← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsoro da karaya take bashi amsa tare da qoqarin qwace jikinta
"Bacci nake ji ka qyaleni" cikin kunnenta yake gaya mata
"Ai nima baccin zan sanyaki yi yanzun kuwa" tuni ya hanata katabus ya hanata komai,kuka haiqan take masa kamar jiya don taji a jikinta saidai sam wanda take saboda shima baisan tana yi ba sai daga bisani ya shiga aikin lallashi,sam baya controlling kansa matuqar suka kebe,yasan kuma wannan wani abu ne daga zuciya da ruhinsa.

Tilas ta lallaba kanta ta shirya da wuri tamkar ba ita taji jiki daren jiya ba har da make up dinta,ya dinga binta da kallo kasancewar bai saba ganin fuskarta cikin makeup ba,ba qaramin kyau tayi ba,make up ce ta nutsuwa kamar yadda yanayinta yake,komai dan daidai na hankali,ba shakka ko cikin mata komai nata daban ne,shima a shirye ya sake dawowa bangaren nata,kasancewar yau zai fita don hidimar bikin bude kamfaninsa har yau bai kammala su ba,sai sukayi kacibus,ya kasa daurewa sai daya tanka
"Inye ba,raihata ashe ta fara makeup?" Yanayin yadda yayi magabar dole ya baka dariya,tamkar yadda yake magana da au ne a can shekarun baya zamanin quruciya,sai ta kauda da kai gefe amma duk da haka sai da yayi nasarar jefa murmushi kan fuskarta,ya zagaya bangaren da take tsaye din yana sake lalubar qwayar idanunta
"Ni baki ga tawa kwalliyar ba baki ce komai ba,bayan ba haka sisinki ke yimin ba,kullum nayi kwalliya sai ta yaba" ta fada cikin sigar shagwaba,ta daga idanunta a hankali tana qare masa kallo,ko da baiyi ado ba rayyan din mai kyau ne,ko baiyi wanka ba idaniyarta bata fasa ganin kyawunsa,ingarman namiji ne a zahirinsa da badininsa,ballantana yanzun da ya sheqa kwalliyarsa yana fidda qamshi cikin yadin kufta wanda yaji aikin sarauta wanda bata tantama mai martaba ne ya aiko mishi da shi cikin kyautututkan aurensu,blueblack ne wanda yayi masifar fidda haske da kyawunsa,qafarsa sanye da half cover na maza,yayin da kansa ya kafa hula damanga wanda tayi kala da zaren aikin da aka yiwa kuftarsa,babu macen da zata kalleshi bai burgeta ba.

Tayi qarfin halin dauke kanta daya gefan dai tana tabe baki tace
"Baka yimin kyau bane shi yasa,siai na kawai kake burgewa amma banda ni" murmushi ya saka aboye yana leqa fuskarta,yasani kawai fada tayi amma bawai har zuci ba,sai ya sake narkewa yana cewa
"Ok,muje gurin siain naki,na sani cewa zabinku daya ne,indai har tace nayi kyau to nayi din kuma sai na ciki taãra,idan kuma tace banyi kyau ba to na yarda zanyita sauya kayana har sai nayi muku kyau" sai ta kada kai don yanke tsaiwar tasu tana shirim yin gaba ya janyota ta dawo da baya har tana fadawa jikinsa,hannayensa yasa ya rungumeta tsam yana shaqar qamahun da jikinta ke fiddawa na asalinn turarukan 'yan maiduguri
"Ban gama maganata ba madam raiha,badon nazo ba qilan tafiya zakiyi gun sisin naki ki barni kenan?" Tana son masa tsiwa don ya qyaleta amma sai ta kasa bakinta yayi naiyi,yanayin rungunar da ya mata kadai ta kashe mata zuciya,maimakon tsiwar sai ta buge da cewa
"Bai kamata sai tazo jemanmu zamu je ba,kaima kuma fita zakayi kana dab da yin latti fa"
Sai ya sassauta riqon da ya mata ya kama qugunta suka soma tafiya yana cewa
"Bakison ayimin bulalar makara ko?,thanks for caring"ya fada har cikin zuciyarsa yana jin dadin 'yar kulawar data nuna,sai taji wami iri,me akayi na godiyar a ciki?,abu nawa shi ya mata na kulawar,ko dazun bai fita daga sashen ta ba sai da shiryata tsaf,makeup kawai tayi da kanta.

