← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 66

Sashe 7

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tuni auwal direbansu tun na quruciya ya gama gyara parking su kawai yake jira,rumana ta fara shigewa sannan raihana ta mara mata baya
"Kayi haquri don Allah yaya auwalu,mun barka kana ta jira" cewar raihana lokacin da take rufe motar,dariya yayi yana tada motar"ba komai anty raihana,nasan daga inda matsalar take ai"ya fada cikin son tsokanar rumana,ta dagoshi kuwa,kuma bata iya yin shiru ba
"Eh nikam saidai haquri,tunda nace banayi ba shikenan ba,uwar garkenka dai ta isheka" ta fada itama cikin salon wasa da yake mutum ne mai barkwanci sai biyu ta hadu,nan kuwa suka fara sana'ar tasu raihana na jinsu bata tanka ba har zuwa wani lokaci kafin suyi shiru sanadiyyar kiran wayar rumana da akayi.

Juyawa tayi tana sake kallon rumanan lokacin da take rufe murfin wayar suka hada idanu,har rumanan ta dauke kanta sai ta kuma juyowa ta dubi raihanan"madam wannan kallon nasan da magana a bakinki,fadi kar ta kasheki"kamar ba zata tanka din ba sai kuma ta fuskanci rumanan sosai cikin sanyin muryarta
"Dazu saif ya kiraki,yanzu kuma ibrahim,anjima kuma ina da yaqinin salis ko wani daban zai sake kiranki"dariya rumana ta fashe da ita" abun naki kuma ya koma sharri mss raihana?",kai raihanan ta girgiza"ba batun sharri ko kadan,gaskiya ce...rumana,duka wadan nan,gefw guda ga yaya rayyan....shin ina shi zaki kaishi?".

Lumshe ido rumanan tayi gami da runguma hannayenta aqirji,ta saki ajiyar zuciya fuskarta qunshe da murmushi"haba,har kin sani a wata duniya daga ambatar sunan rayuwata,me kike tsoro?,rayyan jini da tsoka da kuma jijiya ne,kuma mijin aure na da yardar Allah,duka wadan nan dama wasu da kike lissafawa mutunci ne kawai tsakaninmu,friendship ne ba wani abu ba,temporary ne su"lumshe ido raihana tayi ta kuma bude duka lokaci guda
"Rumana....ki fahimceni....babu wata alaqa tsakanin mace da namiji mai sunan abokantaka data wuce soyayya,ko ke ba haka bane cikin zuciyarki su na tabbata haka ne a zuciyarsu"dariya ta danyi
"Babe wannan ba fagenki bane bafa,ko na miki bayani ba fahimta zakiyi ba,tunda ke dubeki,budurwa mai kyau da aji amma ba wanda kika taba budewa zuciyarki ya shiga,a rufe take ruf,kinga kuwa kona gaya miki...ba zaki fahimceni ba".

Ci gaba tayi da kallonta ba tare da tace mata komai ba,daga bisani ta dauke idon daga kanta tana jijjiga kai,can qasa tace" Allah ya kyauta miki rumana"dariya ta saki tana kama hannunta"ni da ke my sister,na gaji so nake naga wane mai sa'ar ne zai samu nasarar daukar wannan 'yar uwar tawa"murmushi raihanan ta saki ba tare da ta shiryawa hakan ba,tasan da biyu rumanan ta fadi hakan don taji amsar da ta saba bata ko da yaushe,saidai taqi bata irin amsar a yau face shiru da ta bita da shi,itama rumanan taso tace wani abu don ta samu space din shigar mata da maganar al'ameen daketa kama qafa da ita.

