← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 66

Sashe 25

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan qofae gidan a cike take saboda 'yan dinner dake ta dawowa,qaryar fitsari takeji tayi musu tayi shigewarta gidan ta barsu da siyayyarsu,rumanan bata shigo ba har sai da raihana ta gama shirin kwanciya.

****************

Tun daga ranar bata kuma bari sun sake hada hanya da shi ba,ranar lahadi da daddare bayan sun dawo daga kai amarya rumana ke gaya mata gobe zata bi ya rayyan su wuce kano,yace gidan babu kowa ba dadi,wani abu taji ya taba zuciyarta saboda tayi zaton tare zasu koma da rumanan,tunda gobe take son zuwa wa dangin abbanta
"Yayi kyau kam,nikam da sauran ziyara gabana" abinda tace kenan.

Qarfe takwas suka gama shirinsu,har bakin motar rayyan din ta raka rumanan,tun ranar sai yau ta ganshi,tamkar ma wani abu bai faru ba haka ta dake ta gaidashi tare da yi musu godiyan zuwa da addu'an sauka lafiya,tace su gaida ummu bayan uwar tsarabar da umminta ta bada a kaiwa gidajen iyalan guda biyu.

**************

Duk da tayi kewar sisinta haka ta ture gefe ta shiga kuma dangin abbanta,ina suka sa ina suka ajiye haka suka dinga yi da ita,kaf dinsu babu wanda bata je ta kwanan masa ba wanda hakan ba qaramin dadi yayi musu,sannan kuma shi ya sake ja mata lokacin komawarta kano,don sai da tayi wata guda cur sannan ta dawo cikin dangin umminta,tun rumana na qorafi har ta koma mita,da qyar ta lallabata kan cewa tana hanya kada ta damu.

Duk lokacin data tuna koda ta koma din abinda ke gaba yana jiranta duk sai taji komawar ta fita fit a ranta,wani lokaci zuciyarta kan bata qwarin gwiwa na babu abinda wani abu da zaici gaba da faruwa,tunda har yau tun ranar da suka bar maiduguri bata qara ganun kira ko saqon rayyan ba,koda yaushe addu'a take Allah ya sanya ya haqura ne,sau tari sai ta kammala addu'ar kuma sai ta dinga jin wani iri tare da ganin baiken kanta da take roqar Allah ya nisanta tsakaninta da rayyan din duk da yadda take ji a zuciyarta,duk sanda ta tuna hakan sai kuma wani sashe na zuciyar tata ya tuna mata wane rayyan?,hawaye kan zuba sosai cikin idanunta,takan kada kai tare da sake tabbatarwa da kanta cewa koda rayyan ne kadai namijin da ya rage a duniya ta haramtawa kanta aurensa saboda RUMANA,ta yarda ta kuma amince zatayi SADAUKARWA koda hakan na nufin qarewar jin dadin rayuwarta,albarkacin QAUNA SOYAYYA DA ABOTA dake tsakaninta da 'yar uwarta.

Wani lokaci idan tayi zurfi cikin irin wannan tunanin sai taji zuciyarta na zafi har ta kasa control din temper din da takeji,babu ko tantama tanason rayyan so irin wanda zaiyi wuya ka iya fassara yadda kakeji,duk wani qoqari na dakiya shariya da fada masa magana mara dadi idan tayi tanajin tamkar kanta take hukuntawa ne,don zafin da takeji a lokacin ita kadai tasan irinsa.

Rayyan ne irin namijin da ta dinga yiwa kanta fata da sha'awa tun kafin tasan darajar kanta,tun kafin tasan irinshi dinne zuciyarta ke da muradi,wata iriyar halittar zuciya Allah ya bata mai nutsuwa da gane daidai tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya take iya gane dabi'u kyawawa abun koyi tunda wuri,hatta da ummunta tun a lokacin tasha mamakin nutsuwa da kaifin fahimta da Allah ya bawa raihanan a qananan shekarunta.

