Sashe 30
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ayyyiriririririri ango kasha qamshi" maganar data daki dodon kunnenta kenan,ko ba'a fadi mata ba tasan ko waye,saboda yadda qamshinsa ya game ilahirin tsakar gidan,duk yadda taso ta dake ta hana kanta kallon sashen da yake zuciyarta taqi aminta da hakan,a hankali ta daga kanta tare da fara juya idonta zuwa sashen da jikinta ke bata yana tsaye,karaf idanunsu suka hade guri daya,wani irin maganadisu ya fisgi kowannensu,hakanan kwalliyar kowannensu ta burge dan uwanshi,wani lumshe mata ido yayi tare da kashe mata ido daya wanda ya sanya tsigar jikinta tashi,dauke kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani abu da batasan ko mene ne ba ya taso ya tokare mata wuya,kwalliyar da yayi ta shiga yawo cikin idanunta,sanye yake da shadda fara qar tamkar takarda wadda keta faman maiqo da daukar ido,riga da wando ne da babbar riga wadda tasha surfani irin na maza,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan ba qananun kudi ya lasa ba,komai da yayi amfani da shi fari ne,kama daga hula agogo da takalmi,yayi gyaran fuska tare da rage kwantacciyar sumarsa sai hakan ya sake fidda masa wani sigar kyawun na daban.
Laushin da jikinta ya sakeyi shi ya haddasa mata jin kamar ba zata iya ci gaba da tsaiwar ba don haka ta juya don shigewa kitchen ta karbi abinda ya fiddo da ita,qarar shigowar tex taji cikin wayarta,ta bude wayar a hankali,numbobin wayar rayyan suka bayyana,sai ta samu kanta da saurin budewa
_ina fatan kwalliyar da nayi ta burgeki kamar yadda taki tayi masifar tafiya da imanina,much love my dear raiha_
Sai ta tsinci kanta da waiwayawa a hankali sashen da yake din,har yanzu idanunsa na kanta din,murmushi ya sakar mata wanda saura kadan yayi gaba da numfashinta,hakan ne ya haddasa mata saurin shigewa kitchen din ta fada kan kujerar plastic dake ajjiye cikin kitchen din don kada ta zube a qasa
"Ke,meye haka?" Taji muryar umminta na tambayarta,gaggawar daidaita natsuwarta tayi sannan ta saki murmushi
"Babu komai ummi,abincinmu nazo dauka"
"Gasunan,zo ki dauka" inji ummu tana nuna mata matsakaitan coolers din,hannu tasa ta dauki ta abincin daya hannun kuma ta dauki ta miyar kana ta juya zata fice,kacibus sukayi a bakin qofar yana niyyar shigowa ita kuma tana niyyar fita,sai ta ratse don ta wuce ta gefansa hannu taji ya sanya yana niyyar amsar kular abincin hannunta,dagowa tayi a rude tana dubansa,shima nashi idon na kanta,ta tabbatar daga kitchen din har tsakar gidan ko ina jama'a ne kuma wani kallonsa na iya kaiwa kansu yayi musu fassara,ta lura rayyan din ta bare yake nema,neman magana da rigima ta hanga fal qwayar idanunshi,hakan ya sanya ya ta sakar masa kular tayi gaba cikin azama,ba bata lokaci ya biyo bayanta,qasa qasa yake mata magana
"Tafi a hankali mana 'yammata na,duka saurin na meye?" Bata tanka masa ba illa kadawar da zuciyarta keyi kamar ta faso qirjinta ta fito.
A bakin qofar dakin taja tunga ta tsaya tana dubanshi a marairaice idanunta fal qwalla,roqonta daya ya barta a nan kada
Yace zai shiga dakin,don ta riga da ta san kadan ne daga aikinsa
Miqa mata cooler din yayi ta sanya hannu ta amsa,sai yabi lallen hannunta da kallo
"Ina fatan yadda lallen nan ya miki kyau haka ya yiwa amaryata?" Bin lallen tayi da kallo kamar yanzu ta fara ganinshi sannan ta sake dubanshi,har yanzu ita yake kallo fuskarsa qunshe da murmushi,sai tayi shiru tare da juyawa don shigewa dakin ba tare da tace da shi komai ba
"Ki gaida min amaryata,i love you" taji daddadan muryanshi saitin kunnenta wanda ya sanyata zabura ta shige dakin
_11:30 pm_
Qarfe sha daya da rabi na ranar juma'ar alqawarin Allah ya cika,wato daruruwan jama'a suka shaida daurin auren RAYYAN YUSUF ADAM da kuma UMMA RUMANA DALHATU ATTAHIR,ba qaramin farinciki iyayen ango da amaryar ke ciki ba,ganin sun sake qulla wani zumunci mai qarfi tsakaninsu.