Taso qwace jikinta amma ya hana ta hanyar cewa
" mai sisi,don nasan qorafin naki kenan,to ai aiain ba'a harabar gidan take ba ko?"sai tayi shiru sukaci gaba da takawa sannu a hankali,ya sake katae shirun ta hanyar cewa
"Ya jikin naki?" Kunya ta kamata sai ta wani basar tace
"Ni lafiya qalau," idanu ya qwalalo yana dubanta
"Ashe dama kukan qarya kike min duk kibi ki cikamin kunne?,to na gane logic din,kuce yau ma na shirya akwai sabuwar duniyar da zan sake shiga ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,gabanta ya fadi tayi kicin kicin da rai,yadda tayi shiru tana tura qaramin bakinta gaba ya bashi dariya,daga haka ya yanke duk wata magana tata shi kuma yaci gaba da dan tsokanarta yana cewa
"Bidiri burede,rayyan ango" har suka isa qofar sashen rumanan,inda anan ta janye jikinta daga nasa tayi gaba yabiyota a baya.
.

Ba kowa cikin falon da suka shiga,da alama tana bedroom,saidai ko ina akillace yake,haka dining din jere yake da kayan abinci,kai tsaye dining din ya nufa ya fara bubbuda kwanukan,ya dago ya dubi raihana dake zaune gefan kujera yana shafa cikinsa
"Nifa gsky yunwa nakeji,pls raihata kiyi sarving dina kawai ni na fara" baki ta dan murguda wanda hakan ya matuqar burgeshi
"Ba wanda zai karya sai sisi ta fito,Allah yasa naga hannunka cikin kwanukan" ta fada tana miqewa ta shige dakin gadon rumanan bayan tayi knocking.

Daga wanka ta fito,tana gaban mirrow tana shafe shafe,kowacce fuskarta dauke da murmushi take duban 'yar uwarta
"Nifa ince kamar na jiyo muryoyinku"
"Eh ashe kina wanka ne,mrng sisi"
"Mrng amarya,ina angon namu" ta fada tana shafa foundation,hararta tayi sannan tace
"Ba na gaya miki ki daina kirana amarya ba,ango kuma ban sanshi ba sai rayyan,na baroshi falo zaya bude miki kwanukan abinci" dariya ta tuntsire da ita tana cewa
"Wallahi sisi kin koyi rigima kema,hala yunwa yake ji"kafada ta daga
" oho,ko yunwar ce ma nidai nace sai kim fito"da sauri rumanan ta miqe tana bin foundation din da powder tana cewa
"Kai kai kai,ban lamunta ba abarshi da yunwa,tashi muje" ta fada tana lalubar kayan da zata sanya ta soma zurawa,baki raihanan ta tabe taba kallonta
"Uhmmm,masu miji"
"Ai gaskiya ce,domin na sani mijina yafi na kowa(mamam farida)" rumanan ta fada tana dariya sannan suka jero suka fito.
.

Raihanan ce tayi sarving din kowa,suna ci suna taba hira,rayyan ya dubi rumana
"Angel,da gaske kwalliyata bata yi kyau ba" ta juya ido tana dariya sannan bayan ta kalli raihana
"Hala sisi na ke tsokanarka?,gaskiya sisi bana supporting dinki yau,na gaya miki mijina yafi na kowa" murmushi yayi ya dubi raihana gami da kashe mata ido
"Ya zama wajibi naci tararki,me zaki bani?"narke fuska tayi don ta gama fuskantar me yake nufi ta juya ta dubi rumana
" kinga ki yiwa mijinki magana"dariya tayi hadi da yi mata gwalo
"Oho,me yasa kika ce bamuyi kyau ba" sai ta gyada kai tace
"Ok,ni zaku ware ko?" Dariya rumaman ta sake mata sannan tace
"Sorry sisi" yayin da rayyan yaci gaba da dubanta,ganin yadda ta karaya yasa yace
"Kafin na dawo kisan me zaki ban,idan ba haka ba duk abinda muja zaba dole a bayar ko ba haka ba my angel" ya fada yana duban rumana
"Qwarai kuwa daddy" ta amsa itama tana dariya qasa qasa.

