← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 66

Sashe 36

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali wasu siraran hawaye suka fara zirya bisa fuskarsa,jikin mukhtar din yayi tsananin sanyi,ya riga da ya dade da sanin waye rayyan,jarumin gaske da bako wanne abu ke saurin karyashi haka ba,saidai baiyi mamaki ba,so yana da qarfin da zai iya karya dukkan wani mutum komai girma da qarfinsa kuwa,kusan zai iya cewa bai taba ganin karaya ko hawaye tattare da rayyan ba,sai yau karon farko a tarayyarsu.

Hawayen na sauka ne tare da radadi da zugi mafi tsoka da zuciyarsa ke masa,sai ya dinga jin sanyi na sauka cikin zuciyarsa,fiye da rabin nauyin da qirjinsa yayi ya zabge,mintina kusan talatin kafin ya sanya mukhtar ya taimaka masa ya miqe tsaye,da kansa ya shiga toilet ya daura alwala sannan ya dawo inda ya zauna ya tashi yana duban mukhtar
" ya riga ya wuce mukhtar,qaddara ta riga fata,raihana ta zama matar wani,bai da muhalli ci gaba da tattauna maganarta,Allah ya riga ya qaddara hakan ce zata kasance,abinda kawai nakeso daga gareka kada ka gayawa kowa cewa damuwa ta kwantar da ni,ko wanene,maganar ta tsaya iya mu biyu"
Kai mukhtar ya jinjina
"Ko baka fadi haka ba akwai sirri tsakanin likita da mara lafiyansa,Allah ya sanya haka shi yafi alheri gareku baki daya"
"Inaso ka rubutan sallama,inaso na koma gida hakanan,yau kwanan biyar a asibitinku,inata sa mutane zirga zirga,kuma nima na gaji hakanan" murmushi mukhtar din ya danyi
"Ba damuwa ai sai amarya ta qarasa jinyarka ko?" Shima mayar masa da martanin murmushin yayi ba tare da yace komai ba

****************

Gaba daya ta tattara qarfin qwanjinta dana zuciyarta ta hana kanta yin wani motsi da zai bayyana halin da zuciyarta ke ciki,ta gayyato walwala farinciki da sakewa ta azawa kanta,ta dauki duk wani abu da ya faru a baya a matsayin mafarki ko almara,wani lokacin tsantsar qarfin hali takan nuna a fili tamkar tafi rumana kuzari da walwala,saboda har yau rashin komawar rayyan daidai ke mintsinar zuciyarta.

Kusan tunda ya dawo gidan shima yayi namijin qoqarin maida komai ba kamai ba,musamman duk lokacin da tunaninta ko wani abu yaso tasiri a kansa,yakan tunawa kansa da jaddadawa kansa matar wani ce a yanzu,dukkansu gudun juna suke,don kowa baya bari ya hadu da dan uwansa,shi iyakarsa da cikin gidan ya shiga ya gaida ummunsa,gadan gadan ya tayar da aikin gyaran gidan da na nashi gidan baki daya,cikin sati biyu komai ya kammala,gidan ummun ya koma sabo,sati na gaba kuma suka sanya za'ayi sauran shagulgula irin na mata.

Ba qaramin rawar gani daddy dalhatu yayi ba,don kowa ya gwagwaje kowaccensu da kayan jere na gani na fada,kowacce set bibbiyu ta samu,yayin da umminta daga maiduguri ta musu komai na kayan kitchen da kayan humara da turaren wuta,maman rumana kuma duka sauran tarkacen qyale qyale da sauran abinda ba'a rasaba ita ta hadasu.

Cikin gidansu ammar aka yi mata jeranta,da yake gidan akwai girma,part ne guda yalwatacce wanda ya cinye duka kayanta,ita din ma hakan ya mata dadi,tunda ko babu komai zata zauna cikin mutane,mutanen kuma dake sonta suke kuma ji da ita.

