Sashe 15
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A gaban mirrow ta sameta ta fiti daga wanka ta sanya kaya tana shafa mai
"Sannu raihana,ya akayi ne?,naga bakin kin nan kamar a kwai magana"
Murmushi tayi sannan ya yi qasa da kant"uhmmm,inajinki raihana"
"Ummu dama akan yaya rayyan ne da rumana" sai ta dakata da abinda takeyi din tana duban raihana
"Uhmmm,wani abun ya faru ne?"zuciyarta taji ta dada sauri kan bugunta nada,tana jin wani iri amma zuciyartata ke qarfafarta kan zatayi abunda ya dace ne,zatayi abinda zai zama kwanciyar hankali ga kowa,don haka cikin qarfin hali ta bude baki
" ummu,rumana da ya rayyan ne,sabanin da suke yawan samu ummu yana damuna,shine nake ganin me zai hana a matso da batun aurensu kusa ko hakan zaisa su maida kai su kawar da duk wani sabani dake tsakaninsu....."sai kuma tayi shiru,kai ummu ke jinjinawa,tabbas ita din ma ta lura,kawai batason matsa masu da tambaya ne ko shiga lamarinsu,tunda ko da can dama su suka hada kansu,tabbacin suna son juna kenan,amma yanzu raihanan tazo da wani hanzarin wanda taji dadinsa matuqa,tayi mata hangen da ita batayi ba,shi yasa take sake qaunarta kullum saboda kaifin basirarta da tunaninta
"Tabbas don kada shaidan ya shiga ya wargaza lamarin ba,tunda dama shi babu abinda yaqi jini irin sunnar ma'aiki,gaskiya ne,bari abbanku ya dawo insha Allahu yau zan sake tuntubarsa da batun,Allah yayi miki albarka raihana kinyi tunani qwarai da gaske"
Dakinsu ta nufa saidai tanajin gwiwarta sam ba qwari,bangaren zuciyarta na sake qarfafarta daidai tayi,don haka ta qara saurinta don ta isa dakin ta yiwa rumanan albishir kan maganar da sukayi da ummun,don tasan tabbas maganar zata wanke duk wani bacin rai take ciki.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[7/23, 8:55 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo daga nana Aisha r.a tace"manzan Allah yana kasancewa cikin hidimar iyalansa ta cikin gida(yana taya matansa ayyukan gida),yana dinke tufafinsa ko takalminsa da kansa,har sai an kira sallah sannan ya fita zuwa masallaci"*
________________________
*babi na sha hudu*
A inda ta barta anan ta taras da ita zaune,qarasawa tayi gefan rumanan ta zauna fuskarta qunshe da murmushi,ajjiye litattafin itama tayi tana dubanta,raihana ta kama hannayenta tace
"Albishirinki sisi"
"Goro fari qal" ta fada tana murmushin itama tare da yatsina fuskarta cikin qaguwa da son jin me zata ce
"Yanzu daga dakin ummu nake,kan maganarki da ya rayyan,tace in sha Allahu yau idan abba ya dawo zata sake tunasar da shi maganar".
Ido ta dan zaro" da gaske kike?"
Kai ta jinjina mata
"Zan miki qarya sisi?" Batasan sanda ta Rungume raihanan ba hawaye ya cika idonta"na gode sisi na,bani da kamarki,Allah ya saka miki da alkhairi"
"Yiwa kaine ai" inji raihanan.
Sai data nutsu kana tace"bani labarin amir"murmushi raihana ta mata sannan ta lanqwashe qafafunta tana duban rumana
"Ai kin ganshi ko?"
"Eh amma ina fatan yayi miki?" Fuska ta dan yamutsa"eh,ba laifi kam"
Kai rumana ke jinjinawa tana cewa"ki bashi dama kawai sisi,tunda har ya samu makin ba laifi na tabbata wataran zaici nasara"dariya sukayi baki daya sannan suka fara hada kayansu na tafiya gidan biki
************
Ranar lahadi aka kammala biki aka kai kai amarya,don haka gidan aka samu sauqin jama'ar dake cikinsa.
Ran monday raihana duka ta rigasu tashi,yawancin jama'ar gidan da sukayi saura nata baccin gajiya,saboda tana da lacture qarfe tara na safe,saboda haka tun takwas da rabi ta kammala shirinta ta wuce makarantar ko rumana bata tasa ba.
Biyu na rana ta fito,sai ta samu qasan bishiya ta zauna tana duban yadda garin ya qwalle da rana mai zafi,don har yau ba'a samu saukan ruwan sama ba,tunaninta kawai yadda zata shiga ranar ta wuce qoqi,gashi bata sanar da auwal yazo ya dauketa ba,kuma bata sani ba ko yana da wanu uziri kada ta katse masa.
Wayarta ce ta soma ruri,ta janyo jakarta da bata rufu ba saboda handout da ta zuba a ciki,ta zura hannu ta lalubo wayar,sunan ya rayyan ta gani,ta daga ta kara a kunnenta
"Kuna cikin makaranta ne?" Ya fara da tambayarta
"Eh"ta bashi amsa ga tunaninta yana sane ne
" ok,ina capteria"
Ya katse wayar,ta fuskanci me yake nufi don haka ta maida wayar jaka ta miqe.
