← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji tayi zuciyarta kamar zata fado,a iya saninta da rayyan baya qarya,hasalima tunda suke ba zata iya tuna wani abu guda da ya taba fada ba na qarya,wato da gaske kenan idan batayi wasa ba rayyan zai jaza mata tashin hankali?,zai janyo mata abinda zai sanya farinciki yin qaura daga rayuwarta?,aurensa fa na nufin faruwar komai game da ita,ta raba rumananta da shi,sannan ta zama butulu mayaudariya maci amana a idon duniya,ba zata iya ba,ta gwammace ta dawwama cikin qunci,ta gwammaci ta rasa nata farincikin.

Ba shakka ta lura nuna qiyayya barazana da nuna duk wani qarfin zuciya da qwanji bazaya tafiyar da rayyan daga kan ra'ayinsa,abu guda take ganin yanzu zai iya mata aiki,lallashi wayo da dabara har ta samu su rabu lafiya din.

Ta sake dubansa tana goge hawayen fuskarta tare da qoqarin daidaita yanayinta,ya zuba abincinsa yana ci a nutse tamkar baya da wata damuwa,a hankali ta taka inda yake ta samu gefansa ta zauna

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Shiru tayi yayin da shima yaqi tanka mata har ya kammala cin abincin yayi gefe da kwanukan
"Yaya rayyan" ta fada cikin murya mai cike da rauni,idanunsa ya daga kawai ya kalleta,sai ta zame qasa kan gwiwoyinta,wasu sabbbin hawayen na neman zubo mata
"Na roqeka yaya rayyan ka janye dukkan qudurinka,kana sakani cikin tsaka mai wuya duk lokacin da ka bijiromin da wannan maganar,na roqeka don Allah yaya rayyan ka barmu mu koma kamar yadda muke a baya,mu koma 'yan uwa masu qaunar juna da fahimtar juna" ci gaba yayi da kallonta har ta kammala,a hankali ya bude bude baki ya fara magana,yanajin wani abu ja zagaya jikinsa
"Zanso hakan,nina zanso hakan idan da zuciyata zata iya haqura da ke raihana,raihana.....na tabbata babu qiyayyata cikin zuciyarki,kina pretending nr kawai saboda rumana,me yasa kikeson haramta halas?,me yasa kike son dora son zuciyarki gaba da abinda Allah ya halatta,kada ki yarda raihana ki shiga hurumin ubangiji,dukkaninmu bamu muka dorawa kanmu a binda muke ji cikin zukatanmu,ban damu ba raihana kuma bazan damu ba da dukkan ma abinda zai faru,abinda na sani kawai shine ina son RAIHA".

Ji tayi tamkar yana sosa mata zuciyarta ne,zuciyarta ta sake yin rauni,sai kawai ta sanya tafukam hannayenta kan fuskarta tana jin yadda hawaye masu dumi ke fitar mata,tabbas da tana da iko da babu abinda zai hanata tsaga zuciyarta ta jefar ko kuma ta tsaga ta uban tafiyar rayyan ta sauya masa da wata wadda rumana kawai zata so ba tare da ta hadata da raihana,sai yanzu take gasgata kalaman wasu kalamai da wani yayi wanda ta taba cin karo da su garin bincike bincikenta,inda yake cewa
_babu shakka so dafi ne,so masifa ne kuma bala'i ne ga wanda Allah ya jarabceshi,so yakan iya zama linzami ga duk wanda ya tsinci kansa a tarkonsa,so wani maruru ne da kan azabtar da zukatan masoya,wani tsiro ne da yakan tsiro a zuciyar duk wanda yaga dama,so na gaskiya baya buya a zuci ko a baki,ba zaka taba sanin mene ne farinciki ko baqinciki ba sai lokacin da kake soyayya,soyayya tafi komai dadi amma tafi komai azabtar da zukata_
Lokacin da taci karo da kalaman murmushi kawai tayi tare da kada kai,ashe tabbas haka suke,ta tserewa fadawa irin wanna yanayin kamar yadfa mutum ke qoqarin tserewa mutuwarsa ashe gudun da babu tsira tayi tayi tsawon shekaru,sai kawai ta miqe tana niyyar ficewa daga parlour tana jin jiri na dibanta,numfashinta na daukewa,wani abu ya tokare mata qirji

