Sashe 54
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qarar wayar amman ya katse maganar tasu,ta ciro wayar sannan ta kara a kunne
"Gata" kawai tace tana kara mata wayar,hajja yakolo ce,ta soma gaidata,bata amsa mata ba ta hauta
"Na kira ki ne na jiki naso idanunki ma na gani,hajiya babba ta gaya min komai,ai bansan ke butulu bace raihana sai yau,ashe har kina da bakin da zakiqi jinin yusufu?,har yauahe kika zama mutum da zaki nunawa jinin yusufu qiyayya,nayi zaton ko wani kika ga yaqi jininsa sai inda qarfinki ya qare ki"
"Ya ialahi ina zan sanya kaina ne?,ba qinsu nake ba hajja ina duba 'yar uwata ne,ina duba alaqarmu fa......"
"Kinga yimin shiru ya isheni,yarinyar ba ita ta bankada abinda kuke ciki ba?,to ki shiga hankalinki,wallahi kika sake kika musguna mata ko kika bata ranta kan wannan batu sai munyi tur da ke don na fahimci take takenki....yauwa,sannan uwarki ma na fuskanci inda tasa gaba ta biyosu sun taho,to wallahi kada naji kada na gani,kada naga sabanin alkhairi idan ba haka ba ku duka biyun sai kun gamu da bacin raina" duban amman tata tayi,handsfree ne saboda haka tana ji
"Kina jina ko?" Inji hajja yakolo ta dora
"Ki biyo su meram ku taho tare,su furma da kaajima zasu zo jibi su daukesu,ki biyosu nan ina son ganinki"
"To hajja" ta fadi a sanyaye daga haka ta katse kiran,miqawa amma wayar tayi ta karba ba tare data ce komai ba ta miqe ta fice,don ba al'darsu bace babba ya fada kaima ka fada
.
Kwanansu biyu a kano suka dauki hanya sai maiduguri,bata iya tafiya ba sai data turawa rumana tex na tafiyar tata,ta yi mata fatan alkhairi,sai kuma ta kirata ta fara mata qorafin ta nemi izinin tafita gun rayyan ne,tsaki taja sannan tace
"Kinga ke da mininki ku fita sabgata wallahi" ta kashe wayar baki daya ta cillata cikin jakarta don tasan halin rumana da neman abun fada tsaf zata sake kiranta ta kuma tubure mata,gidan hajjan ta sauka wanda a baya na gaya muku gida ne mai girman gaske mai dauke da part part wani part din ma babu kowa ciki,tare take surukanta saidai babu takurawa kowa cikin gidansa yake yana rayuwarsa yadda yake so,tunda taje hajja yakolo ke mata mita har sau da tayi kuka ta sarara mata,wani gyara da shiri da sukewa amaren barebari aka fara yi mata,kusan zamanta a can yasa ta dan samu nutsuwa har ta fara manta wasu damuwoyin nata,ga matan baffanninta akwai kirki meram,fatime,ayysa da kuma nafissa,kowacce nan nan take da raihana,yau tana parta din waccan gobe tana na waccan,sukan sata a gaba kowacce da irin darasin da zata dora mata wandabkowacce macen kanuri ke taqama da shi,ganin cewa bata girma cikinsu ba batasan da yawa daga al'adunsu da surrukansu ba,baki kawai take sakewa tana kallonsu,basu san babu wani tanadi da take buqata ba?,gidan 'yar uwarta fa zata shiga,binsu kawai take da kunne da baki,nan ta soma ganin al'adar garinta tsantsa,al'ada ta uwa da uba,cikakken isa girma da iyawa irinta kanuri,ta lura kowanne bangare wannan karon a shirye yake da aurenta ba kamar wancan karon da akayi cikin gaggawa ba ba tare da shiri ba,yadda taga suna mata kyautar sai ta tsaya dubansu,gold wani 'yar sarqar hannu,wani ya bata zobe wani ya bata barima ta kunne kota hanci,dariya falmata cousing dinta take mata sosai tana fada mata haka al'adarsu take lokacin bikin aure,kwalliyar gold sukewa amarya musamman idan dangin irin nasu ne masu wadata.
