Sashe 34
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaisawa sukayi ta yiwa hajiyan sannu da jiki sannan tace
"Don Allah ko zaki taimaka min na daga hajjaju zan bata ruwan zafi zata sha magani lokacin shan maganinta ya kusa,gashi yaya ammar ya fita bai shigo har yanzun"
"Ba komai yarinya,Allah ya sawwaqe,raihana jeki ku dagata"
"To" ta amsawa hajiyan sannan ta ajjiye kayan hannunta tabi bayanta zuwa dakin.
Tare suka daga hajjajun da budurwar mai suna fatima,taso tafiya amma fatiman ta daj tsareta da surutu,ta lura mai yawan magana ce
"Taku zata zo daya da sisi na" raihana ta raya cikin ranta.
Da kaya a hannunshi ya shigo dakin fatiman ta karba tana masa sannu da dawowa,raihana ta miqe tana musu sallama zata fice lokacin da yake tambayarta waya daga hajjajun ta gaya masa ita da raihana ne,tana bakin qofar ficewa ya biyo bayanta,ya cimmata lokacin da take gab da shiga nasu dakin
"Amma ai ko godiya kya tsaya 'yammata nayi miki ko?"
"Wa ya gaya maka ni budurwa ce?,matar aure ce ni" ta fada don ta soma lura da take takensa,dariya ya saki kana yace
"Ni kuwa bakiyi min kama da matar aure ba sam,amma tunda kince haka muje a hakan,nima mijin aure ne"
"Mun gode Allah ya saka da alheri,kuma don Allah idan ba zaki damu ba zan iya samun lambar wayarki?"kai ta kada ta tura qofar dakin nasu tana shirin shigewa tace
" bani da waya"sannan ta maida qofar ta rufe.
Idanun hajiya na kanta "ke da waye kike cewa baki da waya" kamar ba zata amsa ba sai kuma tace
"Wani ne hajiya"
"Har yau baki bar kora samari ba kenan raihana,kada ki manta kefa ba yarinya bace,hakanan wanda ya mutu baya dawowa,ya kamata ki haqura hakanan ki barwa Allah lamarinsa ki fidda wani mijin kuma,amir ki masa addu'a Allah ya jiqansa ya gafarta masa ko?" Shiru tayi tana hadiyar zuciya,itakam ta gaji da wannan walagigi haka,tana buqatar bigire guda da zata tsauda zuciyarta kota hutashshe da kanta da zuciyar tata ma.
Sosai fatima ta dinga shige musu,da yake mai surutu ce itama sai nan da nan aka saba da ita,musamman rumana data samu abokiyar yi,su hajiya babban aka fara sallama don haka suka tattara komatsansu suja barsu a asibitin.
Ranar farko da ya soma kiranta tayi mamaki sosai kan inda ya samu lambar wayarta,daga baya kuma tayi zaton fatima ce ta samar masa gun rumana,don data tambayeta dariya ta dinga yi tace kawai ki bashi dama.
Saurarensa kawai takeyi shima don ta huta da surutun taqi kula kowa,amma ji take sam bai mata ba,yadda taji amir ko rabin haka bata ji ammar ba,amma ko banza yana debe mata kewa,saboda mutum ne mai iya labari tsara zancan da ban dariya,wannan dalili yasanya lokaci lokaci idaj taso ta kan daga kiran nasa,duk da shima din ba mai damun mutum bane a waya,don ko gidansu bai matsantawa sai yazo,idan ya tambayeta yaushe zaizo tace ba yanzu ba,yace sai yauahe tace sai nan gaba yakance to Allah ya nuna mana lokacin,hakan kuwa yana mata dadi sosai.
