Sashe 3
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kammala idda kuwa suka dawo don tafiya da ita din,a nan ne su alhj dalhatu suka gabatar musu da buqatarsu na a bar musu raihana da zainaba zasu kula da su,mutanen nada qima da daraja a idonsu babu abinda zasu tambaya su kasa basu kamar yadda suka san ko bukar na raye bazai iya hanasu komai ba,sun amince zasu bada daya amma dayar saidai suyi haquri don dangin mahaifin bukar ma sun matsa suna son riqon.
Ba yadda suka iya haka suka amshi raihanan don a son ransu a basu duka kowa ya dauki dai dai,alhj dalhatu shi yaso karbeta alhj yusuf yace haba ba za'ayi haka ba,kai da gidanka ke cike da yara,ni kuwa da muke mu uku daga ni sai fatima sai rayyan,ai a tausaya mana ko?,bai ja ba alhj dalhatun yace ba komai ya riqe din don da gaskiyarsa,amma fa shima ba za'a samu ladan babu shi ba,shi zai dauki nauyin karatun raihanan kamar yadda ya dauke na yaransa da rayyan ma baki daya,baice komai ba bayan godiya don yasan abotarsu tafi gaban haka don daga Allah take.
Komawar raihana gidan alhj yusuf ita ta kawo komawar rumana ma baki daya ta bar yin weekends kawai ta koma ta din din din,hakan ba qaramin dadi ya yiwa raihana na don jininsu ya hadu sosai da rumana,tanason surutunta iyayinta da rawar kanta,sai ta sata gaba ta yita kallo tana bata dariya,haka ma hajiya fatima ba qaramin dadi taji ba,ganin an share mata hawayen yara da bata samu ba,ta kamasu qam ta riqesu,duk qwaqwqwafinka baka isa kace ba ita ta haifesu ba,tana matuqar ji da su.
Hakanan rayyan sai yake jin shima yanzu gidansu akwai mutane ba kamar da ba da yake shi daya qwal,suka zama abokansa musamman rumana da shaquwarsu dama tafi qarfi kasancewar sun dade tare.
Wannan shine tarihin wadan nan iyalai guda uku,gidansu RUMANA RAIHANA da kuma RAYYAN
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*watpadd:huguma*
© *haske writers asso*💡
(Home of expert and perfect writers)
*An karbo daga usman dan affan R.A yace:manzan Allah S A W yace"duk wanda ya sallaci isha'i acikin jam'i tamkar yayi tsaiwar dare ne ta rabin dare,wanda kima ya sallaci sallar asuba cikin jam'i tamkar ya raya daren ne baki dayansa"*
_muslim ne ya rawaito_
________________________
*babi na hudu*
Tafe yake da 'yar sassarfa har ya qaraso bakin get din gidan nasu,bai wani saurari a bude masa qofa ba ya tura 'yar qaramar qofar dake maqale da madaidaicin get din nasu,ba bata lokaci ya bayyana cikin 'yar madaidaiciyar harabar gidan nasu dake shimfide da interlock,wadda motoci uku kawai take iya dauka,duk da ba girma ne da ita mai yawan gaske ba amma sai ta baka sha'awa,don qawace take da shuke shuke da kuma wadatar tsafta.
Tsaye suke cirko cirko bakin motar,daga raihana har rumana uniform ne a jikinsu,raihana na goye da jakar makarantarta daya hannun nata kuma riqe da lunch boxs dinta,yayin da daya hannun nata take riqe da lunch boxs din rumanan.
Ita kuma rigimammiyar na sabe da tata jakar makarantar,kai maqale kan kafadarta tana sharbe qwalla.
A hankali dariya ta subucewa rayyan,tabbas mai hali baya fasa halinshi,babu ko shakka yau ma darun tafiya makarantar akeyi da rumana.
Ya qarasa inda suke tsaitsaye su da auwal wanda abba yusif ya daukeshi don kaisu makaranta duk sanda baya gari ko ya fita kasuwa da wuri,don yace rayyan yayi qanqata da driving tunda duka duka shekarunsa basu wuce goma sha shida ba.