_A nan zamu tsaya in sha Allah saboda gabatowar watan azumi wata mai albarka sai zuwa bayan sallah da yardar Allah,muna fatan Allah ya yafe mana kurakuranmu,ya bamu dacewa,yasa muna daga cikin 'yantattun bayinsa ameen summa ameen_
*subhanakallahumma wa bi hamdika,ashhadu an ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika*🤲🏼🤲🏼🤲🏼
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
*dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu aron rai da lafiya,tsira da aminci su sake tababbata ga wanda ba'ayi ba kuma baza a yi kama tasa ba dan gatan Allah annabi muhammad s.a.w,Allah ya karbi ibadunmu ya yafe mana kura kuranmu,yasa muna cikin bayinsa da ya 'yanta amin*
*Babi na talatin da takwas*
Cikin sati biyu ita kanta a jikinta tasan ta sauya,gyara suke mata irin na wadda ta taba yin aure duk a tunaninsu hakan take.
Bata sake gasgata qaunar da 'yan uwanta ke mata ba sai ranar da aka fara biki,dangi ne masu zumunci gami da kara wadanda basu manta alkhairin da abbanta ya mata ba lokacin da yake raya,kamu sukayi mata irin na al'ada,washegari aka hada dinner na dukka family,wata washegarin akayi yini,a ranar aka yi mata hadadden qunshi irin na bare bari ja wanda ya sake fidda kyawun ainihin kalar fatarta chaculet wadda gyaran da ta sha ya sake fidda mata kyawunta na musamman.
*************
Qarfe goma na safe ta farka saboda gajiya,anata hada kaya da shirin tafiya kano da zasuyi washegari don a miqawa su ummu ita su gabatar da nasu bikin,masu zuwan nada dan yawa don haka gidan kusan kowa cikin shiri yake,toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin mutuniyar tata doguwar riga ta wani lace dinkin buba wadda tana cikin kayan da hajja yakolo ta mata,tayi matuqar karbarta,bata wani yi kwalliya ba sai dan kwalin data daura kawai ta fito falon hajja yokolon don ta samu abinda zata karya.
Tana gefan hajjan tana shan farfesun kaza mai hade hade,tana yi tana mita hajjan na doka mata harara.
Baba gana ne ya shigo hade da yin sallama idanunsa kan raihana,ya samu gefen hajja yakolo ya zauna yana janta da wasa,ta biye masa suka dan taba barkwanci,raihana ta gaidashi ya juyo yana amsawa gami da yi mata Allah ya sanya alkhairi,ta amsa kanta a qasa tana dan jin nauyinsa sabida yana ganin kamar ta gujeshi ne,tana jinsu suka gama hirarsu da hajja yakolo ya miqe ya fidda kudi daga aljihunsa,rafar dari biyar biyar ya ajjiye gefanta
"Amarya ga tawa gudun mawar" kai ta kada gami da cewa
"Ba haka tsakaninmu fa" hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa yana fadin
"A'a,saidai idan kin raina ne" da sauri ta kada kanta tana fadin
"Ni na isa,na gode qwarai,Allah ya saka da alkhairi" ya amsa yana musu sallama ya fice.
Kamar a mafarki ta fara jiyo muryar rumana daga harabar gidan,da sauri ta miqe tana nufar qofa ta yaye labulen falon,ita dince kuwa sanye cikin swiss orange dan ubansu,gefanta zainab ce dauke da
Islaha,juwairiyya qanwar rumana na gefanta,sai wasu mata su uku dangin abba yusuf daya kuma qanwar ummu ce dukansu daga nijer.
Bakinta har kunne ta qarasa ta rungume sisinta,duk ta manta wani fushi da take da ita,sunyi kewar juna sosai,ta yi musu jagora zuwa babban falon hajja yakolo,karba ta girma da mutunci aka yi musu sannan daga bisani suka kebe dakin da raihanan ke zaune ita da sisinta.