Sosai rumana taso a hada dinner ta gani ta fada,saidai daga raihanan har rayyan din zuqewa sukayi,ita raihana ta bada hanzarin cewa ammar bazaya samu damar zuwa ba,yayin da rayyan yaqi cewa komai yace dai kawai baida ra'ayi,tunda ya sani dole su hade da raihana da ammar,bugu da qari har yau qarfin hali kawai yakeyi amma bai soma jinsa daidai ba.

Wunin biki kadai akayi sai walimarsu ta iya su,kausar ta shaqi takaici don ba haka suka so ba,sunso su gwangwaje matuqa da gaske.

Ranar lahadin qarfe takwas kowacce tana gidan mijinta,rabuwar rumana da raihana abune da babu wanda bai koka musu ba,kasancewar babu wanda baisan irin shaquwar da take tsakaninsu ba,sun rabu suna masu qauna da kewar junansu,kowanne zuciyarsa cike fal da alhinin rabuwa da dan uwansa.

_kashin farko kenan ku biyoni din jin gaba ta biyu ta labarin_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:30 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Manzan Allah S A W yace"imanin dayanku baya cika,har sai ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa(na duk wani abu na alkhairi)"*
_______________________

*_saqon gaisuwa da fatan alkhairi ga duk fans na dangantakar zuci_*

*_sadaukarwar shafi dungurun gum ga 'yan_*

*Z B I*

*Babi na ashirin da bakwai*

Inda suka tafi suka barta a nan taci gaba da zama,kukan kam babu kalar wanda bata yi ba,fargaba take na wacce kalar rayuwa zata shiga,tabvas tasha ji daga bakunan ma'aurata cewa rayuww ce mai wuya,hakanan rayuwa ce mai cike da qalubale iri daban daban,koma meye dai itakam ta shigo cikinta da niyyar yin bauta wadda take fatar ta samar mata aljanna madaukakiya.

Su biyu rak suka shigo shi da maisara,hannayensu dauke da ledoji,barkwanci na 'yan mintina maisaran ya jata da shi wanda ta gaza amsawa,kana daga bisani ya dubi ammar yace
"To ni zan fa wuce,amma zo na ganka mana"
"Ok muje,raihana ina zuwa" inji ammar wanda yabi bayan maisara.

Tun tana kasa kunnen dawowarsa har ta janye,sai bayan shudewar awa guda sannan ya shigo,har ya sauya kayan jikinsa,ya dubeta
"Au,baki tashi hakanan ba,ya kamata ki tashi ki rage gajiya ko?" Ya fada yana zama kan kujerar dake daura da ita,cike da kasala gajiya damuwa da baqunta ta miqe ta shige bedroom dinta,tayi wanka ta daura alwala,babu sallar da ake binta bashi saboda haka ta maida kayan jikinta ta dawo falon.

Yana inda ta barshi,saidai wannan karon gabansa akwai plate wanda ya juye kazar da suka shigo da ita,daya hannun nashi kuma riqe yake da wayarsa yana danne danne,dubanta yayi sannan ya sauko qasa yana tura mata plate din kazar da lemo mai sanyi.

Kasa sakewa tayi taci,ya lura da hakan sai yace da ita
"Ki sakit jikinki,kada ki wani damu ko takura,ni babu wani abu da zan miki kinji" yayi maganar yana dubanta,tilas ta sake ta danci don kada ya sanya tunanin hakan a ransa.

Ta rigashi kammalawa daya gama shi ya hada kwanukan ya maida kitchen din sannan ya umarceta taje ta kwanta.

Tana tsakiyar lallausan gadon nata amma tsoro ya hana barci yayi nasarar saceta,sai data kashe kusa awa guda sannan ammar ya shigo
"Baki bacci ba raihana,kiyi bacci nasan kin gaji,nima a gajiye nake" ya fada yana rabewa gefanta yaja filo ya dora kansa,tun tana dari dari har ta saki jiki jin shiru babu wani motsi da ya biyo baya,da haka nannauyan bacci mai cike da gajiya yayi awon gaba da ita

****************

Tare sukayi komai da ammar din wanda kiran maisara ne ya tashesu,shi ya tayata ta sake gyara gidan tayi goge goge ta hada musu break fast,suna shirin karyawa saiga aiken break din daga hajjaju,fatima ce dauke da kwando niqi niqi
"Ayyah anty dama bakiyi ba,tun dazu dama naje cewa hajiya ta kawo na kai muku tace a'ah bari rana ta dan sake dagawa,mai yiwuwa baku tashi ba kada na tasheku" murmushi raihana tayi tace
"Babu komai,nikam na hajiyan ma zanci,don dama ruwan tea da qwai kawai na hada mana,kice ina gaisheta kafin na shigo"
"Zata ji anty,su anty sabira ma suna gaisheki,sai anjima idan zasu koma gida zasu shigo"
"Ina amsawa" ta bata amsa fuskarta qunshe da murmushi.