Daga gefe guda kuwa farinciki ne fal zuciyar rumana musamman lokacin da hayaniya ta sake cika tsakar gidan alamun an gama daurin aure 'yan uwa na shigowa ana gaisawa,yayin da wata iriyar fargaba da tsoro wadanda batasan daga inda suke ba suka mamaye raihana,a hankali ta dinga jin wani sanyi na ratsata,da fari tayi zaton a.c din suka qurewa dakin ne,don haka ta ja mayafinta ta lullube jikinta tana zaune daga gefan gado,sai daga bisani ta fahimci sanyin ya wuce na a.c don haka taja jikinta saman gadonta ta cure guri guda,sannu a hankali kidan da kausar ta sanya cikin dakin suna cashewa ya soma hawa mata ka,cikin 'yan mintina qalilan wani zazzafan zazzabi ya rufeta kirif.
Sam ki kadan rumanan bata lura ba,har sai da suka fita tsakar gida ana hotuna rayyan din ya gaza haqurin rashin ganinta ya tambayeta,sai a sannan hankalinta ta dawo jikinta,lokacin da ta isa dakin babu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi,a rude ta dinga mata sannu sannan ta fita ta gayawa ummu,ce mata tayi ta daure suje taga likita,sam ita ta riga data sani ba wani magani na zamani ko na gargajiya da zai iya mata aiki yanzu,sauqin dai na gurin Allah,don tun daga cikin zuciyarta take iya jin ciwon,hakan ya sanya ta kafe kan a bata paracitamol tasha kawai ya isheta,idan bai sauka ba taje asibitin,babu musu rumana ta lalubo ta bata,ummu ce ta dubi rumana
"Hayaniyan nan ma na daya daga cikin abinda ke qara mata ciwon kan,nasan halin raihana sarai batason kwarafniya,maza kamata ki kaita bangaren yayanku ta kwanta a can ta huta,tunda duka gidan a cike yake da mutane saahensa ne kawai ba kowa don sun wuce reception sai kuma yamma ina zaton zai shigo" rumanan ta amsa mata da to,sam batason zuwa sashen nasa,bata son gani ko mu'amala da duk wani da ya jibanceshi,amma babu yadda ta iya haka rumanan ta kamata suka bi ta qofar baya har sashen nasa,taso ta barta a falo amma tace sam sai data danganata da gadonsa sannan taja tattausan bargonshi ta rufeta ta fice bayan ta ja mata qofofin baki daya.
Wata masifaffiyar qaunarshi ce ta dinga taso mata tamkar ta halakata lokacin data tsinci kanta kwance saman gadonshi cikin tattausan bargonshi,qamshinn turaren baccinshi ya buwayi hancinta,ji takeyi tamkar shine kusa da ita din,da gaske kam ta rasa rayyan,ta rasashi kenan,ya mata nisa na har abada,ya kuma haramta ya zama miji a gareta,wasu hawaye masu zafi da radadi suka biyo kuncinta,tabbas babu shakka so shine mafi girman abinda yafi hukunta zukata da sanyasu cikin qunci radadi har ma da bacin rai,kanta ta dinga mirginawa hagu da dama saboda wani qunci da taji qirjinta yayi,ta rasa inda zata dora kanta taji sanyi,a hankali ta dinga karanto addu'ar yaye qunci da damuwa babu qaqqautawa,wata tayita afili wata tayita a zuci,batasan yaya akayi ba bacci ya saceta wanda ta tabbatar albarkacin addu'ar data yi ne,idan banda haka bata jin duk iya satar tasa ya isa ya saceta din.