Tsaf suka kammala shirin kwanciya bacci,rumana na saman gado tana ta faman amsa waya,ko ba'a gaya mata ba tasan da wanda suke wayar,hakan ya sanya ta janyo akwatinta tana ci gaba da shirya kayayyakinta.
A hankali ta sauke wayar daga kunnenta bayan sun kammala tayi murmushi tana duban raihana
"Amaryarmu kinga kuwa yadda kika qara kyau,gaskiya kanuri sun iya gyara,kice gwara da nazo da kaina
Ba aike ba kada agudar mana da ke,da alama ma ke baki kewar angon naki"harara ta jefa mata tana sake kin zafin yadda rumanan bata kishinta
"Wa ya damu da shi,ke dai daya dama kuje can ku qarata" gira ta hade tana duban raihana sannan ta tashi ta zauna
"Gaskiya na fara gajiya da rashin karar da ake nuna mana,ko kunyata baki ji kike gasawa mijina baqaqan maganganu a gaba na?"
"Ko me aka yi muku ma ku kuka jiyo,kuyi zuciya ku huta mana,muma mu huta da shigegen da ake son mana ta dole"tabe baki tayi tana dubanta
" dadin abun dai kin san waye mijina wallahi yafi qarfin talla balle ma kice"itama bakin ta tabe tana sanya atamfar hannunta cikin jaka
"Ke kikasan wannan,ni kam bai dameni ba,ku yarda qwallon mangwaro kawai ku huta da quda shine zaku birgeni"
"Baki isa ba kuma wannan,duk dabararki" rumanan ta fada tana matsowa tana tayata hada kayan
"Gwara ma na tayaki don ki sake tabbatarwa tafiya wajib,aure daram" bata sake cewa da ita komai ba don ta fuskanci abun nata har da neman magana,kusan raba dare sukayi suna hira saboda rumanan bata sake jangwalo mata zancan rayyan ba.
Goma na safe kowa ya kammala shirinsa don tafiya kano wanda acan za'a qarasa bikin da daurin aure baki daya.
Fitowarta kenan daga dakin hajja yakolo cikin dinkin lace riga da skert wanda aka rufe da laffaya mai asalin kyau da tsada ta bare bari wanda ke fidda wani sihirtacce qamshi bayan dogon fada da jan hankali da tasha,idanunta ya hada ja saboda kukan da tasha,kowanne sake jaddada mata yake taci gaba da riqe rumana 'yar uwa,ammanta har da qarawa da cewar matuqar ta musguna mata ko ta cutar da ita bata yafe mata ba,ta yaya ma zata iya cutar da 'yar uwarta?,ta wacce hanya ma zata iya cutar da sisinta?,ba shakka rayyan ya gama da ita ya shiga rayuwarta,ranta cunkushe suka dauki hanyar kano ita da sauran jama'arta dangi 'yan uwa da abokan arziqi.
Ko cikin motar duqunqunewa tayi tana ci gaba da zabga kukanta,haushin rayyan take ji da zafinsa sosai cikin ranta,bata yadda sun shiga mota daya da rumana ba don batasan kukanta ya daga mata hankali.
Sai la'asar sakaliya suka isa kano,sama ta gama hada hadari iska kawai take bayarwa mai dauke sa qamshin qasa kasancewar damina ta shigo wadda da ita ake azumin ramadan,tun kan su kammala parking idanunta suka sauka kan motarsa dake ajjiye a gurin ajjiye ababan hawa na gidan,tsintar kanta tayi cikin faduwar gaba,ko kadan bata da muradin su hadu da shi,ta lumshe idanunta tana jin kowa na ficewa daga motar amma ita ta kasa motsi har sai da taji an kama hannunta,ta bude idanunta a ahankali don taga waye
_kuyi haquri da wannan saboda cika alqawari ku bini bashi gobe da yardar Allah_