Yana gaban kanta hannunshi riqe da bottle na cook mai sanyi yana kurba kadan kadan,ya amshi canjinsa ya zuba a aljihu
"Ga yarinyar nan fa man"
"Me ya kawota capteria ita da ba zuwa take ba"
"Oh my god,yarinyarnan tana firgitani,tana yimin kwarjini,har yau na kasa tararta na gaya mata meke zuciyata"
"Kwarjininta da natsuwarta ne yayi yawa wlh,ba kaiba ma,mutane da yawa basa iya tararta saidai su kama qafa da 'yar uwarta,ita ba ruwanta,tana da sakin fuska da son mutane,bata da girman kai irin nata".
Maganganun wasu samari dake gefansa kenan su hudu,a hankali ya waiwaya ya dubesu,kana shima ya maida idonsa inda yaga suna kalla,a hankali ya taka ya koma bakin qofar shigowa gun cin abincin,ya hade hannayensa a qirji yana naxarinta.
Sanye take da atamfa dinkin riga da zani,sai laffaya da ta nade jikinta da ita mai kyau ta asalin bare bari wadda tayi marching da atamfar jikinta,jakarta na maqale a singalalin hannunrmta,wanda baka iya gani saboda dinkin mai dogon hannu ne,takalminta plate ne mahadin jakarta,kanta na duqe a qasa bata kallon ko ina sai inda zata sanya qafarta
" budurwar jami'a?"ya yiwa kansa tambayar cikin zuciyarsa yana ci gaba da kallonta,sam ba zaka taba cewa budurwar jami'ar bace,babu wannan qyale qyale da rawar kan nasu
_"yanayin raihana kawai da kalamanta ya isa ya gaya maka wacece ita,kasan raihana irin matan dake masifar tsada ne a wannan zamanin?"_
Wasu daga cikin kalaman amir suka dawo masa fes akai.
"Daga kan mana haka ki kalli gabanki kada ki fadi" rayyan ya fada lokacin da take dab da shigowa gurin,don ya lura sam bata ma kula da shi ba agurin,kan nata kuwa ta daga ta saki murmushi
"Allah ya rayyam dan dai kaine,ko rumana ban rakowa nan,bana son zuwa gurin nan kwata kwata" ta fada tana jingina da bakin qofar gun,kallo ya sake binta da shi
_"yanayin kalamanta kawai sun isa su gaya maka wacece ita"_ zancan ya sake fado masa,jin yayi shiru ta dago suka hada ido,sai tayi saurin janye idonta ganin yadda yake kallonta,gabanta ya fara dukan uku uku
"Ina rumanan,ko ita bata kammala ba?"
"A'ah,yau duka bata da lacture,na barota gidan hajiya" kafadarsa ya dage tare da ware hannayensa ya fara tattaki
"Ok,dama zuwa nayi na maidaku gida,kwanan ya isa haka,gidan babu kowa shiru babu dadi"ya fada yana yin gaba,a baya ta soma binsa tana fadin
" muma yau muke shirin mu koma,saboda ummu kewa zata yi mata yawa"
Shiru ne ya biyo tsakani har suka qaraso bakin motar,suka shige dukkansu ya tada motar sukabar makarantar.
"Abba sun sa ranar mu da rumana?" Rayyan ya fada tamkar ba da ita yake maganar ba idonshi bisa titi,da sauri idonta awaje ta dubeshi fuskartar dauke da murmushi
"Wayyo Allah!,da gaske yaya?"
"Zan miki wasa ne?" Ya fada ba tare da ya dubeta,irin murnar da yaga tana nunawa shi ya sashi sawa juyowa ya dubeta,fuskarta tamkar wadda aka yiwa albishir da aljanna,fadi take suyi sauri taje ta yiwa sisinta albishir.
A hankali tari ya soma sarqeta wanda tun yana mata sannu ssi da takai ga ya faka motar gefan titi ya rirriqeta,minti kusan biyar tana yi babu qaqqautawa kafin ya fara sauqi
"Ko mu wuce kiga likita?" Ya tambayeta yana dubanta,kai ta girgiza tare da qirqiro murmushi
"A'ah,ba komai,ai ban taba irin hakan ba,yau ne kawai", ya tada motar yana cewa
" ok shikenan,amma idan kika sake ji kiyi magana kada kice zakiyi shiru"
"To" tace tana jinginar da jikinta a makarin kujerar,tayi luf jikinta ya dan saki,shiru ya ratsa motar lokaci lokaci yana juyowa ya dubeta tare da yi mata sannu,da haka har suka qarasa qoqi.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
______________________
*Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S.A.W yace"idan mace ta sallaci sallolinta guda biyar(na farilla)ta azumci watan ramadan,ta kiyaye farjinta,ta yiwa mijinta biyayya,ranar qiyama za'ace da ita ta shiga aljanna ta duk qofar da takeso(cikin qofofin da aljanna take da su)*
_________________________
*Babi na sha biyar*
Ita yace ta soma shiga ta gayawa hajiya babban zai shigo su gaisa,ta gyada kai ta dauki jakarta ta rataya sannan ta fice,binta yayi da kallo yana duban yanayin salon takunta,komai a nutse kamar wadda ke qirga adadin takun har ta shige gidan sannan ya dauke idonsa gami da lumshesu yana sauraren zuciyarsa kana a hankali ua budesu