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*manzan Allah S A W yace "ku yawaita tuna mai yanke jin dadi(wato mutuwa kenan)*
_______________________

*Babi na ashirin*

Karon da suka ci da rumana ya sanya jarumatarta dawowa cikin 'yan daqiqu,murnar ganin rayyan din ya sanya bata tantance halin da raihanan ke ciki ba,sai tayi ciki fuskarta dauke da murmushi tana fadin
"Suprise ya rayyan?" Murmushin ya maidata mata gimi da dage girarsa yana fadin
"Yes,ko ba'a yi murna da zuwana ba?"
"Haba ya rayyan,ko yaushe ai mu masu maraba da kaine ko sisi?" Ta fada tana duban raihana dake coge bakin qofar falon,murmushin yaqe ta qaqalo tana fadin
"Haka ne,bari na baku guri ku zanta sosai,zan shiga ciki"
"Amma dai kinsan tafiyar tamu ce mu duka biyu ko?,ba a gida muke ba balle kice" wani yaqen ta sake yi
"Na sani,na sadaukar muku da lokacin ne don kufi sakewa sosai" fari rumana tayi sannan tace
"Shi yasa nake alfahari dake sisi na,godiya nake" kai ya jinjina kawai tayi hanzarin ficewa.

Ita kadai tana tafiya kamar iska zata kayar da ita,hakanan sai ta dinga ji me yasa ta fito ta baro su,idanunta naci gaba da hangosu su biyun,saurin kwabar kanta tayi,a haka ta isa sashen hajja yakura,kai tsaye dakin gadonta ta shige,can quryar gadon tsohuwar ta samu ta lafe ta saki wani marayan kuka,a ranar tayi kukan data jima batayi irinsa ba,tayi kukan tausayin kanta da kanta ita kadai,sai data gaji don kanta ta lallashi kanta da kanta gudun samun matsala saboda yadda taji zuciyarta na mata zugi,sunayen Allah ta dinga ambata dari ba daya,idan ta gama ta dawo daga farko,tun tana iya jiyo surutan mutane jifa jifa har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.

Har aka kammala daura auren bata farka ba,tun rumana na cigiyarta harta haqura ta koma gun baqonsu saboda babu wanda yaga shigarta dakin hajja ya kura,hakanan ta kikkira wayarta a kashe.

Qarfe biyar na yamma ya dauki rumanan tare da aisha ta rakasu ya samu masauku cikin wani hotel dake gabansu,tafiyar da yake da shirin yin ya fasata yace sai washegari.

Qarfe biyar da kwata ta farka,salati ta saka lokacin da ta duba agogo,Allah ya taimaketa tayi sallar azahar la'a sar ce kawai a kanta.

Parlour din ta fito,hajja yakura ce zaune gefanta hajja salma yayar ummin raihanan,sai hajja bilkisu da hajja batula qannen ummin raihana,sai wasu mata dake shigiwa da kayayyaki suna ajjiyewa,sannan basma da alawiyya da shigowarsu falon kenan sanye da ankon dinner din da za'ayi bayan sallar magariba,da alama sun fara shiryawa,hajja yakura ta dubeta riqe da baki
"O ni 'yasu,duk neman da yarinyar nan take miki ashe kina qunshe a daka?".

Murmushi tayi tace"bacci ne ya daukeni hajja,yanzun tana ina?"
"Sun fita ita da aysha da yayanku" inji basma
"Ok"cewar raihana kana ta wuce bandaki,wanka tayi ta hado da alwala ta bada faralin salla sannan ta shirya cikin nata ankon,lokaci lokaci tana yi tana duba wayarta ko zata ga kiran rumana amma shiru kake ji,zuwa lokacin 'yammatan sun fara cika gidan wasu daga cikinsu ma sunyi gaba can hall din da aka kama don gabatar da bikin.

Parlour ta dawo ta kwanta hannunta riqe da wayarta tana game,a hankali har aka yoye sai amarya da daidaikun qawayenta makusantan ta,sai ta dinga ji ta damu da rashin dawowar nasu,ba rumana ba rayyan din.