A gaggauce ya shiga dakin don ya sake watsa ruwa ya kuma sauya kaya don su wuce wajen reception din wanda aka sauya shawara kan a bari a sauko sallar juma'a sannan a gabatar ganin yadda lokacin sallar juma'ar ya qarato sosai,ganin mutum ba zata kwance kan gadonsa ya sanyashi tsayawa turus,a hankali ya taka bakin gadon ya sanya hannu ya yaye bargon,idonshi fes kan fuskarta da tayi fayau tare da wata rama ta lokaci guda,jin yadda bargon yayi dumi ya sanyashi taba goshinta,take yaji zafin dake jikinta ya ratsa fatarsa
"Subhanallah" ya fada a gajiye yana zama gefan gadon,wani irin tausayi mai cakude da so ya rufeshi
"Har yaushe raihana har yaushe zaki ci gaba da cutar da zukatan bayin Allah?" Yayi tambayar a fili duk da ya sani babu mai amsa masa tunda bacci take,shiru yayi yana mai ci gaba da kallonta tare da qulla hanyoyin tsira garesu baki daya kala daban daban wanda saida kira ya shigo wayarsa yasa ya ankara da jama'ar dake jiransa,jikinsa babu qwari ya debi kayan da zaiti amfani da su ya koma toilet din falon ya shirya.
Dakin ya sake komawa bayan ya gama shiryawa,yana tsayae yana balle botiran rigarsa yana ci gaba da duban raihanan rumana ta turo qofa ta shigo
"Yauwa yayanmu,dama inata tunanin kota farka?" Ta fadi tana qarasowa kusa da shi tasa hannu tana ci gaba da rufe masa maballayan da bai qarasa ba,murmushi ya saka sannan ya dan sake janyota jikinsa ta hanyar sanya hannayensa ya zagaye qugunta da su yana dubanta
"Bata farka ba,har yanzun bacci take" ya bata amsa yana dubanta lokacin da suke musayar numfashi,mutuwar da jikinta yayi ya sanya ta kasa ce masa komai har ta kammla rufe masa rigar,sai ya janyota ta fada qirjinsa ya matseta sosai cikin jikinsa yana fatan samun sauqin zugin da zuciyarsa ke masa.
A hankali raihana ta maida idanunta ta sake runtsesu,yadda basu ganta ba bata fata su ganta din,dago kai tayi tana duban qwayar idanunsa
"Yaya rayyan,meke faruwa ne?" Tayi masa tambayar tana sake dubansa,shima kallonta yayi sannan ya sake maidata cikin jikinsa tare da dora habarsa saman kafadarta kana yace
"Me kika gani?"
"Jikinka yana nuna weakness dinka,sannan a yanzun ma zuciyarka bugawa takeyi sosai" ajiyar zuciya ya saki sannan ya maida mata amsa
"Gajiya ce my angel,na gaji na gaji sosai" ya fada cikin wani irin yanayi,sai ta tashi daga jikin nashi tana fadin
"Ayyah sorry yaya na,daga yau dai ai shikenan ko?"
Sake riqe qugunta yayi yana duban qwayar idonta wanda hakan ya sake sanya mata kasala
"Bashi kenan ba angel,tunda na tabbata ba za'a bani ke ba sai na dawo daga tafiyar wata shida" kunya ta dan kamata sai tace
"Ai kamar yau ne" kiran wayarsa da aka sakeyi ya katse hirar tasu dake sukar zuciya da duka sassan jikin raihana,ya ansa wayar a gaggauce sannan ya dubi rumana
"Ki kula da ita angel,idan ta farka kika ji zazzabin bai sauka ba is better taga likita,kimin waya zanzo na kaiku"
"Ok sai ka dawo" ya manna mata kiss a goshi sannan ya fice.
Wani tsalle ta daka ta sauka gefan gadon dakin,wani farinciki takeji kamar an mata kyautar duniya da abinda ke cikinta,zamanta tayi tana ci gaba da gadin raihana,duk zaman da take tana jinta amma taci gaba da yin likimo,har akayi sallar azahar ganin bata motsa ba tayi zaton barcin take har yanzu sai ta sake ficewa.
*mrs muhammad ce*👑