Sashe 42
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido ya kafeta da shi,zahiri ta masa kyau amma wani abu mai kama da fushi na son danne zuciyarsa ga barin ganin haka,har yau halayyarta na nan,miskilancin tsiya zurfin ciki da sanyi,natural choculet colour skin nata,murmushi a maimakon dariya ko bada amsa,ta ammali da abu natural da sauqaqawa kai kan abubuwa.
Tsaki ya ja a bayyane wanda hakanan yaji wani haushin ya sake turniqe shi,sarai ta jishi saidai ko a fuska bata nuna alamun taji din ba,tunda bata ga wani abu data masa wanda zai mata tsakin ba,dacin ran da yake bata san masa dalili ba,shi sani ne baiyi ba amma tafi kowa qyamatar tarayyarsu waje guda
"Ke.....rayya"
Sai ta daga dara daran fararen idanunta ta watsa masa,sannan ta tsaidasu qyar a kanta tana jiran abinda zaya fada,wani yarrrrr yaji cikin jikinsa har ya haifar masa da raunin da sai daya lumshe idanunaa sannan shima ya sake watsa mata su tamkar suna son nunawa juna baiwar idanu da Allah ya bawa kowannensu.
Tamkar ramuwa yayi gareta,itama sai ta janye nata idon ta maida kan fuskar islaha data yagi tissue ta fara goge mata fuskarta da bakinta daya baci da maiqon chips
"Ke wacce iriyar baqauyiya ce?" Sai ta sake dagowa ta dubeshi ba tare data ce komai ba,ya lura halin nata ne ya motsa kuma ya tabbatar ba zata ce komai din ba sai ya dora
"Tunda kika ganni a nan kinsan cewa abinci nazo ci ko?"
"Ba gidan saida abinci bane wadanda suke neman custumer koda yaushe da idan sunga mutum zaune zasu zo su tambayeshi me yakeso...."kai ya kada
" kinyi na farko kinyi ka qarshe da zan miki magana kice zakiyi qoqarin maida min,ki hada min breakfast yanzun nan"yayi maganar yana dora qafarsa daya kan daya tare da yin relaxing kan kujerar yana dubanta.
Sauke islaha tayi daga kan cinyarta tace taje ta gaida abba gata nan zuwa su tafi unguwar,miqewa tayi tana duba girmansa na yayanta,girmansa na wanda ya girmeta,girmansa na mijin sisinta abban takwararta,ba don haka ba tana jin da yau saidai ya rube a gun,don dacin ran da yake fama da shi bai shafeta ba.
Tea ta hada masa ta ajjiye gabansa sai ya dubeta
"U know bana shan tea da madara ko?" Ta manta da hakan sabida haka ta janyeshi daga gabansa ba tare da tace komai ba,haushin shurun da take masa yake ji a badini,so yake tace wani abu amma ta qiya,tana cikin zuba masa black tea a cup wayarta ta dauki tsuwwa,cube uku ta zuba masa maimakon daya garin sarin daukar wayar,yana kallo kuma baice da ita komai ba,sultan ke kiranta,sai ta saki murmushi a hankali tace
"sultan"har ga Allah bata ma san ya fito ba,sai kawai ta tura masa kwanukan duka abinda ta dafa din gabansa ta sauko daga dining area din a gaggauce tana amsa wayar ta shige daki.
Binta yayi da kallo yana jin kamar an shaqeshi,lallai babu shakka yarinyar nan ta rainashi,zai ko yi maganinta,yaja qwafa ya zubda tea din ya hada wani.
