Sashe 32
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Maimakon taji zuciyarta tayi sanyi kamar yadda ta saba yawancin lokuta idan tayi kuka sai taji akasin haka,tsoro fargaba da wani irin faduwar gaba ne suka mamayeta,ga wata iriyar kasala da mutuwar duka gabban jikinta,tana zaune har uku saura sannan ta yunqura ta shiga toilet cike da mamakin rashin isowar amir har zuwa wannan lokacin,don tayi tunanin kafin ta kammala shiryawa ya iso me yiwuwa har yama zauna jiranta.
Har ta fito ta kammala shirinta babu labarin amir,ta daga waya ta soma lalubar number dinsa don jin lafiya ganin hudu saura ta kawo kai.
Bugu uku aka daga saidai maimakon muryar amir din muryar mace taji,a hankali cikin shaqaqqiyar murya tace
"Ba amir bane,husna ce"
"Ayyah husna an yini lpy ya mutan gidan"
"Lafiya" husnan wadda take qanwa ce ga amir din ta amsa a agajarce
"Hala amir din bai kusa ko?,ko a gida ya bar wayar?" Ta sake tambayarta,maimakon ta amsa mata sai ta saki kuka kawai wanda ya gigita raihanan ta shiga tambayarta,da qyar ta iya bude baki tace da ita
"Allah ya yiwa amir rasuwa anty raihana a hanyarsa ta zuwa kano,yanzu haka ga gawarsa nan ana shiryata"abinda kunnenta ya iya ji kenan wayar ta sulale daga hannunta.
Wani irin tashin hankali taji an rufto mata wanda bata taba jin irinsa ba,hannu ta dora akai ta fasa qara wadda ta jawo hankalin rumana da rayyan dake zaune a falo take kuma zuciyarta ta tunasar da ita haramcin hakan da kuma azabar da hakan yake jawowa mamaci,jiri na shirin kayar da ita ta zame daga gefan gado zuwa dandagaryar carfer tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a jejjere kuma a fili tana mai fatan abinda taji ya zama mafarki ne ba gaskiya ba.
Rayyan ne a gaba rumana na biye da shi,zuwa lokacin da suka iso tuni raihanan ta qarasa birkicewa,da sauri rumana ta zube gabanta tana jijjiga kafadarta tare da tambayarta lafiya,sai a sannan ta saki innalillahin da take ambata,saidai ta kasa yi musu bayanin komai baya ga sunan amir da take ta kira.
A hankali rayyan din ya samu gefan katifarsu ya zauna,sannan ya fidda wayarsa ya kira layin amir,ba jimawa aka daga,bayanin da ta yiwa raihana shi ta yiwa rayyan,a hankali shima ya dinga ambatan hasbunallahu wa ni'imal wakil kana ya kashe wayar ya yiwa rumana bayani,itama kukan ta sanya,sai suka sakashi a tsakiya ya rasa da wacce zaiji,gashi ummu bata nan,da qyar ya shawo kan rumana ya nuna mata ita ce mai lallashin raihana suka hadu suka dinga bata baki,saidai duk a banza,abinda take ji na zafi da radadi cikin zuciyarta babu abinda ya canza,hakanan ta kasa tsaida hawayenta a haka ummu ta tarad dasu.
Haqiqa ba qaramin jin mutuwar sukayi ba baki dayansu,kada ma raihana taji labari,hatta da rayyan ua girgiza matuqa,mutuwa ba wasa bace,washegari tun bakwai na safe suka shirya baki dayansu sai garin bauchi
.
Zuwan na raihana sai ya sake ruruta wutar rashin da sukayi,batasan amir ya bata matsayi mai yawa a rayuwarsa ba sai wannan karon da take cikin danginsa,kusan kowa yasan raihana a baki,sanin ido da ido ne kawai basuyi mata ba,dakinsa kuwa hotunanta ne birjik wadanda batasan lokacin da ya samesu ba,tayi kuka tayi kuka sosai,ta tausayawa kanta na rashin masoyi da tayi,ta tabbatar ba qaramin so amir yayi mata ba,babu yadda ta iya haka Allah ya rubuta tun usul ba zasu zama ma'aurata ba.
Wannan mutuwar ya sanya rayyan ya daga tafiyarsa ya maidata wani satin,domin suna can bauchim shi da rumanansa da raihanan ana karbar gaisuwa da su,raihana taga karamci da qauna gun 'yan uwan amir din,lokaci guda ta dinga ji kamar an dauke wani sashe na gangar jikinta,ki babu komai akwai SHAQUWA da SABO hausawa kuwa sunce SABO TURKEN WAWA NE.
Ranar da akayi sadakar uku suka dawo kano,sun baro bauchi cike da jimami alhini da kuma jajantawa juna rashin da sukayi.
Sosai mutuwar ta dinga tabata har ta dinga rama,bata iya hana kanta kuka duk lokacin data tuna da amir din,duk lokacin data tuna cewa a hanyar zuwa wajenta ya rasa rayuwarsa,itakam mai zata je da wannan masoyin gaskiyar,tabbas babu abinda yayi shaura a tsakaninsu yanzun face addu'a.
Sosai rumana ta dage gun kula da sisinta haka ummu da abba wanda suke zaton tsantsar soyayya ce tsakaninta da amir din,hatta da rayyan ba'a barshi a baya ba,tausayinta yake ji sosai,ya ja baya sosai da ita duk don su samu ta dawo nutsuwarta
.
A hankali ta dorawa zuciyarta tawakkali,ta dauki duk wani rudu da take ciki tayi wurgi dashi bayanta,ta azama ranta zata yi karbi rayuwa duk yadda tazo mata,qaddarartace haka haka Allah ya tsara mata.