Tun kan ya qarasa ta hangoshi da gudu ta ratsa ta gefan motar ta nufeshi,ba bata lokaci ta maqalqaleshi tare da sakin kukanta baki daya
"To ya isa?,me kuma aka yi miki rigimammiya?"
"To yaya ba kaine ba,kayi tafiyarka bayan kasan da makaranta,kuma gashi ummu tace mu biyu yau zamu","amma dai rumana kinsan exams ke kaini makaranta kuma na gama nayi candy?,me kuma zanje nayi?"ta sake barkewa da kuka tana fadin" "Nima yaya na daina zuwa tunda ka gama,muyi zamanmu a gida"fuska ya dan hade don uasan darun mutuniyar tasa sarai,indai ba haka yayi mata ba ba za'a daidaita ba"a'ah,kina so muyi fada kenan?"kai ta girgiza tana kebe baki"good,me yasa kullum ke ke qin makaranta?,kin taba ganin rumana na kukan zuwa makaranta?"nan ma ta girgiza kai"kina son mu bata na daina yi miki magana?"da sauri ta sake sakin kuka tana bubbuga qafa tare da fadin"a'ah...a'ah"murmushi yayi a boye don yasan abinda tafi tsana ya fada kenan zai daina kulata.
"Ok to daga yau kada ki sake cewa ba zaki je makaranta kina jina ko?"tace "to"
"Promise?"
Kai ta gyada kana yace "da kyau"ya miqe yana amsar lunch boxs dinta daga hannun raihana ya damqa mata,ya yiwa auwal magana ya bude motar ya kaisu,sai ta ja ta sake cogewa tana narai narai da ido.
"Rumanaaaa...ya kuma akayi?"
"Nidai yaya ka rakamu..makarantar babu dadi yaya"
"Rumana baki ganin...."
DA sauri ta katseshi ta hanyar bubbuga qafa da shirin wani sabon kukan"don Allah yaya".
Baya son kukan da take tayi,kuma yasan halin rumanan da kafiya,hakanan kayan motsa jiki ne a jikinsa riga armless da boxer,idan yace zaya koma ciki kuma canzo kaya zasu makara ne kawai,don haka baice komai ba ya bude qofar motar yace raihana ta shiga,ta fara shiga rumanan ta shiga,yana shirin rufe murfin motar ta qiya dole shima bayan ya shiga,kafin sukai makaranta sai gashi baki ya bude tana ta zuba masa hira shi kuma yana biye mata tamkar ba ita ke faman sharar hawaye ba dazun.
Bata yarda ta barsu sun koma ba sai da ya dauki alqawarin tare da shi za'a zo daukarsu,cikin motar ya dinga murmushi shi kadai yana tuna rigima irin ta rumana,shi kansa yana jinjina shaquwa irin tasu,shi yasa ko gidansu baya yadda ta tafi da zummar kwana saidai su tafi tare ko su yini su dawo
*************
shigowarsa ta uku kenan yana tambayar ummu su rumanan basu dawo ba?,dubarsa tayi tana saka jug na lemon zobo da ta hadawa abba cikin freezer
"Basu dawo ba,ina zaton kwana fa zasuyi,ka dauki abincinka kawai kaci,don ko sun dawo dare ya riga yayi,qila ma sunyi bacci"
"Kwana ummu?"
"Eh,da matsala ne?",ba mai yawan son jan zance bane sai kawai ya girgiza kai yace ba komai ya juya ya sake ficewa
Tana zaune ita daya a falon, itama gidan ya mata shiru da yawa saijin sallamarsu tayi,rayyan ne a gaba riqe da hannun rumana wadda dankwalin after dress dinta ke hannu,kitson da suka tafi a yi musu acan gidansu gashinan rangadau a kanta,saidai idon nan yayi jazur da alamu kuka ta sha,raihana na binsu a baya saidai jikinta ba qwari ko bacci ta fara ya tattagosu?.
Riqe baki ummu tayi tana duban rayyan tare da fadin "daga ina?"
