Sashe 55
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_______________________
*Daga abu hurairah R.A yace,manzan Allah S A W yace "yana daga cikin abinda yasa aka halakar da wadanda suka gabacemu,yawan tambayoyinsu(tambayar qure da tambaya kan abinda baida ma'ana ko fa'ida),da kuma sabawa annabawansu"*
______________________
*Babi na talatin da tara*
A hankali ta bude zara zaran idanunta,rumana ce tsaye dafe da hannun nata tana kallonta,kai ta girgiza sannan tace
" kullum ranar Allah sake nunan kike DANGANTAKAR dake tsakaninmu bata kai haka ba,kina sawa ranki cewa akwai wani abu da ya isa ya kutsa cikin alaqarmu,alaqar da babu wanda ya ginata face Allah subhanahu wata'ala,alaqar da dangantakar da Allah kadai yasan yawan qaunar dake cikinta,me yasa raihana?"kai take girgizawa hawaye na son qwace mata,cikin raunin murya tace
"Ba haka bane rumana ki fahimceni,kishi mugun abu ne,mugun ciwo ne da baka da qarfin da zaka iya dakatar da shi,ina tsoro kada ya zama silar rusa kyakkyawar alaqar dake tsakaninmu,me yasa ba zamu ci gaba da zama kamar yadda muke ba?,me yaaa za kiyiwa rayuwarki gibi ki gayyato qata cikin duniyarki?" Kai ta kada itama tana murmushi mai taba zuciya gami da janyo hannun raihanan daga cikin motar tana cewa
"Tabbas kishi halitta ce,kuma kisan kowanne jinsi na halitta walau mutum ko dabba yana da ita,saidai ya rage naka ka sarrafashi ta hanyar data kamata ko akasin haka,qarshe dai sakamakon kai zai dawowa,bana dana sanin sadaukar da farinciki ga wanda ya sadaukar min da nashi farincikin ba tare da na san da hakan ba ma,tabbas ina son rayyan ina kishinsa amma ki sani cewa ke ta dabance raihana,bazan kuma taba zama butulu ba,kome duniya zata kirani da shi wannan ya rage nasu"
"Amma rumana......"
"Shshshsh" rumanan ta fada tana dubabta bayan ta dora yatsanta kan lebanta idanunta sa suka dan sauya suna duban raihana
"Bana buqatar sisi ki sake cewa komai kan wannan magana,aski ya riga yazo gaban goshi,nan da jibi magana ta qare" tilas ya sawa bakinta kwado rumana na jaye da hannunta taci gaba da binta har cikin gidan tana hadiyar zuciya.
A cike ta tarad da gidan har abun yaso bata mamaki,tamkar bikin fari za'ayi,ta daure zuciyarta ta gaggaisa da jama'a saidai bata ga ummu ba aka ce mata tana dakinta,bazata iya wucewa sabgarta ba bata ga uwar tata ba sabida haka kai tsaye ta wuce dakin nata.
Da sallama ta tura qofar dakin ta shiga,idanunta fes kansa yana zaune gefan gado sanye da shadda ruwan qasa wadda tayi matuqar amsarsa,ya daga kai a hankali daga danna wayar da yake yana amsa sallama,idanunsu suka jone guri guda,wata faduwar gaba taji wadda ta sanyata sakin mariqin qofar ta koma da baya da niyyar ficewa yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta da narkakkun idanunsa,kewa ke damunsa sosai,ya jima bai sata a idanunsa ba ga kuma rumanan itama bata kusa,ji yake kamar ya janyota ya sanyata cikin qirjinsa,sosai tayi masa kyau don haka yaci gaba da kallonta yana sauke numfashi shi kadai.
"Muryar wa nake ji kamar ta raihana?" Cewar ummu wadda ke fitowa daga bandaki da alu alwala tayi,maganar ummun ita ta katse mata aikata abinda tayi niyyar yin,sai ta qarasa shigowa dakin tana jaddada sallamarta kanta sunkuye a qasa saboda ta gaji da mayen kallon da rayyan din ke jifanta da shi babu gaira babu dalili
.
Aladabce kamar yadda ta saba ta gaida ummun,ta amsa mata cikin kulawa tare da tambayarta yadda ta barosu,miqewa ummun tayi tace bari nayi sallah lokacinta har ya qwacen,ki jirayeni na idar akwai saqon da zan baki inji mai martaba(kakan rayyan na nijer)"kai ta gyada mata sannan tace
"To ummu" ta waiwaya ta dubi rayyan
"Kai mun gama da kai ko da saura" ido ya dan lumshe sannan ya budesu
"Akwai saura amma ba damuwa zan qarasa rubutasu anan saboda idan na fita ba lokaci,ina da baqi zai iya yiwuwa na mance"
"To yayi kyau" ummun ta fada sannan ta juya ta tada sallarta.
Tsit ne ya biyo baya,tana takure saman carfet gata a saitinsa,yayin da shi kuma ya tsareta da ido yana son ta daga kai su hada ido saboda saqon da yakeson aika mata,kamar tasan da hakan tayi qasa da kanta tana wasa da yatsunta da suka sha lalle,gaba daya jinta take duniya ta takureta gu daya,ji take kamar ko ina yi ake da ita,ji take kamar kowa zargi da zaginta yake,hakan shike qara quntata mata zuciya.