Sai da ta cinye wata biyu a maiduguri hutunsu ya kusa qarewa sannan ta fara shirin komawa gida,tana jin tamkar tayita zamanta ne cikin danginta,kusa da mamanta tacu gaba da jin dumin mahaifiyarta,a yanzu ji take tamkar bata da kowa,rumanan da take gayawa damuwarta su samu mafita tare a yanzu wani qaton abu ya gitta tsakaninsu,a yanzun bata da wani abokin shawarw,bata da wani majibancin lamari,bata da wani wanda zasu iya raba damuwarsu tare,wanda hakan ya sake taka muhimmiyar rawa wajen qara dorawa zuciyarta nauyi mai yawa.

Ranar lahadi ta bar garin maidugurin wanda bata isa kano ba sai bayan sallar magariba.

**************

Yara ne suka fara shigar mata da kaya sannan tabi bayansu.

Da su idanunta suka fara cin karo,saidau fuskarsa ta fara gani saboda shike fuskantar get din gidan yayin da rumana ke zaune gabansa tana fuskantarsa.

Har zata wuce sai suka hada ido da shi,ta daura damarar nuna masa har yau yaya yake gareta ba wani abu ba daban,hakan ya sanya ta nufi inda suke,zuciyarta tayi wani irin bugawa har tsakiyar kanta,sai ta lumshe ido tare da qoqarin saisaita kanta sannan ta sake bude idon nata,har yau hannayensu na sarqafe da juna rumana na hawaye,sai ta taka a hankali ta dafa kafadar rumanan,juyowa tayi suka hada ido,tsalle ta daka ta rungume raihanan tana mata barka da dawowa,sai kuma ta sake barkewa da wani kukan,dagata tayi adaga cikinta qirninta na bugawa,addu'a take ya Allah kada kasa wani abu rayyan ya gayawa rumana dangane da DANGANTAKAR ZUKATANMU da har ya sanyata cikin wannan halin.

Jikinta na rawa haka ma bakinta tace"lafiya rumana?,me ya sameki?"
"Yanzu don Allah yaya rayyan ya kyauta min kenan?,ya yiwa zuciyata adalci?" Ta fada cikin muryar kuka,ji tayi qafafunta na barazanar kayar da ita,don haka ta sake dafa rumanan da dukka hannayenta biyu
"Me yace miki rumana?,me yayi miki?"
"Sisi wai course zai koma uk yayi har na wata shida,kusan gab da lokacin bikinmu kenan fa" wani abu taji ya tsirga mata har ta kasa ci gaba da tsaiwar ta nemi daya kujerar ta zauna,wadda sam saboda tsabar rudewa bata fuskanci ma gaf take da rayyan ba.

Nannauyar ajiyar zuciya ta saki sannan tace
"Kinsan Allah ba qaramin razanani kikayi ba?" Idanun rumanan a gwale tace
"Sabida me?" Da sauri tayi qoqarin canza akalar zancan
"Nayi zaton wani mummunan abu yayi miki ne sisi na,kinsan ban da kamarki"
"Haba sisi?,amma dai ai kinsan ba'a yiwa zuciyata adalci ba,har yau fa bai wuce shekara guda da baro uk din ba,sai da ya dawo muka sake sabawa sannan yace zai sake komawa?,gaskiya yaya rayyan nidai ban yarda ba" ta fada tana dubansa,dukkan alamu sun nuna da gaske take
"Already ba mun gama zancan dake ba rumana,ci gaba ne ya sameni fa,idan na kammala course din na gaya miki tamkar wata dama ce da na samu da zan gina nawa company din na kaina ko?".

Bubbuga qafa ta yi har sau kusan shida kana ta wuce cikin gida hawaye na bin kuncinta,wani abu take ji mara dadi sosai tattare da ita,ji take idan rayyan ya tafi tamkar ta rasashi kenan har abada haka zuciyarta ke gaya mata,ta rasa dalili ta kasa jurewa halin da take ciki.

Binta dukkansu sukayi da kallo har ta shige din sannan suka dauke kansu lokaci guda suka hada ido,kallo daya tak amma kowa sai da yaji cikin jikinsa,shi ya fara janye idanunsa ya tashi yabi rumanan,itama bayansu tabi amma suna zuwa falo suka raba jaha,shi ya shige dakinsu gun rumanan yayin da ita kuma tayi dakin ummu.