A hankali ta daga wayar tata ta sake dubawa a karo na barkatai,sai ta dan ja tsaki ta maida wayar ruwan cikinta,ta rasa dalilin da ya sanya ta damu da yawa haka,gashi ta gaza kiran rumanan taji basu dawo din ba,batason taga kamar ta matsa musu ko tayi musu katsalandan,rayyan kuwa dama bata da ra'ayin kiransa ko kadan.

Baba gana ne yayi sallama hadi daga labulen falon ya shigo yana kiran hajja yakura,sanye yake cikin shadda light blue sai qyalli take wadda aka yiwa dinkin tazarce,turus yayi yana duban raihana
" a'ah,ke bahaushiya ya naganki nan zaune bayan kusan duka an tafi?"murmushin yaqe tayi tana gyara kwanciyarta
"Banajin zanje ne ma baba gana"
"A'ah,me yasa kuma?"ya fada yana qarasowa cikin falon tare da samun kujerar dake gefanta ya zauna,tashi tayi itama ya zauna sannan tace
" rumana har yanzu basu dawo ba,kaga bazan tafi babu ita ba ko?",murmushi yayi
"To banda abinki ba naga tare suka fita da yayanku rayyan ba?"kai ta gyada masa
" kizo kawai mu wuce nima can zani,nasan idan ya dawo zasu wuce can tunda da mota hannunsu,amma ya zaki zauna ke daya bayan gidan babu kowa sai tsofaffi?"kamar ta qiya sai kuma taga zaman bai da amfani,bata son taci gaba da zama har tunane tunanen dake bijiro mata suci gaba da uzura mata.

Uwar dakin hajja yakura ta shiga ta sake gyara fuskarta ta sanya glass dinta sannan ta yafa mayafinta mai kyau wanda ya dace da ankon jikinta da aka yiwa dinkin doguwar riga,ta saqala 'yar madaidaiciyar jakarta mai hannun sarqa (chain).

Miqewa baba gana yayi yana dubanta tare da murmushi,jakar kafadarta din ya amsa yana cewa
"Bani na tayaki ta riqon wannan" murmushi ta saki tace"dama ka barshi ai babu nauyi"
"Ke dai ladan kike kin baqinciki" ya fada yana karbe jakar.

A hankali suka jero yana janta da hira har suka fito harabar gidan inda motarshi ke fake gefe daya,mamanta ce tsaye ita da qannanta zainab da ammi sanye suke suma da nasu ankon duk da basu wuce shekara sha biyu ba da goma ba amma sunyi kyau sosai,black beauty ne suma kyawawa kamar yanayin yayar tasu raihana
"Sannu ummi" raihana ta fada tana dan ranqwafawa cikin girmamawa,waiwayowa tayi fuskarta qunshe da fara'a
"A'ah,baba gana baku tafi ba dama?"
"Eh ummi,na shiga amsar saqo hannun hajja naga wannan bakanuwar zaune shine na sanyata ta fito wai da bazata je ba"
"A'ah,dalili da me?"
"Eh mama,rumana ce bata dawo ba,ni kuma banson tafiya ni kadai"
"A'ah,da rayyan suka fita inajin ai ko?,kuma har da aysha,babu mamaki ma sun wuce can din tunda zasuyi tunanin zaki taho"
"Haka nace mata ummi" inji baba gana yana fiddo maqullin motarsa daga aljihunsa.

"Yaya,bamu samu mota ba muzo mu tafi tare don Allah?" Cewar zainabu
"Me zai hana qanwata ku taho mana" cikin murna suka bi bayansa yayin da raihana ta yiwa ummin sallama ta bi bayansu.

Remote ya danna su zainab suka bude gidan baya suka shiga,motarsu rayyan ne ta kunno cikin gidan,ta kalli sashen da motar ke shigowa sai kuma ta dauke kai,baba gana ya miqa mata jakarta tayi hanzarin bude gidan gaba ta shige,shima ya zagaya ya tada motar tasu suka fara ficewa daga gidan lokacin da motar su rayyan din ke tsayawa.
Chapter 23 · 0% Book details