Saidai duk da haka zuciyarta na mata zillo tare da gaya mata kallonta fa ake daga gefw guda,saita daga kai a hankali don ta tabbatar,bai kuwa yi qasa a gwiwa ba ya aika mata da saqon take kuwa ya isa gareta har kwanyarta wanda ya haifar mata da wani kasala ta daban,ta janye idonta tare da lumshesu taja numfashi can qasa ta sauke,sai ta maida kanta ta kwantar kan qafafunta bata sake muradin kallonsa ba,don ta fahimci abun nashi mugunta ne,duk lokacin da tayi niyyar wancakali da shi sai ya ruguza mata shiri,duj sanda zuciyarta ta soma jin zafinsa sai ya sauyawa zuciyar tata akala,ta dade da sanin rayyan dan garari ne,bai iya riqe soyayya da sauqi ba,bai iya sanya wajen cimma muradinsa ba.
Cikin wannan yanayin ummu tayi sallama,sif dinta ta bude ta fiddo wani dan akwati mai azabar kyau ta ajjiyewa raihana
"Ke da 'yar uwarki ne ita na bata nata" tun kafin ta bude ta soma godiya
"Saiki duba" inji ummu ta fada tana ficewa a dakin,kamar wadda aka tsikara ta miqe itama ta dauki akwatinta tana shirin bin bayanta,cikin azama ya sha gabanta tamkar zasu hade jiki har sai da tayi baya
"Haba yarinya baki isa ba,ai sai kin biya farashin abinda kika yimin" cikin rashin fahinta take dubansa,girarsa ya dage sannan yace
"Kina nufin duka abinda kikayi baki sani ba?,ok zan lissafa miki,na farko kinyi tafiya babu izinina,na biyu kin dauke min mata ta biki can,na uku kuma daga dawowarki kinzo kin ishi mutane sa kallo har sai da kika......."
"Don Allah ya rayyan ya isheni matsa na wuce"
"Ta qarfi ce hanyar" ya bata amsa kai tsaye,sai ta raba gefansa zata wuce ya tare hanyar ta sake komawa dayan side din nan ma ya bita ya tare,haka suka dinga yi har ta gaji sai kawai ta saka masa kuka,abinda yake nema dama kenan,baiyi qasa a gwiwa ba ya tarairayota jikinsa
.
Zamewa taso yi saidai ina tuni ya soma kashe mata jiki,sai ta samu kanta da yin luf kan qirjinsa tana sauke ajiya zuciya kafin daga bisani ta sanya dukka hannayanta ta tureshi,sai yayi baya luuuu kamar zai fadi sai kuma ya turje tare da fadin
"Wash" waiwayo tayi ta dubeshi ga zatonta ko wani abune ya sameshi,sabanin haka ta gani,ya zuba mata ido yana dubanta,suna hada idon ya kashe mata idonsa daya hadi da sakin murmushi qasa qasa yace da ita
"Raiha ta!",takaici taji ya kamata,da hanzari ta dauki akwatinta ta fice hawaye na layi kan fuskarta,shi din ma bai hanata ba don yasan meke damunta,zuwa wani lokaci yasan dole kukanta ya tsaya.
Haka ta dinga wuce jama'a kanta sunkuye don kada suga fuskarta,Allah yasota ma duhun magariba ya soma kawo jiki don haka ba wanda ya kula har ta isa can bayan gidan,wajen babu kowa hakan yasa tayi zamanta a nan,Allah ya sani tana qaunarsa har cikin jininta,to amma tana jin hakan sam bai da wata fa'ida tunda sukayi tarayya da 'yar uwarta,baida amfani bai kuma kamata su raba abu guda da kowacce keso ba,tana ganin mafi kyau ta sallama mata,saidai sam rayyan ya ruguza tsarin ya hana damar,itama kuma rumanan ta biye mishi saboda farincikinsa.
***************
Washegari aka gabatar mata da kamu mai matuqar qayatarwa,yare uku ne suka hadu agun saboda haka dole abun ya burgeka,kowa na qoqarin nuna tashi bajintar da kuma al'adar,ga hausawa,ga buzaye ga uwa uba iyayen gida bare bari wato KANURI.
Kusan komai da raihanan ta saka ko tayi amfani da shi iri daya ne da na rumana,wannan kuwa tsarin raihanan ne,rumanan taso ta turje amma ta kafeta da manyan idanunta tana kallonta
" ni da kika tursasawa,kika lanqwasani dole,kika wajabtamin aikata abinda na dade da haramtawa kaina shi banda baki ko ikon bijerimiki sai ke?"
"Ba haka bane sisi,amarya daban take kuma komai nata ya kamata ya fita daban" kai ta shiga girgizawa qwalla ta tarar mata tana shirin zubowa
"Banda wannan amaryar,amaryar dake shirin auren mijin 'yar uwarta?" Da sauri itama ta shiga kada mata kai
"A'ah,kada muyi haka dake raihana,aure zakiyi tamkar kowacce mace,namiji zaki aura kamar kowanne namiji....kada ki kuma daga wannan maganar na gaya miki,kaya na amsa zan kuma yi amfani da su don faranta ran sisi na" ta fada tana kama hannuwanta,kai raihanan ta kada tana fidda murmushin yaqe yayin da rumanan ta mayar mata da martani.
Qememe taqi kowanne dinner party ko walima don ta bangaren qawaye babu daya data gayyata,tilas rumanan ta zuba mata idanu,daga kamu babu abinda suka dada sai yini da daurin aure.
Ranar juma'a aka daura auren kamar yadda aka daura na rumana,qarfe sha daya na rana alqawarin ubangiji ya tabbata,
RAYYAN ya zama miji ga RAIHANA.
Tana zaune gefan gado wanda tunda ta shirya take zaune kai kamar mutum mutumi ta kasa motsawa,sanye take cikin wani swiss voile dan gasken peach colour wanda yasha aikin sea grean,tayi kyau qwarai kwalliyar da aka mata ta karbeta,saidai sam hankalinta baya wajen,saboda tunda rumana ta fita bata sake ganin ta ba har aka kammala daura auren,idanu taketa rarrabawa ko zata hangota amma ba ita.