Sashe 35
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya bude idonsa daidai lokacin da yaji mai motar ya tsaya
"Yallabai saidai fa muyi parking dole a nan,idan yaso sai na taimaka maka da kayan zuwa qofar gidan naku,don naga layin a cike yake da alama taro ake" a hankali ya dinga bin layin nasu da kallo ba tare da ya furta komai ba,tabbas taro ake,kuma taron yafi kama da na daurin aure,saboda maroqa da yake hangowa,hakanan tufafin mafiya yawan mahalarta taron fari ne,saidai amma bai gane a ainihin wanne gida cikin layin nasu ake taron ba,murya a sarqe yace da driver din
"Ok,ba damuwa" ya fada yana bude qofar tare da fitowa a kasalance.
.
A hankali ya dinga ratsa mutanen yana wucesu,sai ya dinga ganin daidaiku wadanda ya sansu amma babu wanda yacewa qala haka har ya kutsa cikin gidan,a bakin get sukayi kacibus da abbansa na fitowa cikin manyan fararen kanya,tsayawa yayi yana dubansa
"Ikon Allah,kace kai kana tafe,yanzu yanzu muke maganarka nace qila cikin satin nan ko satin gaba zaka dawo ashe ma kana hanya,shi yasa nayita neman wayarka jiya da shekaran jiya kenan bata shiga,saika qarasa ciki yau gidan a cike yake" abban ya fada yana yin gaba,shima din bai iya cewa komai ba baida karsashin yin magana ma ya cusa kansa ciki.
Kai tsaye dakinsa kawai ya lalubi maqullansa cikin aljihun trolly dinsa ya bude ya shiga,takalmansa ya watsar sannan ya jingine jakar tasa tare da fadawa saman daya daga cikin jujerun falon dafe da kansa da haka kurum yaji ya fara sarawa.
Mamaki ne sosai ya kama rumana data wucewa ta qofar tasa ta ganta a bude,cikin wasi wasi ta nufi gun ta tura qofar,mamakinta ya sake daduwa ganin rayyan din zaune,murza idanunta tayi ta juwa tabbatar shine,sai ta saki wani dan ihun murna tare da tsalle tayi gurinsa,a hanzarce ya dago kansa,miqewa yayi ya bude hannayansa ta fada ciki tana cewa
"Da gaske yaya rayyan kaine don Allah?"
"Nine mana rumana" ya fada muryarsa can qasan maqoshi
"me yasa baka fadi kana dawowa ba,ban tanadar maka komai ba,gashi kazo ka tadda mu cikin hidima kaima bakasan da ita ba,munata neman layinka mu gaya maka baya shiga hankalina ya tashi sosai" sai a lokacin ya samu kuzarin yin magana,a gaggauce yace
"Me akeyi?,naga gidan duk mutane"
"Nima sai na baka mamaki yadda ka bamu,daurin auren sisi na ake"
"Sisinki wa kenan?" Ya tambaya cikin jirkicewar tunani,baki ta dan zumburo ba tare data kula da shi ba don kanta na qirjinsa
"Kaji yaya rayyan,wace sisin nake da ita bayan RAIHANANMU"
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:29 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and _________________
_____
*Daga abdullahi dan umar R.A yace:manzan Allah s a w yace"ku biya dan qwadago(ko wanda ya muku wani aiki)tun guminsa bai bushe ba"*
_ibnu majah ne ya rawaito_
_______________________
*Babi na ashirin da shida*
Wani abu yaji ya soki zuciyarsa
"Ya salam" ya bata can qasan maqoshi da murya kamar ta dan maye yana dafe da qirjinsa,take jikinsa ya dauki rawa yaji tsaiwar ma na neman gagararsa,rumana dake jikinsa ta dago tana dubansa jin yadda jikinsa ke rawa ta fara tambayarsa a rude
"Yaya rayyan lafiya?"
