Sashe 11
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tabdi,yau kam bansan kalar haukar da zaki sanya ya rayyan ba a airphort,irin wannan ado haka sister"
Dariya ta saka taba miqewa daga gaban mirrow din"kada dai ki fasan kai da yawa,kuma naje na kasa burge ya rayyan din"miqewa raihanan tayi daga kwanciyar da tayi dazun"haba.....haba don Allah wuce nan wallahi.......ba irin sister na ba dai,ta wuce wannan class din wallahi"
Dago labulen dakin da ummu tayi shi ya katse musu hirar,a shirye take cikin atamfa holland mai asalin kyau da tsadar,itama tayi kyau sosai,cas da ita ba alamun girma ko tsufa tattare da ita,wanda mutane da yawa kan alaqanta hakan da rashin haihuwa da batayi mai yawa ba
"Mun fito fa mu"
"Ummu muma mun gama" inji raihana tana saukowa daga kan gadon tare da daukar gyalenta ta yafa bisa kanta ba tare da ta daura kallabi ba,qasa qasa rumana ke wa raihanan magiya ta tsaya su fita tare don Allah kunya takeji,sai da ta gama zolayarta kan cewa taqi din,batasan da su ummun ba ta zuba ado haka sannan ta jirayeta ta gama daurinta suka fito
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:53 AM] El-hajj💥: *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo hadisin daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace((haqiqa farkon abinda za'a fara yiwa bawa hisabi a kansa ranar qiyama shine SALLARSA,idan ta gyaru tayi kyau haqiqa ya rabauta yayi nasara(ya haye kenan),idan kuma ta baci haqiqa ya tozarta yayi asara,idan aka samu naqasu ko rashin cika daga cikin ayyukansa na ibada na farilla,sai ubangiji mai girma da daukaka yace:ku duba,shin bawa na yana da wasu ayyuka da yayi na neman lada(wadanda ba farilla bane)sai a cika masa abinda (da ayyukan da yayi na neman ladan)inda aka samu naqasu cikin ayyukan farillarsa"*
_________________________
Abba da kansa yau yake tuqin don zuwa tarbo yaron nasa,shi da ummu na gaba,yayin da rumana da raihana ke zaune gidan baya,kallo daya zaka yiwa fuskokinsu su baka amsa cewar iyalin cikin farinciki da nishadi suke
Basu wuce mintina arba'in ba suka sauka cikin filin jirgin sauka da tashin jirage na mal aminu kano,a hankali suka qarasa har zuwa gurin da aka tanada domin zaman jama'ar dake jiran isowar 'yan uwansu.
Raihana ce ta miqe rumana ta kalleta bayan ta dubi agogon hannunta tana tambayarta ina zata
"Qishirwa nakeji,zan siyo ruwa yanzu na dawo"
"Saikin dawo,don ni daga nan babu inda zan dara sai naga isowar ya rayyan" murmushi ta saka ta soma tafiya tana cewa
"Dama nima bance ki rakani ba madam".
Fitowarta daga kantin hannunta dauke da gorar ruwan swan guda biyu mai sanyi suka kusa cin karo,ta dan ja baya da sauri yayin da shi kuma ya sakar mata murmushi,dauke kai tayi tana neman rabeshi ta wuce tamkar ma bata taba ganinsa ba,da azama ya sha gabanta har yau da murmushin dauke a fuskarsa yana fadin
" ranki ya dade ayimin afuwa idan nayi laifi"ya fadi yana hade tafukan hannayensa
"Na tuba nabi Allah na biki"inji al'amin.
Shiru tayi kamar mai nazari,kana ta dan saki fuska ganin yadda damuwa ta bayyana akan fuskarsa qarara
" ba wani laifi fa"ta fada a gajarce,ajiyar zuciya ya saki yana fadin"har naji dadin wallahi,ga zatona laifi nayi,kawo na rage miki nauyin"yayi maganar yana qoqarin karbar robobin ruwan daga hannunta,ganin yadda mutanen dake shige da fice a shagon suka zuba musu na mujiya yasa ta sakar masa kana ta fara tattaki don yin gaba,da hanzarinsa ya biyota din samun damar jerantawa da ita kada ta wuceshi,yana son qara mata da drink yana tsoron kada garin neman gira ya rasa ido.