Kusan shi kadai ya iya sha,daya gama maimakon ya bar gurin sai ya zauna yana tsimayen fitowarta,yana jin yau sai ya sauke duk wani bacin ran da yake ji,yana zaune a hakan hannayensa harde a qirji yana duban qofar dakin ummu ta fito riqe da islaha,dubansa tayi
" af,ashe ka gama,kaje to abban naku ma ya gama"
"Ok kawai yace ya miqe ya wuce sashen abban,ummu kuma ta qwalawa raihana kira tace ta fito su tafi kada suyi rana sosai
Duk ta taras dasu kuwa a gidan,anty sauda sabira da fatima sai salim qaninsa da halima,murna suka dinga yi da ganinta,suka rasa inda zasu sanyata,haka ma hajjaju wanda jikin nata yayi dama dama,farinciki duk ya cikasu,abinci da abin sha har ta rasa da wanne zata fara,islaha na gunsu babyn ta burgesu,fatima tace
" anty ki bar mana ita don Allah"murmushi ta saki
"Nima arota nayi fatima" hajjau ta danyi murmushi
"Da tuni taki ce raihana,ammar bai kyautatawa rayuwarmu ba baki daya" sai qwalla ta soma qoqarin fita,da sauri raihanan ta dubeta
"A'ah hajiya,don Allah kada ki sake sanyashi a wani bala'in,kada ki zubar masa da qwalla wallahi abun sai yayi masa yawa,addu'a zaki ci gaba da yi masa"
"Hmmm,raihanatu kenan,bakisan duk cikinmu babu wanda yasan inda ammar yake ba ma,ko a waya bamu samunsa?" Batun ya girgizata amma duk da haka ta kwantar musu da hankali tare sa qarfafa musu gwiwar yi masa addu'a.
Basu baro gidan ba sai la'asar,shima da qyar suka barta ta taho cewa sukayi sai dare zata koma.
Tun azahar ya rufr affice dinsa,hakanan ya kasa yin kowanne aiki,duk motsin da yayi sai ya hangeta sanda take ambatar sunan tare da qoqarin amsa wayar da gaggawa.
Yana bakin gun da ma'aikatan ke ajjiye motocinsu driver dinsa ya qaraso da sauri cikin girmamawa ya rusuna
"Alhaji,ina zamu je" hannu ya daga masa
"Yi tafiyarka gida zan wuce,sai Allah ya kaimu gobe" ya fada yana miqa masa hannu,da sauri ya saka masa a tafin hannun nasa yana fadin
"Allah ya kaimu yallabai" ya bude motar ya shige.
Maimakon ya koma gida sai ya tsinci kansa da karya akalar motar tasa zuwa gidansu,ummu na bakin kintchen zaune tana zuge zogalen da za'a yiwa abba tuwo da shi lantana na daga ciki tana hade haden abincin dare ya shigo,daga kai ummu tayi ta dubeshi
"Lafiya rayyan ka dawo gida a irin wannan lokaci?ko jikin ruman ne?" Kai ya girgiza yana dafe kujerun falon
"A'ah ummu,kawai na gaji hutawa nake son nayi"
"To,dama jiki da jini ai yana buqatar hutu,banda lafiya ma da Allah ya baku ga aikin wani companyn ga aikin ginin naka,Allah dai ya qara lafiya kawai"
"Ameen" ya amsa yana sosa tsakiyar kansa da maqulli
"Ummu akwai kuwa irin lemon mangwaron nan?"
"Eh ai kuwa kaci sa'a,jiya da daddare raihana ta hadashi saboda abbanku ma na sonshi" turus ya danyi,yanzu komai yace a bashi raihana ce tayi,baisan sanda yace
"Gidan nan babu wani meyin abu ne sai raihana?"
"To waye a gidan?,daga ni sai ita sai lantana,tafi lantana kuzari da himmar aiki,ni kuwa indai tana nan bazata taba yarda nayi wani abu ba...."
"Shikenan,kisa lantanan ta kawomin ina gun lilon can" ya fada da sauri yana juyawa sai kuma ya waiwayo
"Halan islaha tayi bacci?"
"Ai tun safe suka fita ita da mamanta,suna gidan su yaron can data taba aure,taje duba mamarsa ba lafiya,wallahi tunda akayi abun nan har yau jikin yaqi dadi" wani abu ya shaqa,har ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa yasa kai ya fice
.
Guri ne mai kyau daga gefan gidan wanda yayi kama da garden,saidai kana iya hango harabar gidan duka,wata da'ira aka yi masa mai kyau da shuke shuke tsakiya kuma qananun fareren dutsuna na wuta,sai teburi na qarfe mai kyau da kujerunsa guda hudu,gafe daya kuma lilo ke qwaya daya amma irin dogon nan,duk aikin raihana ne lilon kuma saboda islaha ya siya aka saka shi,kofin glass guda ya cika da lemon sannan ya jingina bayansa da lilon dake lilashi kadan kadan yana kurba,sanyinsa da dinsa suka ratsa qwaqwalqarsa
.