"Zaunar da ni ruma,kaina da qirjina" cikin sauri ta kamashi ta zaunar da shi saman kujera tana jero masa sannu
"Yaya dama baka da lafiya?" Kai kawai iya daga mata,ji yayi duniyar na juya masa hakan ya sanya ya maida bayansa saman kujerar ya kwanta rigingine,rawar da jikinsa yake bai fasa ba,lokaci guda wani azababben zazzabi yayi masa kirif,hatta da numfashinsa huci yake fiddawa,idanunsa tamkar wanda aka gambadawa yaji haka suka koma jazur da su.
Ba qaramin tashi hankalin rumana yayi ba cikin rudewa tace masa
"Yaya,ko nayi kiran abba muje asibiti?"
"Kada kimin kiran kowa,bana buqatar kowa" ya fadi idanunsa a rufe,shi kadai yasan kalar azabar da qirjinsa yake masa,wani suya yake masa tamkar an zuba masa garwashi,wani kumburi yaji zuciyarsa na masa kamar zata fashe ta fito.
A hankali yanayin da yake ciki ya soma ta'azzara,rumana ta tsorata sosai,abun tamkar jinnu, ganin yadda rawar sanyin da yake ta fara jijjiga kujerar da yake kai tamkar wanda ke shirin yin jijjiga,babu shiri ta miqe a gigice ta fito don neman dauki.
Harabar gidan babu jama'a da alama 'yan daurin auren sun gama watsewa,karo sukaci da abba wanda ke tsaye yana sallamar likitan daya gama duba raihana yanzun wanda ta suma,babu wanda ya kula cikin jama'ar dake dakin har sai da ummu ta shigo neman rumana ta tabata taji shiru,sai data kai hannunta fuskarta ta lura numfashi baya fita
"Abba,yaya rayyan,yaya rayyan" rumana ta fadi tana nuna bangaren rayyan din da yatsunta idanunta na fidda hawaye cike da tsananin rudewa
"Me ya samu rayyan din umma rumana gayamin"
"Abba baida lafiya,don Allah kazo ka gani kada ya mutu" jin hakan ya sanya abban sanya kai bangaren nashi tare da yiwa likitan umarnin ya biyoshi.
Yanayin yadda yaga rayyan din ya sanya yace da abba
"Shikam bai yiwuwa na dubashi a nan,abinda zaifi kyau mu daukeshi mu wuce da shi asibiti" ba tare da bata lokaci ba abban da likitan suka kama rayyan din suka fice da shi.
Gaba daya gidan sai ya koma na jajjabi,wadansu ma basusan da dawowar rayyan din ba sai lalurar tashi wanda suka fi danganawa da cewa dama can baida lafiya ne ya taho gida a hakan
"Oh Allah mai yadda yaso mai juya lamura,dazu dai muna cikin farincikin daura auren raihana tashi daya kuma ya juye ya koma mana tashun hankali,ya Allah ka kawo mana da sauqi"cewar maman rumana
" babu yadda Allah bai iya ba ai,da mutuwa ce ma haka duka zata zo mana ba zata"inji ummu.
****************
Zaune take gaban raihanan wadda keta bacci yayin da qarin ruwan ke shiga jikinta a hankali,jin duniyar take gaba daya ta quntace mata guri daya,rayyan ba lafiya raihana ma haka?,har gwara jikin raihana ma da kyau akan na rayyan din,don shi tun jiyan bai farfado ba,tana zaton hakan ne ma ya sanya su abba suka hajata zuwa ta ganshi.
A hankali ta sanya hannunta ta share hawayen fuskarta kana ta miqe don shigewa bandaki ta daura alwalar sallar azahar sai taga raihanan ta bude idanunta,ta dawo da sauri ta koma ta zquna a inda ta tashin,fuskarta dauke da dan murmushi tace
"Yauwa sisi,don Allah ki tashi ki warke hakanan,na rasa da wanne zanji,da cutarki ko data yaya rayyan" shiru tayi tana duban rumanan din bata san ya dawo din na,hakanan batasan me ya sameshi ba,wai rayyan baida lafiya shima?,take ta dinga jin ya kamata ta warke din don kauda zargi,ya kamata ta warke don hankalin rumana ya kwanta,ya kamata ta warke don kowa yasan matsayinsa,kowa ya kama rayuwar da Allah ya riga ya tsara masa
"Me ya samu yaya rayyan din?"
