana,banga inda kika kyauta ba anan gaskiya.....hana rumana,wai maza nawa zaki aura ne?"
"Ce miki akayi soyayya nake da su?....duk wanda kika ganni da shi mutunci ya hadamu kuma bazan iya wulaqanta su ba.....me yasa kuka kasa fahimta ne?,kunsan matsayin ya rayyan kuwa a zuciyata,ke kinfi kowa sanin matsayinsa raihana,a yau idan na rasa ya rayyan inajin har na koma ga mahaliccina bazanyi aure ba".

Shiru ne ya ratsa dakin,tausayin rumanan ya fara ratsata ganin yadda idanunta suka soma hada qwalla,da alamu maganar ta taba zuciyarta ne,ita kanta shaidace lamba daya kan son rayyan dake zuciyar rumana shekaru bila adadin da batasan yawansu ba,tunda ko ita din ma tare tazo ta taras da su,matsalar rumana sakin fuska ga kowa da saurin sabo,hakan sau tari sai tace ka kori wanda yake yinka tamkar ka wulaqantashi ne,itakam ta rasa yadda zata fassara abun
" bari naje na dawo,kada ki damu zanzo mu tattauna kinji sisi na 'yar tsalle"ta qarashe maganar cikin sigar zolaya,ta kuwa samu yadda takeso,don murmushi rumanan ta saki tana share hawayen fuskarta,cikin zuciyarta tana godewa Allah da ya bata 'yar uwa irin raihanan
"Saikin dawo ina jira"
"Ince to kina gaida shi?" Kai ta kada sauri
"Nidai ban aikeki ba"
"Zaki aikenin ne ma,kowa fa ya sani fadan masoya hutu ne" tayi maganar tana ficewa a dakin tana murmushi

A hankali ta tura qofar dakin ta shiga da sallama,yana zaune kan kujera ya jingina bayansa a makarin kujerar,yayin da ya miqe qafafunsa bayan ya hardesu saman center table,idanunsa a lumshe suke,tsaf dakin yake cike da qamshi da sanyin na'urar sanyaya daki,rayyan badai tsafta,akwaishi da qyanqyami hakan ya sanya yake gwani wajen tsafta.

Ya bude ido ya kalleta na 'yan sakanni kanna ya masa mata ta maida qofar ta qaraso,da hannu ya mata nuni da kujerar dake fuskantarsa
"Gani ya rayyan" ta fada cikin muryarta mai sanyi
Sauke qafafun nasa tayi qasa sannan ya gyara zamanshi
"Raihanah" yanayin yadda ya kirata dinne ya sanya ta sake shiga nutsuwarta
"Na'am" ta amsa masa tana duban gefensa bashi din ba
"Ina so ki gayan wace rumana,ma'ana wace rumana bayan barina gida,ya rumana ta kasance bayan ta girma?".

Cikin rashin fahimta ta dago tana dubansa
"Yaya ban gane me kake nufi ba"
"Kin gane tunda gwari gwari nayi miki,saidai kice kina buqatar qarin bayani ko?...."ya fada yana sake daidaita zamansa
"Ina nufin ki gayan meye halayen rumana,na tambayeki ne saboda wasu abubuwa da na lura tattare da ita wadanda zasu iya haifar mana da matsala".

Shiru tayi tana jin ya dora mata nauyi mai girma,tabbas rumana ta jama'a ce maza da mata yara da manya,ta yaya zata gayawa rayyan haka ta sigar da zai fuskanceta?,ta sani kuwa sarai idan ta bude baki da niyyar cewa komai to zatayi qarya ne.

Ci gaba yayi da zuba mata ido har tsawon kimanin minti goma,tuni ya gama karantar ma'anar shirunta,gyaran murya yayi kadan sannan yace
"Ni bari na gaya miki tunda ke bazaki gaya min ba,rumana nada tarin jama'a da take mu'amala da su,bawai ina nufin mummunan mu'amala ba,irin abinda kuke kira da friendship ko?" Batasan sa'ar da ta dubeshi,da sauri ta fara girgiza kanta
"A'ah,ka fahimceta ya rayyan,kowacce budurwa idan ta taso dole ta masu masu son qulla mu'amala da ita,haka yake ga kowacce mace indai tana kan lokacinta......"
"Ke haka kike?" Ya tambayeta kansa tsaye,dif tayi masa kama daga bisani ta daga masa kai a sanyaye alamar eh.