Kan idonsa motar raihanan ta shigo gidan,a hankali ta samu gefe guda ta ajjiyeta sannan ta kashe,mintina qalilan qofar motar ta bude ta fito sabe da islaha da tayi bacci ta kulle motar sannan ta nufi cikin gidan.
Ganinsa kawai tayi a gabanta,hannayensa harde da qirjinsa ya dubeta yana fidda huci kadan kadan,hannu ya miqa mata don ta bashi islaha,ganin bata fahimta ba ya sanyashi sake matsowa daf da ita har tana sheqar qamshinsa,ya sanya hannayensa don dauketa daga kafadarta wanda garin hakan hannun sa mai dauke da kwantacciyar gargasa ya shafi wuyanta,wani shock taji wanda ya sanya ta sakar masa yarinyar ba shiri ta ja baya tana dubansa.
Sai da ya dorata saman kafadarsa sannan ya dubeta
"Daga yau kada ki sake fitarmin da yarinya yawo,idan kin tashi bibiyar gidajen ki tafi abunki ke daya ba damuwata bace,amma bada yarinyata ba" ya kewayeta ya wuce ta bishi da kallo ba tare data iya cewa komi ba,sai wani abu yake sai kace wadda ta kashe masa wani nasa?.
,muqullin motarsa ya saka ya bude ya kwantar da islahan a baya sannan ya dawo ya shige mazauninsa ya tashi motar suka fice a gidan yana faman hadiyar numfashi shi daya.
Jin falon shiru babu kowa ya sanyashi hayewa sama don yasan tana can,a dakinta ya sameta kwance tana waya da wata qawarta jamila meela da suka hadu a saloon,ta gayyaceta birthday dinta amma saboda batajin dadin jikinta ba zata iya zuwa mata ba,shigowarsu ne ya sanyata katse kiran,ta miqe daga kwanciyar da take bayan ta ajjiye wayar tana duban rayyan din dauke da mamaki,ya samu gefan gadon ya kwantar da ita sannan ya qaraso gefanta ya zauna
"Daddy ya na ganka da islaha,yaufa sunday?"idanunsa ya watsa mata sannan yace
"Wai yarinyar nan me ta tsare miki da kika wajabta mata dole tayi weekend a waje?,ko ni nace miki na gaji da ganinta ne ko ke kin gaji da ita?,bama wannan ba daga dawowata baki tambayi komai ba sai na dawowar raihana?" Ta karyar da kai
"Ayyah,afuwa yaya ba haka nake nufi ba" bai bi ta kan maganar tata ba ya sanya hannunshi ya shafi wuyanta da goshintan sannan yace
"Ya jikin naki?,ina fata da sauqi" murmushi tayi tace
"Alhamdulillah"
"Masha Allah" ya fada yana miqewa,drower din da yake ajjiye magungunansa ya qarasa ya jawota ya balli uku kala daban daban,sannan ya qarasa gaban 'yar qaramar freezer dake dakin ya ciro ruwa mara sanyi ya balle murfin ya kora maganin
"Yaya ina fata kaima ba jikin naka bane,naga ma yau ka dawo ba lokacin dawowarka ba" dan qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarsa yayi
"Babu wani jiki,kawai hutawa nake so nayi,ina buqatar hutu" ya fada yana balle botiran rigarsa ya cire ya janyo towel ya rataya
"Na hada maka ruwan wanka to"dakatar da ita yayi
" a'ah my angel,kema kina buqatar hutun,ki barshi zan hada"kai ta gyada tana murmushi tana kallonsa har ya shige toilet din
****************
Da sauri sauri ta fito daga dakin saboda kiran da taji ummu na qwala mata sanye da kayan bacci masu sulbi ruwan hoda mai haske mai dogon hannu iya cinya da dogon wando,kanta matse da qaramin ribbom.