Da wannan suka iso unguwar qoqin

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
__________________________

*An karbo daga nana Aisha 'yar abubakar saddiq R.A tace:Manzan Allah S A W yace"duk wanda yakeson haduwa da Allah to Allah zai so haduwa da shi,duk kuma wanda yake qin haduwa da Allah to Allah zai qi haduwa da shi,sai nana Aisha tace:amma dukkaninmu muna qin mutuwa,sai annabi yace"abun ba haka yake ba,saidai shi mumini idan akayi masa bushara da irin ni'imar ubangiji(da ya tanadar masa)sai yaso(yayi begen) haduwa da Allah,amma kafiri idan aka masa bushara da azabar ubangiji(da ya tanadar masa)sai ya guji haduwa da Allah,to shima sai Allah ya qi(guji/qyamaci)haduwa da shi*

_bukhari da muslim ne suka rawaito_

___________________________

*babi na takwas*

A bakin qofar gidan auwalu ya tsaida motar"qarfe nawa zaku koma sai na dawo na daukeku?"ya tambayi su raihana dake shirin fita a motar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta duba kana ta dago ta dubeshi"kada ka damu yaya auwal,idan muka bar nan ba gida muka nufa ba,zamuje wankin kai,amma ka tadda mu can inda muka saba zuwa,kamar qarfe biyar na yamma,ina tsammani kafin lokacin mun kammala"kai ya gyada yana tada motar
"To shikenan,kuce ina gaida hajiya babba din"
"Ba wanda zai gaya mata tunda baka shigo da kanka ba" inji rumana tana masa harar wasa
"Ko baki fada ba qanwata raihana nasan zata fada" murmushi raihana ta saki kawai ta shige gaba rumana nabin bayanta tana mata hira.

Tsarin ginin irin tsarin asalin ginin gidan bahaushe ne da muka sani,wato gida mai dauke da dakali hauni da dama daga qofar gidan sai zauruka guda uku da zaka wuce kafin ka isa ga ainihin tsakar gidan,fes ginin yake mulmul shafe da fenti ruwan madara,tamkar sabon gini,tsakar gidan ma mulmule yake da sumunti da ya shafu yayi kyau,hakanan fes yake gidan a share ko tsinke babu,duk da ranar da take a take,saboda sha biyun rana tayi a lokacin

Dakuna ne ke kalloka guda biyu da ka shigo gidan,dukansu masu dauke da qofofi irin na zamani masu fadi masu qofa biyu,ciki da falo ne manya da bandakuna a cikinsu,wadanda suka wadatu da kayan more rayuwa daidai da tsofin masu gidan,daga hannun dama kuwa wasu dakunan ne falle daidai guda hudu,uku spare ne daya kuma jikokin gidan da ake riqo ne su hudu,duk da baka raba gidan da jikoki masu kwana biyu kwana uku da masu zuwa hutun makaranta,biyu samari ne wadanda dakunan sa na zauren na biyu na gidan,biyun 'yammatan kuwa daya dakin suke amfani da shi,hannun dama kuwa kitchen din gidan ne qato da shi,kitchen ne irin na zamani,sai bandakuna biyu na wanka da na toilet sai store din gidan daga can gefe guda,wannan shine tsarin gidansu alhj dalhatu wanda Allah ya yiwa mai gidan rasuwa shekara goma baya,amma iyalan na zaune cikin hadin kai da zaman lafiya.

Sallama sukayi kana suka nufi dakunan kai tsaye,daga kitchen aka leqo aka amsa musu,baba ramma ce,itace mai musu girkin rana da na dare,sai kuma wanke wanke,ba wata tshohuwa bace,don ba zata haura shekara arba'in da biyar ba,ta jima agidan tun kafin rasuwar alhj attahiru mahaifin alhj dalhatu.

Dakin hajiya qarama abokiyar zaman haj babbar kakar rumana suka soma leqawa,tana kashingide tana qailula don haka basu tasheta ba tunda ba tafiya zasuyi da wuri ba,suka juya suka shige dakin hajiya babba.