Ummun na ninke hijabin sallarta tayi sallama,fuskarta fal fara'a har cikin zuciyarta tace
"Oyoyo raihanata,oyoyo mutan birnin shehu" tana dariya ta qarasa inda ummun take ta rusuna tana gaidata,ta amsa tana mata barka da hanya,zamanta tayi a dakin ummun suka dinga hirarsu,kasancewar abba ya fita yayi baqir bai dawo haka suka kashe a qalla awa kusan daya da rabi tana bata labarin maiduguri da yadda bikin ya kasance,basu rabu ba har sai da ummun tace taje ta huta hakanan,dakin nasu ne bata son shiga din tana zaton ko rayyan na ciki har yanzu.

***************

Cikin kwanakin daru sosai rumanan keyi masa,ya rasa yadda zayayi da ita,ranar juma'a da yamma raihana na zaune na cin abinci bayan ta dawo daga makaranta ta duba time table nasu,lokaci lokaci tana kallin rumana dake kwance ruf da ciki tana danne dannan waya da alamu sana'ar tata take charting,saidai sam fuskarta babu wannan walwalar,haka ta koma kwana biyun har ummu ta lura da hakan.

Juyi tayi ta dawo da fuskarta bangaren da raihanan ke zaune saman carfet dinsu
"Yaya rayyan yace mu shirya,zamu rakashi wani guri" shuru ta danyi tamkar tace ba zata je ba,sai kuma taga idan tayi hakan zai iya haifar musu da matsala ita da rumanan,bai kamata ta dinga nuna abubuwa da zasu sanya kokwanto ko ganin rashin kyautatawarta kan rayyan a idanuwan rumana ba,tunda ko babu komai abinda zuciyarta keso ne
"Ok qarfe nawa kenan"
"Qarfe biyar na yamma yace" kanta ta daga ta dubi a gogo qarfe uku da ashirin lokacin,akwai awa kusan daya da rabi a gabansu.

"Ruma" raihana tayi kiranta,sai ta daga kanta ta dubeta tace na'am
"Me ya sanya ba zakiyi haquri ki sawa zuciyarki nutsuwa ba,kin saka damuwa mai yawa a kanki kan tafiyar yaya rayyan,naga a baya shekara tara yaje yayi balle yanzu da bazaya wuce wata shida ko bakwai ba" tashi tayi ta zauna sosai sannan ta girgiza kanta
"Raihana,akwai banbanci tsakanin shekarun baya da na yanzu,kin riga kin sani zuwa yanzu ya rayyan ya gama zama cikakken cikakken namiji da duk wata mace zata yiwa kanta sha'awar mallakarsa"
"To me yayi zafi haka rumana shi ba wuta ba,meye abun tashin hankali?"
"Bana son in rasa yaya rayyan ne,zuciyata na raya min kamar hakan na iya faruwa,kinsan yawan 'yammatan dake son rayyan acan garin?,ni nasan da zaman kowaccensu,bazan iya jurewa ba idan na rasashi ne" murmushi raihana tayi tana jin tausayin kanta na taso mata,babu shakka rumana kukan dadi take,ina ma ina ma,cikin salo na lallashi tace da ita
"Bai kamata a ganina ki tada hankalinki ba,rumana rayyan naki ne,ke kin riga da kin sani tun baya ma ballantana a ayanzun,babu wani abu da ya isa ya shiga tsakanin alaqarku su abba kin sani sarai ba zasu bari ba,ballanta na ni da sai inda qarfina ya qare" murmushi rumana ta saka,har kullum tana jin dadin yadda raihana ke nuna qauna gareta
"Ina fatan haka in sha Allah"
"Allah zai amsa da yardarsa"

Rage gudun da yakeyi yayi sannan ya gangara a hankali ya shiga daya daga cikin layukan anguwar,qofar wani gida da ake kan gininshi yaja ya tsaya sannan ya kashe motar.

Kallo daya zaka yiwa gidan kasan ba qaramin tsarashi aka yi ba duk ba a kammala gininsa ba
"Bismillah ku zagaya ku gani" yace da su yana tsaye hannyensa soke cikin aljihun trouser dinsa yana duban rumana,gidan nada girma shi ya sanya qarshe kowa ya rasa dan uwansa ya shiga wani saqon daban.
Chapter 25 · 0% Book details