Sosai fatima suka saba da rumana,don tana ziyartarsu lokaci lokaci,duk sanda kuwa zata zo din baka rasata da wani saqo daga hajjajunsu,ta lura matar na sonta sosai,hakan 'yan gidansu ammar din suke sonta,abun har mamaki yake bata yadda suke nuna mata qauna,amma fatima tace yayan nasu ne yakai shekara kusan talatin da takwas babu aure,kuma shine babba a maza,hakanan bai taba kawo wata yace yana so ba,kullum zancansa aure lokaci ne,da kawunsusu ya matsa masa ma zancan aure sai ya fara wasan buya da shi,bai yarda su hadu,da yake shekara goma baya Allah ya yiwa babansu rasuwa,hakan da fatima ta gaya mata yasa ta rage mamaki kan yadda suke nuna mata qauna,don ba wanda fatima bata zo da shi ba yaga anty raihana
.
Rana ta farko data yarje masa ya ziyarceta tare suka zo da abokinsa ko ace amininsa wato maisara,komai nasu iri daya hatta da takalmin qafarsu,hakan shi ya shaida mata qarfin amintar dake tsakaninsu,ya iso mata hannunshi fal da tsaraba daga hajjajunshi,tana mamakin yadda hajiyan ke sonta da ji da ita,amma ba abun mamaki bane yadda ta lura cewa hajiyan naji da ammar din bisa ga dukkan alamu
"Abokina,nifa inaga ayi abun nan da wuri fa kafin kwado ya maka qafa" cewar maisara kenan wanda ke duban ammar,ajiyar zuciya ammar din ya saki yana duban raihanan
"Nima abinda nakeso kenan abokina,saidai gimbiyar ce har yau nake ga kamar ban karbu ba,baka ga da yadda ta amince nazo mu gaisa ba?",maisara ya dubi raihana
"gimbiya raihana,abokina yafa kamu da yawa,ya kamata arage masa wahalar hakanan a bashi dama ya fito ko kuwa?" Murmushi kawai raihanan tayi sannan tace
"Me kuke ci na baka na zuba,gaggawa ai aikim shaidan ne,mubi komai a sannu har lokaci yayi" ajiyar zuciya ammar din ya saki sannan yace
"Shikenan,Allah dai ya nuna mana lokacin"
"Amin"maisara ya amsa musu.
Turmin atamfar da umminta ta siya mata ta hada da turare ta baiwa ammar din tace ya kaiwa hajiyan,don ta rasa me zata baiwa dattijuwar,sukayi sallama bayan ya ajjiye mata kudi shi da maisaran amma sam taqi amsa,don bata taba yarda ta amshi kyautarsa ba tace ta hajiyan ma ta isa
**************
A qalla sun shafe awanni kusan biyu suna waya,raihana na kwance saman gadonta tana duba wata jarida da abba ya gaka dubawa da safe ya bata,don idan ya gama din dama ita yake baiwa,don ya santa da maitar karance karance.
Tayi nisa cikin tunani har rumanan ta iso gareta bata sani ba,sai da ta sanya hannu ta bubbuga bayanta sannan ta dago
" haba sisi?,karatu ko tunani?"
"Amma jarida kika gani a hannu na ko 'yar rainin hankali" dariya rumanan ta saka tana cewa
"Allah ya baki haquri,idan ma tunanin ammar kike wa ya isa ya hanaki,ungo nan yaya rayyan ne yace na baki wayar,yanata kiran naki layin is switched off" kamar tace ba zata karba amma don kada rumanan ta nemi ba'asin abinda yasa wanda bata da amsarsa yasa ta karba din,tana sane ta kashe wayar don taga saqonshi na zai kirata anjiman,juyawa rumanan tayi ta fice tana cewa
"Bari ka dauko mana abincinmu".
Ringing wayar ta dinga yi tana hannunta amma ta kasa dagawa,yadda bata daga ba haka bai fasa kira ba har kusan minti biyar gajeran saqo ya shigo
"Mafi kyau shine ki daga kira na,idan kika qi kuwa duk abinda zai biyo baya kada kiyi kuka da ni" da hanzari ta goge saqon wanda garin hakan har wani kiran ya shigo ta daga bata sani ba,ganin kiran ya dagu din ya sanyata karawa a kunnenta.
