← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 66

Sashe 16

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yammata ne ke shigowa layin su uku,kallo daya zaka yi musu ka fassara su waye su,don duka cikinsu babu wadda babu tabon bleeching bisa fuskarta,biyu daga ciki sanye suke da atamfa,yayin da dayar ke sanye da material,dinki ne aka yi musu na badala wanda bashi da maraba da babu,musu suke ko me suke oho Allah masani,amma kana iya jiyo hayaniyarau tun kafin su qaraso inda kake,suna tafiya jikinsu ta kadawa,duk da hirar da suke kwararawa hakan bai hanasu tafiya suna taunar chewing gum dinsu ba,da haka har suka qaraso inda motar rayyan ke fake,daya daga cikinsu taja birki tana cewa,"bari ja sake gyara fuskata a nan"saboda baqin glass ne basa gano na ciki,biyun ma dawowa sukayi suka dan dubi layin sukaga ba jama'a,ba bata lokaci suka hau gyara makeup dinsu jikin glass din motar,rayyan na zaune yana kallon ikon Allah har suka kammala suka qara gaba,idon nashi ya sake lumshewa abun na bashi dariya dariya
_ban taba zaton zanyi katarin samun matar aure irinta ba a wannan zamanin,sai gashi dare daya Allah ya yimin kyauta mafi tsada_ zancan amir ya dawo masa fes cikin kwanyar kansa,sai ya bude ido a hankali yana dubi seat din da ta zauna,wayarta na gefe da alama mantata tayi,yasa hannu a hankali ya dauka,ko daya babu irin qyale qyalen nen da ake cikawa jikin waya,ta haka yake gane wayarta data rumana tunda iri daya ce sai banbancin cover da suke sawa lokaci lokaci,hoton heart ne kawai pink guda biyu mai qyalli a jiki a fuskar wayar daga gefe da kuma bayanta wajen murfi,babu password cikin wayar don haka kai tsaye ya bude,contact nata ya duba duka numbers din da suke kai basu wuce talatin ba,suma din duk na 'yan uwanta ne mai duguru da wasu daga take hulda dasu a nan,number din amir kawai ya gani da sunan namiji,ya sauka ya shiga gallery dinta,nan din ma hotunan ummu abba da mamanta ne fanna,sai na zainab qanwarta,sai nata sai na babbar 'yar uwa rumana,wanda majority hotunan rumanan ma sunfi naya yawa.

Murmushi yake yana duba hotunan,idan yazo kan wanda sukayi tare yakan tsaya ya kalla sosai kana ya wuce,tsaki yaja lokacin da ya tuna binciken waya kenan ya mata ya maida wayar da sauri ya ajjiyeta yana istigfari saboda binciken da ya mata bada izininta ba.

Rumana kawai ta taras a falon tana cin abinci,murmushi suka yiwa junansu sannan rumanan ta amsa mata sallamarta,zaro ido raihana tayi"sisi kada dai kice min sai yanzu kika tashi?"ta fada ganin kayan data kwanta barci sune a jikinta"
"Ke dai bari,gajiya ce ta dannemu in gaya miki" ta bata amsa tana bula ruwa pure water mai sanyi ta soma sha,darita raihana ta qyalqyale da ita
"Tab,kice yau ya rayyan zaiga matarsa qazama,to tare muke yana qofar gida yana jira a masa izini ya shigo" qwarewa ramanan tayi,ta saki ruwan tana zaro ido
"Bama haka da ke sisi,da gaske kike?" Hararar wasa tayi mata
"Zaki gasgatani idan kika ganshi cikin falon nan".

Dire kwanan abincin nata tayi tana qoqarin shigewa toilet din dake falon,da sauri raihana ta tambayeta" ina hajiyan take?"
"Tana bandakin tsakar gida" ta qarasa shigewa tare da rufe qofar,girgiza kai raihana tayi,rumana kenan,tana shirin fita sukayi kacibus da hajiyan na shigowa sai ta gaya mata zuwan rayyan din
"Kice mai gidana ne da kansa,ke cene da shi ya shigo mana" inji hajiyan tana murmushi,raihana ta amsa da to sannan ta kuma ficewa.

Yana zaune dai cikin motar shiru,sai sanyin a.c da ya karade motar
ta qwanqwasa glass din,ya danna madanni yayi qasa da shi yana duban qwayar idonta,bata iya wannan kallon ba don haka ta maida qwayar idon nata kan sitiyarin motar bayan ta zira hannu ta dauki wayarta tana cewa"hajiya tace ka shigo"
"Tsayani mana mu shiga tare,ko so kike na bata?" Ya fada yana fitowa daga cikin motar ganin tana niyyar shigewa ciki ta barshi,tsayawa tayi har ya qaraso daidai kafadarta sannan yace"muje to".

A hankali suke takawa cikin gidan,tafiya suke kamar wadanda basu son shiga cikin gidan haka nan,suna cikin zauren gidan wayarta ta fara tsuwwa,ta duba mai kiran,amir ne,sai ta rasa ta yadda zata amsa kiran,saboda bata iya amsa waya indai ta wani bane gaban mutane,saidai ko rumana,kuma batason ta qi daga wayar sabida tun dazun amir din ke kiranta lokacin tana lacture,tana ganin qima da girman amir din,batason tayi masa wani abu ba daidai ba har yaji babu dadi ya gayawa rayyan,a sanyaye ta daga ta kara wayar a kunnenta,ajiyar zuciya ya fara saki sannan yace
"Alhndlh,ina nan cikin zulumi na jiki shuru tun dazun inata kira ba amsa"
"Afwan,ina cikin uziri ne"
"To Allah yasa kin gama don muryarkin nan mai sanyi nakeson ji"
"Eh to,da saura kam"
"Omg,shikenan amma pls idan kin kammala ki kirani"
"Ba damuwa"
"Na gode,ki kular min da kanki da kyau"
"K" ta amsa masa tana qoqarin katse kiran.

