← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 66

Sashe 18

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baice da ita komai ba sai da yaga kukan yaqi sararawa
"Ya kamata ki tsagaita da kukan haka nan don bazai zamar miki mafita ba" ya fada yana nufar table dinsa,ya rufe computer ya tattare duka kayan aikinsa guri daya ya kwashe wayoyinsa ya zuba a aljihunsa sannan ya kuma dubanta
"Ki shiga toilet ki gyara fuskarki mu wuce gida" ya fada still yana tsaye rungume da hannunsa,kamar an tsikareta haka ta miqe duk da jirin da take ji,domin babu abinda takeso yanzu da ya wuce ta ganta a gida kwance kan gadonta ko zata samu sassaucin abinda takeji.

Tafiya kawai take amma ji take iska ce tafiyar da ita,haka take jinta babu nauyi ko kadan.

A 'yar harabar ajiye motocinsu yayi parking,ya dubeta lokacin da take kici kicin bude qofar motar
"Duk tunanin da zakiyi kiyi shi,amma kada ki taba zaton ko da wasa rayyan zai barki" sabbin hawaye masu dumi suka biyo kuncinta,bata iya furta komai ba face ficewa daga motar.

A hankali take kutsawa cikin gidan tamkar ba zata shiga ba,addu'a take cikin ranta kada Allah yasa tayi karo da wani cikin rumana ko ummu,don bata da amsar da zasu bata idan sukaga yadda fuskarta ta sauya,wanda kukan da tayine ummul aba'isin komawarta haka.

Cikin kitchen ta hangi rumana da alamu girkin rana take shirin dorawa,hakanan taji wata mummunar faduwar gaba,cikin sanda tamkar barauniya ta shigeta ta kutsa falonsu,nan ma babu kowa hakan ne ya bata damar shigewa cikin dakinsu,a qasa ta watsar da duk wani abunda ke hannunta ta fadi bisa gadon bayan ta dora kanta saman filo,wani sabon kuka ne mara sauti ya qwace mata,kadaici da kewa irin wanda bata taba ji ba ya mamayeta,me yasa?,me yasa rayyan zaiyi mata haka?,me yasa yakeson tuno mata wani abu da ta jima da yin jana'izarsa cikin babin rayuwarta?
Cikin qanqanin lokaci zazzabi mai zafi ya garzayo ya rufeta kirif,ta dinga rawar sanyi ita kadai,hakan ya sanyata jan bargo babu shiri ta lulluba,tafi minti ashirin cikin wannan matsanancin halin kafin wani wahalallen barci ya saceta wanda ko daya babu jin dadi cikinsa.

Sai data daura alwala ta shigo cikin dakin nasu bayan ta kammala girkin rana,qarfe biyu ne harda minti goma,mamaki take na rashin ganin raihana ko rayyan kamar yadda yayi mata alqawarin zasu dawo da wuri,ta shigo da niyyar idan ta idar da sallar azahar tayi kiransu taji ko lafiya sai kuma idanunta ya hango mata mutum lullube cikin bargo,ta qarasa bakin gadon a hankali ta janye bargon tana duban ta,kallo daya tayi mata ta tabbatar ba lafiya take ba,tafin hannunta ta dora saman goshinta da niyyar tashinta.

Sanyin da taji saman goshinta yasa ta bude idanunta a hankali sukayi tozali da rumana wadda dumin da taji jikin raihanan ya jefata cikin damuwa,take abinda ya farun dazu ya dawo mata fes cikin kwanyarta,addu'a ta shiga yi Allah ya sanya cikin mafarki ne
"Sisi,me ya sameki haka?" Maganar rumana cikin damuwa ta dawo da ita hayyacinta,sai ta maida idanunta ta lumshe,zuciyarta ta karye wasu hawaye masu dumi suka shiga fita daga idanunta,ji takeyi ta tsani kanta gaba daya
"Subhanallah,sisi na me ya sameki don Allah kiyi magana mana,ga zafi a jikinki ko baki da lafiya" daure zuciyarta tayi cikin dan qwarin gwiwar da ta bawa kanta tace
"Ciwon kai da zazzabi ne ke damuna"
"Ayyah,sannu kinji sisi,ki tashi ki watsa ruwan famfo ki daura alwala ko zazzabin zai ragu,sai na kawo miki abinci da magani kisha ki kwanta,ko kuma na gayawa ummu muje asibiti kada anjima yafi haka" da sauri ta riqe hannun rumanan zuciyarta na sake karyewa,kuka nason qwace mata amma tana danneshi
"Kada ki gayawa ummu kinsan yanzu zata daga hankalinta,bari naje na watsa ruwan in sha Allah zai sauka" ta fada tana qaarara jikinta tare da miqewa,jiri taji na sake dibarta gudun zuciyarta na kuma daduwa amma sai ta lallaba ta shige bayin.

Kafin ta fito har ta kawo musu abinci wadda mostly tare suke ci dama matuqar suna tare,doguwar rigar wani material mara nauyi ta saka,ta goga roll on ta tufke kanta dake tsefe ba tare da ta damu da ta sake tajewa ba,sallah tayi sannan ta zauna suka fara cin abinci duk cikin dakiyar ta,don babu wani dandano na abincin ko kadan da ke tasiri kan harshenta,turashi kawai take rumanan nayi mata sannu jifa jifa,ga tsammaninta duk ciwon ne,a daddafe suka gama ta balli maganin ta sha ta koma gado,rumana ta gyara gun ta dawo ta nade saman nata gadon ta hau charting lokaci lokaci kuma tana gadin raihanan.