Tana zaune qasan tiles,ta miqe qafafunta tana gurza gori fari sol jikin magogin qarfe,daga kai tayi tana amsa musu sallamar,da gudu rumana 'yar tsalle kamar yadda hajiya babba ke kiranta tayi halin nata,wato rugawa da gudu ta fada jikinta tana juye juye tare da fadin"yar tsohuwa mai ran qarfe,Allahk kasheki musha gumba"dogon salati hajiyan taja,bayan ta dire tace"dagani don qaniyarki,gyatumarki ce zata mutu bani ba,yanzu ace har yau 'yar tsalle baki bar tsalle tsallenki ba...to dagani tun kafin nasa tsohon qashina na maujeki"janye jikinta rumana ta fara yi tana muzurai"kajifa,ke sai ki damu kan kin dade bakiga mutum ba,amma da zarar yazo kuma saiki gallabeshi,gobe ma rana ce"
"Ta jibi ma ta fita don gidanku" ta bata amsa tana watsa mata daquwa,"ni dama bake na nema ba,kinga wadda na nema nan"ta fada tana nuna raihana da baki wadda ke kallonsu tana murmushi kadan kadan tare da tuno nata kakannin da sai tayi wata da watanni bata gansu ba,kai wani lokacin ma har shekarewa take yi.

Qwafa rumana taja"kinji ko raihanah,daga yau kada ki qara cewa nazo na rakaki tunda abun haka ne"ta fada tana janye jikinta ta koma saman kujera tana latsa wayarta da alama an fara sana'ar kenan
"Ke kika jiwo sautin kidan mahaukaciya.....raiihana" hajiya babba ta fada tana dubanta,fuskarta qunshe da murmushi ta sauko daidai qafar hajiyan cikin girmamawa ta rusuna tana gaidata,cike da kulawa ta amsa tare da tambayarta mutanen gidan,hajiya babba nason raihana,tun tana qarama tun kafin rasuwar mahaifinta alhj bukar takeson yarinyar.

Ta miqawa hajiyan saqon ummu tana karbar goron da magogin tana ci gaba da gogawa hajiyan,sosai tayi farinciki da saqon tana cewa"oh,fatima basa gajiya,to Allah ya bar zumunci,Allah yayi albarka"kadan kadan suke hirarsu da hajiyan,yayin da rumana ma sam batajin me suke fada,ta nitsa cikin chart da qawaye da abokai,hajiya ta dauka fushi tayi,yayin da raihana tasan ta cikin da bai sarai tasan me ya sanyata shiru da nutsuwa haka.

Baba ramma ce ta katse hirar tasu ta hanyar yin sallama tare da shigowa da kulolin abincin rana,hajiya tayi mata sannu kana ta tambayeta taji shiru hajiya qarama ko lafiya?,ta sanar mata bacci tayi amma yanzu ta farka sallar azahar,jin haka yasa rumana ta miqe ta nufi dakinta,don a can ne take samun damar cin karenta babu babbaka,don haj qarama kam ba ruwanta.

Tana fita qofar dakin haj babba ta saki ihu gami da yin kan kausar jikar gidan da ake riqo,mutuniyar rumana ce sosai sakamakon hali da yazo daya.

Da sauri hajiya babba ta fito tana zaton ko wani abu ne ya samu rumanan tana ambatar subhanalla,hajiya qarama ma dake salla ta shiga gaggawar sallamewa.

itama gun shukran gun rumanan tayo suka rungume juna tana tambayar yaushe suka zo suka bar hajiya babba da kama baki tana tafa hannu hadi da salallami kana ta juyo cikin dakin baki bude tana fadin"anya raihana 'yar uwar nan taki babu motsi bisa kanta kuwa?,bari dai dalhatu yazo naji"wannan karon sai da hajiyan ta bawa raihana dariya,ta dara kadan har sai da fararen haqoranta suka bayyana
"Lafiya qalau fa take hajiya,me zaya sameta"
"Um_um raihanatu ina tantama".

Koda hajiya qarama ta leqo taga meke faruwa ita din ma komawa dakinta tayi tana fadin" Allah ya sawwaqe muku,ko yaushe zaku girma oho"kasancewar duka tasan halinsu,da rumanan jikar hajiya babba,da tata jikar wato shukra,basu bi ta kanta ba sai rabe ta da sukayi suka wuce uwar dakanta suka baje hirar da suka saba koda yaushe.

Tun suna jiran rumana don suci abinci har hajiya babba tace raihana ta barta ta zuba musu suci,qila suna can sunci ita da abokiyar sakarcin nata,itadai raihana murmushi kawai tayi,don ita babu baqo cikin halayen rumanan da ta gani.
Chapter 7 · 0% Book details