Yana mata wani mugun so,saidai ya rasa ta yadfa zaiyi ya shawo kanta,ya samu number dinta saidai ta kusan zame masa hoto,don ko ya kira ba amsawa takeyi ba,hakanan ko yayi saqo ba reply.
Ya danyi gyaran murya kadan ganin sunata tafiya kamar kurame"sai kuma na ganki anan,hala wani guri zaku?"kai ta kada sannan ta numfasa tace"munzo taryar yayanmu ne"cikin zumudin da baisan yayi ba yace"kice yau zamu gaisa da 'yan gida ko?"sai taci burki ta tsaya inda take tana dubanshi hannayenta harde a qirjinta
Tun rumana na duban hanyan dawowar raihana har ta shagala saboda jin isowar jirgin dake dauke da su rayyan,gaba daya ta maida idanunta sashen da take saka ran fitowarsa
"Af,kin ganshi can ma" inji abba
"Kai,kai,kai,kai,masha Allah,masha Allah,Alhamdulillah" inji ummu da bakinta ya kasa rufuwa bayan hango yaron ta kuma gudan jininta da tayi,wani farin ciki ta dinga ji soaai,shekara tara ba wasa bace,yayin da rumana ta sandare gu daya,ashe babu abinda ta gani cikin hoto,indai haka ne ma to ba shakka hoton rage masa kyau yayi ya boye.
Sanye yake da suite ash colour masu bala'in kyau da daukar ido,gashin kansa a kwance luf baqiqqirin sai sheqi yakeyi,fuskarsa saye take cikin sun glases,yayin da qafarsa ke saye cikin sau ciki na maza mai matuqar kyau da tsada,idan ka hangoshi sai ka rantse da Allah daya daga cikin jaruman bollywood ne,ya sake fari,tsaho kuwa ba'a magana,saidai ya masa kyau don yana tafe ne da 'yar qibar da tsawon ya boyeta
Hangosun da yayi yasa fuskarsa ta fadada da murmushi,sannu a hankali ya tako zuwa inda suke,rungume juna sukayi shida abba yana masa sannu da zuwa bayan ya saki abban ya dan rungume kafadar ummun yana dariya qasa qasa,sannun itama take masa.
[7/23, 8:55 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo daga nana Aisha R.A tace:manzan Allah S A W ya kasance yana son damantawa(wato fara komai da dama),cikin tsarkinsa ne,ko cikin sanya takalminsa,ko cikin taje kansa,da cikin al'amuransa ma baki daya))*
_______________________
*Babi na sha biyu*
_note_
_Shekaran jiya babi na goma sha daya mukayi na manta ban rubuta ba_
Sanya wayar tayi a silent tana ci gaba da kallonta har kiran ya katse ba tare data daga ba,yana katsewar kuwa tayi gaggawar kashe wayar baki dayanta,yayin fa gefe daya rumana da rayyan ke kallonta,rumana na kallonta ne cike da fargaba da faduwar gaba,ganin ta kashe wayar ne ya sanyata sakin boyayyar ajiyar zuciya tana hamdala cikin ranta tare da godewa raihana.
"Nifa na yiwa abokina kamu?" Duka suka waiwaya suka dubeshi,rumana dariya na cinta tace"kamun wa?"
"Kamun raiha mana" kasa boye dariyar tayi sai ta fashe da ita tace
"Tab,lallai ya rayyan ashe kana gab da shan kunya" girarsa ya dage yaba dubanta
"Kamar yaya?"
"To ai raihana da kake gani ba abokiyar hada kai bace ta wannan bangaren,wallahi kunya kawai zata baka,nan da kake ganinta ko zance bata taba tsayawa ba".