Tissue ya cira yana goge bakinsa
"Ya kamata islaha ta dawo hakanan"
"Haba daddy,ka barta mana,da ta dawo sai ta takura kowa kasan hali"
"Me ruwanki,mudai kawai a dawo mana da ita" inji raihana,hannu rumana ta daga
"Afuwa mamma,zata dawo".

Tare suka jero rayyan din na tsakiyarsu,raihana bata yi gardama ba albarkacin rumanan,har bakin mota,ya dubesu baki daya farinciki na ratsashi,rumana ta miqa masa jakarsa bayan ta yiwa raihana sign ta bude masa qofar motar,hannayensu duka ya riqe cikin nasa yayi kissing sannan yace
" Allah ya yi muku albarka
.

Rumana ce ta amsa cike da farinciki
"Ameen daddy" ya maida idonsa kam raihana
"Ke baki ce komai ba....angel sisinki na lura muguwar 'yar qauye ce fa,jibi,miji ya muku addu'a amma ki kasa amsawa" baki ta tura tana sake jin nauyin yadda rumanan da rayyan din ke harkarsu free ba ruwansu basa jin nauyin komai,sai kawai ta koma bayan rumanan ta tsaya,bata sake cewa komai ba har ya shige mota ya tasheta ya fice,sai lokacin ramanan ta juyo tana harararta
"Yadda ya rayyan ya fadi dinne hala ke 'yar qauyence"
"Oho,dukanmu kenan qauyawa ne haka zakice" ta fada tana dariya tare da bin bayan rumanan.

Bangarenta suka wuce ranar tare suka yini sur,sukayi abincin rana suka ci tare sannan daga bisani suka dora girkin dare,wanda hakan ya taimaka qwarai wajen warwarewar jikin raihanan har ta dinga jin kamar ba abinda ya faru da ita.

Sai da suka kammala abincin dare sannan kowa ya wuce dakinsa don yin wanka.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:54 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*

______________________

*Daga sa'id dan zaid R.A yace:manzan Allah S A W yace"duk wanda ya yanke taqi guda na qasa(fili ko gida ko gona)da zalunci,to,Allah zai rataya masa shi ranar alqiyama tun daga qasan bakwai"*

_bukhari da muslim ne suka rawaito shi_

______________________

*Babi na arba'in da shida*

Tana idar da sallahr magariba ta isa gaban madubi bayan tayi wanka tun shigowarta,saita kuma tsintar kanta da yin kwalliya mai qayatarwa,tana daura dankwalinta cikin sauri don komawa gun sisinta suci gaba da hira don ba qaramin dadin hirar da suka wuni yau sunayi ba taji.

Sallamarsa gami da turo qofarsa ce ta katse mata hanzarin,ya shigo dauke da jakar office dinsa,kwalliyarta ta ta tsone masa ido har ya tsaya kallonta,hakan sai ya bata kunya bayan lokaci mai tsawo rabon da taji hakan,ya qaraso a hankali ya rungomota ta baya ya dora habarsa kan kafadarta sannan ya saki ajiyar zuciya yana ci gaba da kallon kwalliyar tata ta madubin dake gabansu qamshin jikinta na ratsashi,a hankali ta bude bakinta kanta na duban qasa ta masa sannu da zuwa ya amsa mata cikin wani irin salo
"Raihata kinyi kyau,dama kin iya kwalliya har irin haka amma bakiyi?"
"Wa zanwa a wancan lokacin,bayan na fidda rai da samun wani wanda zaya zamemin SANYIN IDANIYATA,wani wanda zaya zamewa rayuwata GARKUWA,meyw amfani ko ma'anarta idan nayi" ta fada cikin zuciyarta.
Chapter 61 · 0% Book details