"Daukosu mukaje mukayi,lawan ya rakani"ido ta zare kana ta rufeshi da fada akan saboda me zaiyi haka?,tana cewa can ma gida ne kamar nan,kuma yau juma'a gone da jibi duka ba makaranta?
"Kiyi haquri ummu,gobe da jibin ne kawai naga muke zama tare,ragiwan kwanakin duka suna makaranta"abinda ya iya fadi kenan ya zube saman kujera
"Sai kace ba gid daya kuke kwana ba?ko weekend din cewa akayi ta qare ne,to naga yadda zakayi idan lokacin tafiyarka yayi"ta fada tana janyo wayarta ta nemo lambar hajiya rabi'ah maman rumanan ta kirata
lumshe ido yayi, yayi shiru don ko maganar tafiyar baiso,idan banda baba muhammadou da ya matsa a gida zai qarasa karatunsa shikam.
Gaisawa suka fara yi da haj rabi'ah kana tayi mata qorafin barin rayyan ya taho da su raihana
"Daina bata bakinki hajiya,ko rayyan baizo ba dama komai dare nayi niyyar dawo miki da yaranki,nikam bazan iya da su ba,kuka ta zauna dirshan tanayi tana kiran sunansa qatuwa da ita kamar wata yayayya,taqi cin abinci ganin haka yasa raihanan ma ta kasa ci,a haka yazo ya taddasu nace su tafi Allah ya raka taki gona"
Murmushi haijya fatima tayi"to ai shikenan,a gaida sauran yaran da abbansu"
"Zasuji in sha Allahu,Allah ya bamu alkhairi"
"Ameen sai da safe"
Ta ajjiye wayar tana dubansu,wuni daya tak duk sunyi wani fiqi fiqi dasu su ukun baki daya,damuwar ayyan da rumana ta hada har raihanan duka,duk sai suka bata tausayi don tasan nan da dan qanqanin lokaci zasuyi mai dalili.
Ba abinda ta kuma cewa da su illa kitchen da ta shiga kai tsaye raihana ta bita a baya ta tayata daukar plate ta hado musu abincin ta ajjiye musu,tana gefe tana kallonsu har suka kammala
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
*An karbo daga abu hurairah R.A,manzan Allah S A W yace"haqiqa ranar alqiyama ubangiji zaice:ina masoyan juna wadanda suka so juna saboda ni saboda girma na da daukakata,yau zan inuwantar da su qarqashin inuwata,ranar da babu wata inuwa sai tawa inuwar"*
_Allah kasanya mu daga cikinsu🙏🏽🙏🏽_
_________________________
*babi na biyar*
Misalin qarfe takwas na dare bayan sallar isha'i,zaune suke su hudun cikin parlour din gidan,rumana da raihana wadanda ke sanye da kayan bacci riga mai dogon hannu da dogon wando cotton,sai rayyan dake sanye da jallabiya baqa wadda ta haska fara tas din fatarsa,yayin da ummu ke gefe daya zaune cikin kwalliya take wadda basai an gaya maka kwalliyar dare ce irin wadda mace kan yiwa mijinta.
Suna kan carfet ne su biyun,littattafan makarantarsu ne a gabansu bude suna assigment rayyan na taimaka musu yayin da rabi hankalinsa ke kan wani novel mai suna lovestory,wanda ya cire cover dinsa don kada su ko ummu wani ya gani,hakanan yake son littafin sosai,yayin da ummu ke dauke da littafin rahiqil maktum tana duba wasu pages din.
Falon yayi shiru baka jin motsin komai sai na takardun rumana da raihana.
Alama ya sanya ya rufe littafin sannan yace"kun gama da arabic din?"
"eh" suka fada kusan a tare"
"ok"yace sannan ya amshi littafin raihana ya fara dubawa,jimla ce guda uku kowacce sai ka cika shafi bibbiyu da ita,tayi matuqar qoqari sosai,don ba qaramin kyau rubutun nata yayi ba,baifi layi goma ta qarasa ba,tura mata yayi yace"maza ki qarasa kafin abba ya shigo" ya waiwaya ya karbi na rumana.