Ta girgiza kai cikin sarewa
"Nima ban sami ba har yau,don abba ya hanani zuwa,idan da lafiyarki qalau nema nasan zaya barmu muje mu biyun".
Sai ta saki murmushin qarfin hali,ta tattaro duka ragowar qarfin da ya rage mata ta yunqura ta tashi rumana na cewa tayi a hankali
"Na riga da na warke fa sisi kada ki damu,taimaka ki zaren ruwan nan na shiga bayi" a hankali ta kama hannun nata ta cire mata ruwan kamar yadda likitan ya nuna mata,ta kamata don taimaka ta miqe sai ta yi dariya kana ta tsaidata
"Nifa da qwarina,bari kiga" tayi maganar tana yunqurawa tare da miqewa cikin dakiya,ji take iska na yawo da ita amma haka ta daure ta shige bandakin,wani dadi ya kama rumana ganin raihanan ta miqe har ta taka da kanta,fatanta Allah ya sanya rayyan ma haka.
Ta fito daga bandakin a hankali rumana ta dubeta
"Yan gidansu ammar nata zuwa sisi,hankalinsu ya gaza kwanciya,gaskiya ki godewa Allah,sun kasa sukuni gaba daya amaryarsu ba lafiya" murmushu tayi tana zura hijabin da rumanan ta miqo mata,ita kanta ta dade tana yaba irin qaunar da suke mata,ko donsu zata zauna da dan uwansu zama na gaskiya da amana
***********
Ajjiye file din likitan yayi bayan ya gama 'yan rubuce rubucensa a jiki,a hankali ya tako ya iso bakin gadon da rayyan din ke zaune bayansa jingine da filo ya zauna gefansa.
Dubansa yayi na 'yan wasu daqiqu sannan yace
"Rayyan" kai tsaye saboda abokinsa,abokin da zai iya kira kai tsaye aboki na kusa da shi sosai wanda sukan iya musanyan ra'ayi shawarwari da kuma sirrika,abotarsu ta samo ne tun tafiyarsa england na farko,inda suka hadu da shi mukhtar da amir.
Bai amsa ba face daga shanyayyun idanunsa da yayi ya dubeshi,yasan babu lallai ya amsa din saboda haka ya dora
"Wacce iriyar damuwa ka shiga haka lokaci guda mai zafi wadda take barazana da lafiyar zuciyarka?me yasa kake son cutar da zuciyarka?" Mai makon ya amsa masa sai ya hau girgiza kai na tsawon lokaci ba tare da ya furta ko kalma daya ba
"Rayyan,ni abokinka ke ta wani bangare amininka,ka gayamin me ya sameka ko meke faruwa da kai?,barin kashi a ciki baya maganin yunwa" tabbas haka maganar take,saidai duk sanda ya rasa ta yadda zai iya furta maganar,saboda duk lokacin da yayi yunqurin hakan sai yaji wani abu yazo ya tokare masa qirji,numfashinsa ya hau kai komo ya fara jansa da qyar.
Ya dade idanunsa a rufe hannayensa cikin na mukhtar,a hankali kuma karon farko yace
"Laifi nayi don ka sota kuma naso 'yar uwarta wadda ba ciki daya suke ba?,laifin me na mata ta yanke mana irin wannan mummunan hukuncin?,wanne irin tsana ta yiwa tarayyarmu da ta yi mana wannan kisan mummuqen?"
"Wacece?" Mukhtar ya tambayeshi kai tsaye
"Mukhtar raihance.....raihana ta qini saboda rumana......" Sai maganar ta maqale masa,wani abu ya tokare masa qirji,nauyi yaji an azawa qirjinsa wanda ya sanya shi jan numfashi da qyar,abun yayi matuqar bawa mukhtar tsoro,a tsorace ya dinga cewa
"Kabar idanunka suyi kuka mana rayyan ko zaka ki sanyi,kada ka bari ciwo ya kamaka rayyan pls mana".