Shiru tayi ba tare data ce komai ba
"Ba maqaryaciyar soyayya nake miki ba wadda zata sanyani barinki da wuri haka duk da qoqarinki na nesanta kanki da ni" karo na farko muryarsa ta daki dodon kunnenta tun bayan watanni biyar da sati biyu daidai da tayi rabon da taji ta,murya ce ta musamman cikin kunnuwa da zucuyarta,bawai don tana sonshi ba,a'ah,tunda can dama yadda Allah ya masa baiwar kyau kwarjini haka yayi masa baiwar dadin murya
"Koda ba zaki amsa ba zan isar da saqona gareki,ina sonki har yau raihana,son da nake miki bai taba canzawa cikin zuciyata ba daidai da second guda,ina mai miki albishir din ki saurari isowata nan da sati biyu in sha Allah,bance ki sanarwa kowa ba,kema din don na sake tunatar dake alqawarinmu,ko ince alqawarin da na daukawa kaina wanda nake tabbatar miki wannan karon babu abinda ya isa ya sauyashi banda qaddarar Allah,kiyi bacci mai kyau sahibata" ya qarashe zancansa yana mai kissing din wayar wanda ya ratsa kunnenta zuwa gangar jikinta,ya kuma haifar mata da tashin tsigar jiki wadda ke cakude da tsoro da fargaba,rayyan na nufin nan da sati biyu ya dawo?,hakan na nufin bayyanuwar wani babban asiri dake rufe?,wannan na nufin bayyanar soyayyar da rayyan ke mata ga rumana,abba,ummu da duka sauran iyalin guda uku?,wannan na nufin zata iya zama matarsa kishiyar rumana?,kai ta dinga girgizawa ita kadai tana ji har cikin zuciyarta ba zata iya lamuncewa hakan ba,ba zata iya lamuncewa kallon da duniya zata mata ba,ta tabbatar cewa mutane ba zasu taba bin ba'asi ba,mutane ba zasu taba yi musu uziri ko adalci ba,zasu kallesu ne a butulu maciya amana,a ma ture ta mutanen,shin da wanne ido ita rumana zata dubesu su duka biyun?,ta gwammace da hakan ya faru gwara ita ta rasa farincikinta,kai bama farincikinta ba har zuciyar tata a shirye take ta SADAUKARWA rumanan da su baki daya.
Batasan yadda ta iya sauke wayar daga kunnenta ba,ta dai samu kanta da rarumo wayarta ta kunnata,cikin 'yan daqiqu kadan komai ya hau satinsa,ta lalubo lambar ammar hannunta na rawa ba tare da wani dogon tunani nazari hasashe ko hangen nesa ba
**************
Kusan dakin cike yake da mutane kowa na nashi harkan,wanda hakan ya kawo cikar dakin da hayaniya da surutai,wanda raihana dake kwance quryar gadon rumana cikin dakin nasu take jin tamkar hayaniyar kasuwannin duniya aka hada cikin dakin,hayaniyar tasu babu abinda take bisa kanta sai sukar qwaqwalwarta,wani irin yanayi taji ta shiga tamkar zata bar duniya,sosai jikinta ke wani irin rawa wanda ta tabbatar da a tsaye take babu abinda zaya hanata zubewa qasa warwas.
A hankali zuciyarta ta dinga wani irin bugu da bata taba jin makamancinsa ba,jikinta ya saki baki daya,sannan idanunta suka dinga lumshewa a hankali lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata sanarwa a tsakar gidansu,kunnuwanta basu daina jin amsa kuwwar maganar da mutumin ke fada ba har sai da idanunta suka kammala rufeqa ruf ta daina ji ta daina gani.
Zaune yake cikin daya daga cikin mitocin airphort da ya dauko don ta kawoshi gida,wani irin zumudi yake ji na ya isa gida tamkar zaiyi tsuntsuwa,sai ya danganta hakan da son ganin irin farincikin da ummunsa har ma da abbansa zasuyi idan suka ganshi,mamaki yakeso ya basu,hakan ne ya sanya bai sanar da kowa ranar dawowarsa ba idan ka dauke raihana,gefe guda kuma na zuciyarsa lokaci lokaci na qara gudunta kan wanda take da shi,lumshe idonsa yake ya dafe zuciyar yana tunanin maganar da yake shirin bayyanata a yau ne take zullumi.