Suna gama karyawa ammar yace zai fita maisara na nemansa,tayi masa a dawo lafiya sannan ta dawo cikin falo ta jona kayan kallo ta fara rage lokaci ganin batayi baqo ba,sisinta na ranta saidai batason musu katsalandan ta hanyar fara kiranta,'yar halak sai kuwa ga kiran nata,cikin murna ta daga,sunsha hira sosai kamar ba zasu rabu ba,sai da rumanan tace bari ta koma gun ya rayyan ta baroshi daga shi sai kayan kallo,sukayi sallama kowa ya ajjiye wayar.

Da azahar ma hajiyan ce ta aiko musu da abincin rana ita da ammar din,ganin ammar bai dawo ba sai ta dibi nata taci ta ajjuye ragowar.

Qarfe shida ta shiga toilet ta gyara kanta tare da sake tsala kwalliya cikin atamfa,bata jima da zama ba aka fara knocking ta bada izini aka shigo,yayar ammar ce sauda da qanwaraa sabira da yaransu guda takwas wanda manyan ciki ke riqe da kula,da fara'arta ta tarbesu suma suka amsa mata da fara'a sannan suka bata kular abincin daransu inji hajjaju,godiya tayi sosai tare da yabawa qoqarin matar,iyalan mutane ne masu mutunci da karamci,haka suka ta hira har aka kirayi sallar magariba suka ce zasu koma cikin gida don anjima duka zasu koma gidajensu,cikin kayan gararta danginsu alkaki dublan,nakiya,meatpie ta zuba musu mai yawa bayan botiki guda babba da ba zuba tace a a kaiwa hajjaju.

Sai kusan qarfe tara da wani abu ammar ya shigo,ya mata sannu da gida sannan ya wuce dakinsa dake can gefe guda cikin wani corridor yayi wanka ya sauya kaya ya fito sannan ta gabatar masa da abinci,ya dinga janta da hira har ya kammala cin abincin,sukayi yi kallo na dan wani lokaci sannan suka tafi bedroom,kamar jiya yau ya rigata ma yin bacci,don haka hankalinta kwance tayi baccinta.

Sai washegari mutan maiduguri sukazo saidai babu mamanta ciki,bata kuma so hakan ba,don taso ganinta kafin ta koma sukayi mata sallama kan gobe zasu wuce,tare suka wuni,sun sake sosai don yauma ammar kamar jiya bai dawo da wuri ba,da zasu tafi kamar ta bisu don har kuka tayi

****************

Cikin sati biyu ta fara sabawa da sabuwar rayuwar da take ciki,tanajin dadin zamanta cikin gidan,duk da kasancewar ammar ba mazauni ba yakan fita tun safe sai dare hakan bai fiya damunta sosai ba sabida tana da 'yan tayin hira,ko tayi tafiyarta bangaren hajjajun bata dawowa sai magariba tayi 'yan abinda zatayi kafin ammar ya shigo.

Sam bata damu da rashin neman ta da ammar baiyi ba,tana ganin hakan bai komai bane,mai yiwuwa yana mata uzurin rashin sabo ne ko tausayinta yake ji

**************

Zaune yake cikin falon nashi wanda yake kusan daidai da aljannar duniya,gama cin abincinsu kenan ta kwashe kwanukan ta kai kitchen,kusan minti goma bata dawo ba,hakan ne ya bashi damar janyo computer dinsa ya fara wasu aiki a ciki,don har yau bayajin kuzarin da zai iya fita office.
Chapter 36 · 0% Book details