Cikin mamaki ya dubeta kana ya dubi rumana
" dalili dame?"baki ta tabe gami da dage kafadarta
"Nima bana ce ba,amma ta taban gayan har yau bata samu wanda ya dace da ra'ayinta ba"
Komawa yayi rayyan dinshi sak yana dubanta
"Am seriouse raiha,na miki sha'awar amir,abokin karatu na ne,tare muka kammala da shi,dan jigawa ne kazaure,amma asalinsu 'yan kano ne,yana da hankali da nutsuwa,kuma nayi imanin taku zato zo daya da shi,na sanshi kema na sanki" kanta na sunkuye ba tare data ce komai ba,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta.
Tana jin bata data cewa,abinda ya rage mata kawai ta baiwa amir din dama tunda har rayyan din ya yaba da shi don haka "to" kawai tace da shi,cikin dabara ta sullubewa hirar tasu ta shige cikin gida ta barsu anan suna tsinkar fure
*************
To yadda suka tsara yin ziyarce ziyarcensu a dangi cikin satin da rayyan din ya dawo hakan bata samu ba,sai da yayi hutun kwana uku ba inda yake zuwa yana gida,cikon kwana na hudu ne motocin da yayi odarsu suka iso,guda uku ne sababbi fil masu azabar kyau da daukar ido,daya tashi,daya ta ummu daya abba ya sayawa,shekara shida yayi ya kammala masters degree dinsa a fannin computer science,wani kamfani ne mai zaman kansa suja riqe shi har shekara uku yana musu kyau,suna matuqar ji da rayyan din sakamakon basira da qwaqwalwa da Allah ya bashi,mutum ne shi dan gaske tsayayye,jajirtacce kuma mai riqo da gaskiya da amana,to kasan halin malam bature,irin mutanen da yake son hulda da su kenan,shi kansa yasan ba qananun kudade ya samu da su ba,don suna ninka masa albashinsa ne duk don ya yarda yaci gaba da aiki da su,ko da ya tashi tahowa ya ajjiye musu takardar barin aikin ba haka suka so ba,hakanan suka qyaleshi don babu yadda zasuyi,amma sun sanar da shi duk lokacin da ya sauya ra'ayi suna maraba da shi.
Ba qaramin murna sukayi da wannan kyauta ba,sosai suka dinga sa masa albarka,sannan ya sanar da abba filayen da ya siya guda biyu,daya anan jikin gidan su da suke ciki yanzu,daya kuma cikin unguwar rijiyar zaki ne,yace na rijiyar zakin nashi ne yana so ua fara ginawa,wannan na kusa da su kuma nasu ne
"Masha Allah,da kyau hakan yayi rayyan,Allah ya albarkaci rayuwarka,ya baka zuriya ta gari,ina ganin zuwa ko zuwa sati na sama lokacin abbanku dalhatu ya dawo daga tafiya sai ayi maganar sa auranku kai da rumanan,koda ginin bai kammalu ba indai an samu iya inda zaka iya ajjiyeta falil lahil hamdu" ya dan sadda kai kawai yana sakin murmushi cikin jin kunya
Sun zaga dangi kuwa sosai yadda ya kamata,wanda kusan mafi yawa dangin alhaji dalhatu ne,tunda sune mazauna kano,nasu ahlin kadan jigon suna nijer,amma duka daya ne haka suke daukar junansu.
Kusan ziyarar kamar qara wata 'yar manuniya ta zama kan soyayyar dake tsakaninsa da rumana,wanda baisan da maganar ba a yanzu yasan da ita,kowa murna yake da sam barka tare da addu'ar ganin lokacin aurensun.
Hutun da suka samu na makaranta saboda gama exams dashi sukayi amfani suka mori lokacinsu,hakanan rumana ta samu damar bargaje soyayyarta da rayyan yadda ya kamata.
Abu guda tak dake mata barazana,yawan kira daga abokanta na makaranta maza da take samu,wanda hakan sau tari yana dagula mata lissafi,duk da qoqarin kaucewa idon rayyan da take amma fargabar na nan tare da ita