Wani murmushi ya saki ya maida bayansa jikin kujerar ya sake jingina ganin ta raina masa hankali,a hankali ya dinga kada kansa sannan yace
"Kin manta tun kuna da majina ahanci na sanku?,ba sanin jiya ko yau bane ko gobe.....dubeni nan raihana,ki dago kanki ki gayan ni raihana nima haka nake"
Tanajin rumana ta cancanci ta bata kowacce iriyar kariya daga gareta,da qarfin gwiwarta ta dago ta dubeshi,tashin farko wani irin kwarjininsa ya cika mata ido,ta gaza ci gaba da kallonsa yayin da shi kuma ya kafeta da ido,kunyar yi masa qarya ta mamayeta,a hankali ta janye idanunta ta maida kan yatsun hannunta da suka sha ja lalle tana qare musu kallo,shi din ma maida idonsa yayi kan inda take kallo din kana daga bisani ya janye idanunsa
"Kayi haquri ya rayyan zamu gyara in sha Allahu,rumana na matuqar sonka"
"Ni din ma ina sonta,amma kuma ina da matuqar kishi"
"In sha Allahu zamu gyara ya rayyan,yanzu haka tana daki cikin damuwa don Allah kayi haquri"shiru yayi yana dubanta kamar bazai tanka ba,har sai data dago taga yana gurin,sai ta sake sadda kanta
" please ya rayyan"
"Is ok.....ki turomin ita"
Murmushi tayi ta dubeshi
"Yauwa yayanmu,mun gode" shima martanin murmushin ya maida mata ta juya ta fice a dakin

*************

Da dan sassarfa ta qaraso motar kana ta bude gidan gaba ta fada ciki,ta dubi rayyan dake zaune cikin motar cikin shagwaba tace da shi"afuwa mai gidana,kaga ko kwalliyar ma baban kammala ba na fito"ya dan saki fuskarsa yana qoqarin tada motar
"Kin wuce haka gimbiya,ya wuce",sai ta waiwaya ta dubi raihana dake gidan baya a zaune
" afuwa sisi na"
kada kai tayi tana murmushi"ya zamemin jiki"sukayi dariya ita da rumanan.

dukkansu sanye suke da material pinch sai abun daurinsa maroon,ba qaramin kyau sukayi ba kasancewarsu cikin sahun wadanda Allah ya wadata da kyau,biki akeyi na 'yar qanwar alhj dalhatu sumayya wadda take jika ce agun hajiya babba kamar yadda rumana take,yau ne dinner din,ummu tace rayyan din ya kaisu,dama yayi niyyar yin haka don baison suje su shiga motar wasu.

Daya hannun nasa yasa ya zari cd plate ya tura ciki ya danna play sannan ya rage sautinta qasa qasa,waqar shehu kan giwa ta soma tashi cikin motar,duk da tsohuwar waqace amma kidanta ya fito rangadadau,hakan baitukan cikin waqar a bayyane suke,sosai raihana keson waqar ita da waqar ahmad a ruwa suna burgeta,rumana ta tsaya da daurin da take sannan ta bushe da dariya
"Haba ya rayyan,ni na dauka wata hadaddiyar waqa zaka saka mana"
"Wannan din ma nada ma'ana ki saurara kiji"
"Na dade da saninta a gun sisi,ta dade tana gayan hakan nikam har yau bani da ra'ayinta,ita din ma mayyarta ce,wani lokaci ra'ayinku da halayyarku daya,yanzu ya rayyan waye zaice ka rayu cikin england don Allah" ta fada tana masa dariyar tsokana,ci gaba tayi da daurin dankwalinta tana cewa
"Wannan waqar ai sai su abba da daddy"
"Bakya ganewa rumana,bakisan karatun dake cikin irin wadan nan tsaffin waqoqin bane" inji raihana
"Rabu da ita,batasan waqoqi masu ma'ana bane" nan qaramar muhawara ta hadu wadda ita ta tayasu hira har suka kai wajen.
Chapter 12 · 0% Book details