A hankali ya dauke idonshi daga kanta tare da yin sallama cikin tsakar gidan.

Har hajiya babba ta shimfida masa carfet duk da kujerun dake falon
"Maraba da ango na,hala dai ni ka biyo ba waccar 'yar tsallen ba" cewar hajiya babba,murmushi ya saki kansa a qasa ya qarasa saman carfet din
"Qwarai kuwa,ni ke na biyo,saboda kece ta qarfen,idan bake ba sai rijiya" qaramin murmushi raihana tayi ta wuce cikin daki kai tsaye don tasan yanzu haka rumana na ciki.

Ai kuwa tana cikin tana tsala ado,ta baya raihana ta rufewa rumana ido tana fadin
"Sisi,ina mai farinciki da alamun kasancewata mutum ta farko wadda zata miki wannan albishir din" itama murmushin take
"Qwarai kuwa,ko da yaushe albishir dinki ke dadi ne gareni sis,bakya taba bari naji wani abu mara dadi daga bakinki,ina da yaqinin yau din ma haka take,saboda haka ina saurarenki"
Sai da ta danyi shiru na wasu daqiqu kana tace
"Sisi,an sa ranar aurenku ke da ya rayyan" suman zaune tayi na dan wucin gadi kana ta fasa wata qara,hadi da daka tsalle ta dale raihana,qarar da ta ja hankalin hajiya babba a gigice itada da rayyan ta soma tambayar lafiya?,me ya samu rumanan,qoqarin saisaita kanta sabida tunawa da tayi rayyan na falon tace
"Babu komai,ke kin fiya tsoro 'yar tsohuwa"
Shi kansa rayyan da ya san halin rumanan kai kawai ya kada don yasan wataqila wani abune da bai kai ya kawo ba ya sanyata hakan.

Hawaye ne suka biyo baya kuma,rumana ta rasa inda zata sa kanta saboda farincikin da ya cikata yaso ya mata yawa,itadai raihana binta take kawai da kallo fuskarta qunshe da murmushi,yayin da gefe dayan can qasar zuciyarta takejin wani feelings na maraici,sai take jinta tamkar ita daya jal,tayi qas da kanta ta shiga ninke musu kayansu cikin jakarsu.

Dariya taso kamata ganin yadda dukkansu rumana da rayyan din kowa yayi kicin kicin da dan uwansa,hasalima gidan baya rumanan ta shige abunta tabarwa raihana gaba.

Ta kalli rayyan ta sake juyawa ta dubi rumanan karo na kusan biyar
"Rumana rigima, ya rayyan dakiya da shariya wasu lokutan da guntun miakilancinsaHaka za'ayi zaman auren?" Raihana ta fada cikin zuciyarta,
Sai taji sam bata ji dadi ba yanayin zaman shirun
"Don Allah ya rayyan kayi haquri" ta fada tana marairaicewa har hakan yasa ya juyo ya dubeta sai ya dauke kai kamar bazaya tanka ba kuma sai yace
"Me kika yimin?"ta gane sarai me yake nufi,sai ta juya ta makawa rumana harara ganin taqi cewa komai,sai ta dauke kai can qasa tace da rayyan din" kayi haquri ya rayyan"itama shirun yayi har sai da ya gama shan iska kafin yace
"Baki dauki turba ba,sam bana daga cikin jerin maza marasa kishi,wanda annabi s a w yace ba zasu koda qamshin aljanna ba,ina da kishi rumana.....ina da kishi kuma kinsan da hakan" sai yayi shiru yana maida numfashi,raihana ta saci kallonsa,duk da gefan fuskarsa take iya gani hakan bai hanata gane bacin ran dake kwance bisa fuskarsa ba,a shagwabe rumanan ta shiga neman afuwa,tunda ta riga data sani laifi kam ta yishi,suna gab da shiga layinsun ya kada kai a taqaice yace
"Ta wuce,ki kiyaye gaba"
"Thank you,na gode dan uwana yaya na kuma mijina" tayi maganar cikin salon jan hankali tare da sakar masa fari ta mirrow,murmushi ya dan saki yana faka motar.

************

Qarfe takwas na dare ne da minti goma sha biyu,shiru kakejin dakin nasu sakamakon littafinta da kowacce ta saka a gaba,karatun jarabawa suke saboda daf suke da farawa.

Raihana ce sarkin son laushi saman gadon ta,yayin da rumana ke zaune qasan carfet,qarar wayar rumana ce ta katsesu,raihanan ta dago tana duban rumana,kiran ta duba sannan ta kalli raihana tana murmushi,don tunda suka fara karatun exam ya rayyan din ya qaranta zaman zance da sukeyi don ta samu cikakken lokacin yin karatun
"To ba mutanen naki bane,yaya rayyan ne" jin ta fadi haka yasa ta maida kanta kan littafinta,magana sukayi da bata wuce sakan goma ba ta katse wayar tana duban raihana
"Ya rayyan ke kiranmu"
"Tow,Allah yasa alkhairi" raihana ta fada tana dagowa daga durqushen da tayi
"Eh da alamun haka dinne" rumanan ta bata amsa tana ture tarin litattatafanta gefe gami da miqewa,itama raihanan miqewa tayi ta janyo lafayarta data cire dazun ta mayar jikinta ta nada,ta zira silifas dinta tana jiran rumana dake shirin canza dressing,tana tsaye ta sauya kaya sannan ta dan shafa powder suka fito,sai da suka leqa dakin ummu suka gaya mata sannan suka wuce
Chapter 16 · 0% Book details