A boye take sake wani kukan,nauyin rumana takeji sosai,ji take tamkar sun sabawa mahaliccinsu ne ita da rayyan,har gab da la'asar tana abu daya,daidai lokacin da rumana ta fita dora sanwar dare kira ya shigo wayarta,mama fanna ce ke kiran,tsayawa tayi tana kallon sunan data sanyawa maman nata,wani rauni ya ziyarceta,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gabanta ko zataji sanyi cikin zuciyarta,ita kadai tasan masifa da fitinar da rayyan yau ya haddasa mata cikin zuciyarta,gashi har gangar jikinta ta amshi nata kason ta hanyar zazzabi da ciwon kai.

Katse kiran tayi sannan tabi maman nata,tayi mata sallama da dasashshiyar muryarta da kuka ya dausasheta ya kusa sawa hancinta mura
"Lafiya kike raihana?" Maman ta tambayeta,kai ta kada tamkar tana ganinta
"Lafiya lau mama mura ce ta kamani,ya gida yasu ya gana da su zainabu"
"Lafiyansu qalau" maman ta bata amsa ba tare data bi takan tambayarta ta farko ba,tunda ta riga data sani lafiya lau raihanan take,don ko ita data haifeta da ubanta marigayi alhj bukar riqon da zasuyi mata kenan.

"Dama cewa nayi bari na gaya miki bikin falmata ya taso('yar qanwar mama ce),jiya aka kawo lefenta an saka sati shida,wata daya da sati biyu kenan"
"To mama Allah ya sanya alkhairi,zan kirata nima in sha Allahu,idan kuma mun gama exams lokacin in sha zan halarta"
"To Allah ya yarda,ina diyata rumana?,na kirata wayarta a kashe"
"Ta saka a chargy ne tun dazun" ta fada a gajarce saboda kanta da taji yana ci gaba da sarawa"to masha Allah,ki gaishesu har fatiman duk da dazu ma munyi waya"
"Zasuji mama"
"To Allah ya qara sauqi"
"Ameen mama na gode" ta fada sannan ta katse wayar a sanyaye.

Bata kai ga tuna komai ba taji sallamar ummu hadi da turo qofar tasu,ta daga labulen ta shigo,a hankali tayi qoqarin miqewa ta zauna tare da jan dankwalinta da ya zame tana qoqarin daurawa
"Da kinyi kwanciyarki ma,sannu raihana,ashe babu lafiya?" Kanta a qasa tana tsoron su hada ido da ummun kada ta jefo mata tambayar da bata da amsarta tace
"Eh wallahi"
"Ashsha,Allah ya sawwaqe sannu,baya bata da kadan,kamar ba dazu kika tafi makaranta ba lafiyar Allah" tayi dan murmushin yaqe
"Yanzu to ya kikayi da gwajin?"
"Lacturer din ma baizo ba"
"To alhamdulillah,Allah ya qara afuwa,zuwa anjima idan kinji baki ware ba sarai kiyi magana sai yayanku ya kaiki ko clinic din nan na gaba da mu ne" fadarsa kawai da ummu tayi sai da ya haddasa mata faduwar gaba,kai ta daga kawai ummun ta sake yi mata sannu kana ta fita.

Wunin ranar sur a kwance tayi shi,ko daya ciwon kan bai saketa ba saboda azabar tunani fargaba da tsoro,har bayan sallar magariba sannan taji zazzabin ya sauka ciwon kanne jiya i yau.

Qarfe takwas da minti goma na dare ya shigo gidan,wata iriyar gajiya ke dukansa,bawai don yayi aikin da ya cancanci ace ya gajin bane,zuciyar tasa ce kawai a jigace hakan shi yayi tasiri har zuwa gangar jikinsa,rufe motar yayi sannan kansa tsaye ya wuce cikin gidan.

Parlour din babu kowa hatta da kayan kallon dake cikinsa a kashe suke,da alamu yau babu wanda ya zauna ciki,sai ya sakejin gajiya da kasala ta sake saukar masa,kan kujerar falon ya yiwa kansa masauki yana qarewa falon kallo,gun ummu zashi ko gun raihana da rumana?,yake wa kansa tambayar,bai kai ga amsawa ba rumana ta fito daga dakinsu hannunta riqe da cup da tea flask,bata ganshi ba sai data qaraso daf da inda yake zaunen suka hada idanu,murmushi ya sakar mata ita kuma ta daure fuska tana jifansa da hararan wasa
"Kada ka gayan komai,don nasanka gwanin iya dadin baki ne kai din"
"Kaina bisa wuya na,na dauki duk laifin da kike tuhumata da shi,amma yanzu dai a yimin afuwa da sassauci,kinga shigowata kenan ina buqatar tallafi" ta gyara tsaiwarta har yau bata bar hararsa ba
"Tallafi wanne iri?"
"Yunwa,gajiya,kasala,damuwa duk ni daya rumana,kunga ai ya cancanci a tausaya min ko?" Fari tayi da idanunta sannan tace
"Eh,zan iya tausaya maka ta hanyar kai maka abinci,abinda zan iya kenan?" Kai ya langabe sannan yace
"To kuma hirar fa,da yau fa cikin dakinku zamuyita a gaban sisinki" hannu ta daga masa ta hade fuska
"A'ah,ba dai yau ba,don tun rana sisi bata da lafiya,banason abinda zai takurata".
Chapter 18 · 0% Book details