← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 66

Sashe 58

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake dakewa tayi sannan tace
" babu ruwan mijina,bai shiga tsakaninmu ba ke kikeson raba tsakanin daya da biyu,inaso naga sisi na tana rayuwa irinta cikakkiyar matar aure cikin gidan mijinta,ina so naga rayyan ya rasa gane wadda tafi iya kula da sonshi tsakaninmu,inason naga sisi na ta zama cikakkiyar matar aure kamar kowacce mace"
"Cikin gidan rumana 'yar uwata tare da mijinta?" Raihanan ta tambayeta tana bude idanuwanta kan rumanan,kai ta gyada cike da tabbatarwa
"Eh,idan kuma kika qi,ban taba kai qararki ba tunda muke....amma wannan karon,zan kai qararki gaban hajja yakolo,gaban hajiya babba,kai har gaban abba da daddy ma,na rantse kuma tsaf zan aikata hakan karki dauka da wasa nake,saboda haka ki shirya daga yau zaki amsa sunanki na amarya kuma matar gida" bata kai ga furta komai ba muryar islaha ta cika dodon kunnensu tana kiran rumanan,ta shigo falon sanye da kayan bacci tana haki na gudun da tayi,tayi turus tana duban raihana sai kuma ta kwasa da gudu tayi gurinta,duk da yanayin da take ciki hakan bai hanata cafe yarinyar ba fuskarta qunshe da murmushi,tana bala'in son yarinyar,tana jinta kamar rumana
"Momma,a gidanmu yau kika kwana?"
Kai ta gyada mata tana murmushi tare da shafa gashin kanta
"Itama ta dawo gidanku,ta zama 'yar gidanku" inji rumana,
"Yeyyyyy" islahan ta fada cikin murna
"Da gaske momma anan zaki dinga kwana kema?,nan ne dakinki?" Kai ta sake kada mata,rumana ta sake matsowa inda suke
"Amma kice mata ta ta so daddynki kinji?" Sai ta dubi raihanan ta kwabe fuska
"Momma bakya son daddyna?,daddy na nada kirki fa momma,zai dinga siya mana chaculets da ice cream,yana kaimu yawo,don Allah kice kina son daddy na" hararar rumana raihana tayi irin harar zaki hadani da diyata kenan?
"Ina son daddyn islaha"dariya yarinyar ta saki tare da yiwa raihana kiss a kumata tana cewa
" zan gayawa daddy nasan zai sai miki chaculet".

Tare sukayi break fast dukansu sannan rumanan ta fice ta barsu nan din dubawa ko rayyan din ya tashi,sosai raihana ta dinga biyewa islahan,sai taji damuwarta cikin kaso dari babu hamsin,sai far gaba da take ahiga duk sandabta tuna maganarau da rumana,tasan tsaf zata iya gayawa mutanen da ta lissafo din,tasan kuwa indai hakan ta faru kashinta ya bushe,don babu mai ganin laifin rayyan cikinsu sai nata,me ya kamata tayi?.

Ita ta yiwa islahan wanka ta shiryata tsaf tare da yi mata kwalliya,yarinyar tayi kyau,kamarta da mamanta ta sake fitowa,ta samu baqi ba laifi wadanda suka kaita har wajen la'asar sannan suka tsagaita.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*

______________________

*Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace "lallai da sannu zaku dinga nuna kwadayi akan shugabanci,kuma da sannu zai kasance NADAMA a ranar qiyama"*

_ruwayar imam bukhari_

_________________________

*Babi na arba'in da biyu*

Gidan ta sake gyarawa inda ya dan baci sannan ta sake turareshi da turaren wuta kana ta zauna kallo ita da islaha.

Qarfe shida rumana ta turo qofar falon hadi da sallama,tayi kyau cikin dinkin atamfa riga da skert wadda tayi mata cas a jikinta,make up ne sosai a fuskarta.

Ta zauna kan daya daga cikin kujerun tana duban raihana
"A zaune kike kenan?" Ta mata tambayar tana dubanta ganin ba wani shiri da take
"Eh wallahi" raihanan ta bata amsa ba tare da nuna ta gane me take nufi ba
"Islaha nazo dauka to,oya muje a sake wanka,daddy ya kusa dawowa"ta fada tana miqawa islahan hannu
" oh,tafiya zakuyi ku barni?"
Ta waiwayo ta dubeta
"Amma dai baki manta maganar da mukayi ba dazun?"tabe baki raihanan tayi sannan tace
" oho to sai me?"murmushi tayi tace
"zaki gani ne" ta fita tana sake cewa
"Sai kinzo cin dinner,bance kiyi girki ba"
.

Ci gaba tayi da kallonta saidai hankalinta na kan rumana,bata so ko daya tayi wani abu da zai sosa ran 'yar uwar tata,amma tana ganin dole ta sabawa tsarin rumanan saboda tana jin nauyin bin tsarin nata yadda take so.

Bata tashi daga kallon ba sai da taga an kusa kiran sallar magariba,toilet ta shiga ta hada ruwan wanka tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wani material lemon grean me sulbi dinkinta na yau da kullum doguwar riga,mai kawai ta shafa da powder sai man lebe,ta daure jelar qananun kitsonta da aka mata daga maiduguri da wani dan madaidaicin ribbom orange,ta sake shafe jikinta da humra sannan ta wuce kan abun sallarta ta tada sallah.