*************
Kusan awa biyu suka dauka suna kwabe kwaben meatpie,doughnout da chin chin,sai kuma dambun naman kaza da raihan ta sarrafashi da kanta,duka wannan idea dinta ce data cewa rumana ta yiwa rayyan din,saboda tana iya tuma labarin da yake basu wancan tafiyar na dadewa da yayi kafin test na spices da girkin garin yabi harshensa,sai da suka gama tsaf rumanan tace ta mata mai wuyar,taje ta kwanta ta huta ta barta ta soya,murmushi tayi tana yaba irin qaunar dake tsakaninsu,har yau wani rarrashinta suke suna duba damuwar dake cikin zuciyarta.
Dawowarta dakin ya kasance ita daya,sai tunani kala daban daban ya dinga bijiro mata,sanye take da wani material sil dinkin doguwar riga umbrella mai dogon hannu ruwan sky blue mai zanen hadari,kanta babu dankwali amma yana matse da ribbom kalar kayan jikinta mai laushi,a hankali ta miqe ta isa ga locker dinta ta janyo wadda ke shirye da littattafai kala daban daban,kama daga na karatu da kuma na rubutu,dagawa ta dinga yi tana dubawa idonta ya fada kan wani littafi mai kyau ruwan hoda turarre da mai haske wanda rayyan ya taba aiko musu da shi,a qalla ya qunshi shafi sittin tasan kuwa ya isheta rubuta duk abinda takeso,sai ta ciro shi hade da wani biro ta dawo baki gadonta ta dora qafafunta duka saman gadon,shiru tayi tana tunanin me zata rubuta,murmushi ta saki daga bisani sannan ta fara rubuta duk abinda yazo ranta.
Sannu sannu sai gashi tana shirin tasan littafi dangane da rayuwarta,tun daga randa tasan me takeyi a duniya,quruciyarta da 'yar uwarta rumana da rayyan,wani abun idan ta rubuta tayi murmushi wani ya girgiza kai,wani kuma ta share qwalla,musamman mutuwar abbanta da ta tuna da zamowarta ita kadai a inda bata saba rayuwa ba wato garin kamo gidan abbanta yusuf,sai take jin wani dadi,yanayin yana mata dadi,ji take tamkar tana hira da wani ne rubutun da take,tamkar tana gayawa wani damuwarta ne da ita din wacece,tsaye yake kanta hannayensa harde a qirji yana biye da duk wani harafi da ta rubuta ba tare da ta sani din ba,shi kansa saita rubuta wani abun sai ta tuna masa da moment din ya kanyi murmushi lokavi bayan lokaci.
tayi rubutu mai tsawo kafin ta fado fagen da batasan ta fado din ba
_na gujeshi irin gudun da dan adam kan iya yiwa ajalinsa,na gujeshi gudun da ban taba yiwa wani abu ba a rayuwata ba,na rufe zuciyata saboda shi,na hana kaina dukkan wani 'yanci dalilinsa,ashe yana biye da ni?,ashe yana zai riskeni sannna zai kuma wahalar da ruhi gangar jiki zuciya da ma rayuwata baki daya,na fara son rayyan tun bansan sone ke yawo a zuciyata,na fara sonsa tun lokacin da bana zaton 'yar uwata ta fara sonshi,na fara sonshi lokacin da nake tsammani tsoronsa nake,infact ina zaton da sonshi aka haifeni,nakanji bugun zuciya duk lokacin da aka ambaci sunanshi tun ina gaban iyayena kafin zama ya hadamu da shi,ashe duka sone wanda yarinya da tsoro duka suka hadu suka boyeshi,ban farga da mugun tarkon da na fada ba sai bayan wani lokaci da hankali ya game jikina,wanda zuwa lokacin yayimin nisa baya qasar,zuwa kuma lokaci na makara saboda tuni soyayya tayi nisa tsakaninsa da 'yar uwata,a lokacin da ya bijiromin da buqatarsa bakin alqalami ya riga ya bushe,bazan iya maida masa raddin kan abinda ya nema ba,bazan iya sallama masa kaina ba,ba wai don bana sonshi ba,hasalima nafi duk wata halitta dake doron duniya qaunarsa,saidai da ya riga ya mallaki zuciyar rumana 'yar uwata,wadda nake jinta tamkar cikin mahaifa guda muka kwanta,nake jinta har cikin jina na,na riga da na SADAUKARWA 'yar uwata RAYYAN,SADAUKARWA ta har ABADA,domin ta cancanci fiye da haka ma a gurina,na sallamawa rumana farincikina soyayyata da kwanciyar hankalina,na bar mata shi har ABADA._
A hankali jikinta ya raunana kamar yadda zuciyarta ta raunana,sai ta gaza ci gaba da yin rubutun sakamakin dishi dishin data fara gani saboda rashin glass kan fuskarta,ga wani irin zafi da zuciyarta ke mata,sai ta kifa kanta kawai saman littafin ta soma sheshaheqa don ta gaza boye sautin.
Zare biron da akayi daga tsakanin yatsunta ya sanya ta dago kai zuciyarta na wani matsanancin bugu ga zatonta rumana ce,saidai sabanin rumanan sai taga rayyan ne,da sauri ta janye littafin tana qoqarin rufewa,bai hanata ba don ya na biye da ita,ya riga da ya gama karanta komai,zagayowa yayi gabanta ya zauna a gefan gadon har gwiwarsu na gogar ta juna,tayi yunqurin janyewa daga gurin sabida tsoron kada wani ya shigo ya gansu saidai ya hana mata hakan.