Kai tsaye bangaren rumanan ya wuce wanda sai da yayi knocking wajen sau biyar abinda bai taba ba sannan ta bude qofar falon nata,tana dauke da islaha a kafadarta wadda tayi mata kwalliya itama kamar yadda suka saba cikin riga da wando farare duka,idanunshi cikin nata ya miqa hannu ya amshi islaha dake qoqarin sauka daga jikin mamanta zuwa babanta tana cewa
"Oyoyo daddy" yana fadin
"Daddy's girl,kinyi kyau"yayi kissing kumatunta sannan ya maida dubansa ga rumana wadda ta tsare qofar shiga falon
" yau kuma sai na roqi a bani hanya ne madam"gira ta daga mashi tana murmushi hannayenta harde a qirjinta
"Muje sashenka,yau can zaka sauka" yayu dan jim sannan shima ya daga girarsa duka biyun yace
"Toh,yau kuma?"
Itama sake daga masa girar tayi tace
"Yes" tana qoqarin amsar islaha daga hannunshi tare da cewa
"Taho ki bar daddy ya huta kinga ya gaji" qememe taqi yarda tazo gurin ta hakan ya sanya yace ta rabu da ita suka jera zuwa sashen nasa.

A falo ya ajjiye islaha bayan rumanan ta kunna mata cartoon a tashar m.b.c 3 sannan suka wuce bedroom ta hada masa ruwan wanka ya kintsa sannan ya fita sallar magariba.

Bai dawo ba sai da aka idar da isha'i,ya tadda su a falon tana taya islahan kallon cartoon din,zama yayi kusa da islahan ta dawo jikinsa ta kwanta,ya kalli sashen da rumana take yana shafa cikinsa da hannu daya
"Madam yunwa nakeji,naga alamar yau komai ma roqa nake" miqewa tayi tana dubansa
"Ok,bani minti biyu" ya bita da kallo sanda take ficewa ba tare da yace komai ba.

Kan kujera ta sameta a kwance tana amsa waya,shigowarta ya sanyata katse wayar ta miqe daga kwanciyar fuskarta qunshe da murmushi
"Amarya ki taso muje muci abinci"tsaki raihana tayi tana hararta
"Amaryar wa?,kada ki sake wani cemin amarya wallahi matuqar baso kike muyi fada ba"
"Fada kuma na nawa?" Rumanan ta fada tana mele baki,sam bata kawo rayyan na gurinka ba don bata ji ma shigowarsa ba hakan ya sanya ba musu ta miqe ba tare data damu da yafa koda mayafi ba tabi bayan rumanan.

Bangaren da taga suna shiga ne ya sanyata tsayawa turus ta dubi rumanan
"Ina kuma zamu haka?" Ta tambayeta,shiru tayi mata tare da ci gaba da tafiyar,juyawa tayi da niyyar kowama taji an riqo hannunta,waiwayowa tayi sai suka hada ido da rumanan,wani irin fushi da bacin rai da bata taba gani ba ta hango idanunta,sai jikinta yayi sanyi ta kauda kai daga kallonta
"Zan iya jure komai aa banda cin fuska ko wulaqanci wa mijina,zan kuma iya miki uziri kan komai banda taka doka ko iyakokin Allah" ta saki hannunta tayi gaba,binta tayi da kallo sannan daga bisani tabi bayanta jikinta a sanyaye.

A hankali ta daga idonta bayan shigarsu falon,yana zaune gefan islaha ya bude mata cheesy yana miqa mata tana karba tana ci,ganin suna qoqarin hada ido ya sanyata kau da kai,baiyi tsammanin ganinta ba sam hakan ya sanya masa wani yanayi lokaci guda ya mamayeshi saboda ganin da yayi mata na rashin zato,sai ya maida kallonsa kan rumana yana jifanta da wani kallo,qin dubansa tayi face dauke kai da tayi cikin basarwa sannan tace
"Sai ku tashi muci abincin tunda kowa ya hallara" ta fadi tana miqewar,ta saitin raihana tabi tana sane ta take mata qafa tare da cewa can qasa cikin rada
"Allah ya sawwaqe miki tunda ko gaisuwa baki iya ba" da sauri ta daga kai ta cilla mata harara
"Eh din ban iya ba" ta gaya mata tare da murguda baki,caraf kan idon rayyan,yabi dan qaramin bakin nata da kallo,ya manta kwana nawa rabon da ya ganta din,sai yaga kamar an sake sauyata,sanyinta ya sake daduwa,yanayinta da komai nata ya sauya,kanta na kallon can wani sashen tana tafiya zuwa dining din tace dashi cikin hade rai
"Barka da yamma"banza yayi da ita tamkar baiji ta ba,sai da yazo saitin bayanta sannan ya furta shima can qasa
"nafi qarfin irin wannan gaisuwar,ki riqe kayanki"sai ta tabe baki cikin ranta tace
"ka hutar da ni" ta bar maganar tasa tabi ruwa ba tare da rumanan ta ankara da abinda ya farun ba.

Tamkar kurame haka suka zama kan table din,rumana da islaha kawai ke karadinsu,kallonsu kawai takeyi don ta gama shirya tsiyar da zata musu,haka suka kammala cin abincin,ita ta soma miqewa jin garin ya fara qugin hadari wanda dama kwanansa biyu yana haduwa a sama ba'a samu ruwan ba ta dauki islaha tana fadin
"Oya,muje na sauya miki kaya duk kin bata kayanki,shi yasa banson saka miki fararen kaya wlh"
"Ni momy ban gama kallon cartoon din ba,kuma momma ma tace zata tayani kallo"
"Muje in canza miki sai mu dawo,nima hira nakeso muyi da daddy" dukkansu babu wanda ya fahimci manufarta sai data fice gurin ya zama sai su biyu,sai itama ta ture kujerarta baya ta miqe ta sauka daga wajen cin abincin tayi qofar ficewa daga falon.

Wasa gaske sau uku tana murda handle din qofar taqi buduwa.
Chapter 58 · 0% Book details