← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 66

Sashe 40

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qwallar itama take sharewa saboda tsabar tausayinsu,haqiqa babu wani wanda zaiso yaga wani dan musulmi cikin irin wannan harkar ransa ya masa dadi,bare ace dan uwanka na jini ne yakeyi
" babu abunda aka yimin dama,ni tsakanina da ku sai fatan alkhairi,kun nunan so da qauna,abinda ya shiga tsakanina da anty sauda kuwa nasan ajizanci ne irin na dan adam,ammar kuwa iya zaman mu da shi banda wannan abun bai taba takuran ko muzan tani ba,addu'a zamu tayi ubangiji Allah yasa qarshen abun ne yazo,Allah ya tsare musulmi baki daya"
"Ameen ya Allah,mun gode raihana,Allah yayi miki sauyi mafi alkhairi" da zasu tafi ta basu saqon gaisuwa gun hajjajun,ta kuma ce zata kira layin fatima sai su gaisa,sai kuma ta hararu fatiman
"Koda yake babu ruwana ma da ke,tunda kika karya alqawarin da kika yimin"
Murmushi tayi"anty bazan iya zuba kunnuwa na bane naji ana zaginki bayan kece ke da gaskiya,ke kikayi SADAUKARWA tare da RUFIN ASIRI ga dan uwanmu"
"Gara data fadi din,ai kinga ko addu' ma zage damtse da yi masa" cewar sabira,har qofar gida ta rakosu sukace ta gaida ummu tunda basu sameta ba,taje gadon qaya gidansu rumana duba jikin umman rumaman da bata jin dadi.

*****************

Cikin watanni uku komai ya wuce tamkar ma ba'a yi ba,suna waya da fatima akai akai suna gaisawa har ma da hajjaju,hakanan anty sauda da sabira ma na kiranta lokaci lokaci,saidai babu wanda ya taba yi mata zancan ammar kamar yadda itama bata taba tambayarsu.

Sosai take rayuwarta a sake,taje makarantarta ta dawo,idan ta dawo kuwa bata sake fita sai da wani babban dalili,rumana kam tayi ciwon baki har ta gaji,dom babu yadda batayi tazo ta ko kwana biyu bane amma sam ta qiya,ko islaha saidai ta turata a daukota idan babanta yaga dama ya yarda,rayyan kuwa sau biyu ta ganshi cikin watanni ukun,saboda ba zama take gidan ba,lokacin da zai zo gaidasu ummu wani lokaci ta fice makaranta,idan da daddare ne tana daki tana karance karancanta na al'ada.

Zuwa lokacin tamkara jarrabi sai ga maneman aure sun fara mata caa,idan tana ganin qimarka ta rangada maka qarya tace ita din matar aure ce,idan ka fiya naci kuma tayi maka fata fata,sam bata yarda su biyota koda hanyar unguwarsu ne balle akai gidansu,ko kadan bata jin sha'awar yin aure dai dai da misqalazarratin,jarrabawa kawai take jira zuwa yanzu dalibansu su kammala ta dage zuwa maiduguri ta bawa kano iska.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:41 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Daga sa'ad dan abi waqqas R.A yace:naji manzan Allah S A W yana cewa"haqiqa Allah yana son mutum mai taqawa mai wadatar zuci,mai shagala da ibada da neman na kansa"*
_Allahumma salli wasallim ala khatimunnabiyyina wa imamul mursalina_👏🏼
_____________________

*Babi na talatin da daya*

_abinda nake son jan hankalin makaranta da shi shine,ku kula,raihana da rumana kowacce nada managartan halaye kyawawa,kowacce nason 'yar uwata tsakani da Allah,kowacce nason farincikin 'yar uwarta,koda kuna ganin kuskure ko ba daidan daya daga cikinsu,to ku daukesu a 'yan adam ajizai kamar kowa,har yau babu wadda tayi wani abu da niyya ko nufin cutar da 'yar uwarta da gangan,muje zuwa_

Fushin da rumana ta hau yi da ita gadan gadan na yadda ta nisanci zuwa inda take ya sanyata yau asabar ta tashi da niyyar zuwa mata ta yini,daga nan ta dauko takwara su taho ta musu weekend.

Qarfe sha biyu ta gama shirinta cikin wani lace mai azabar kyau blue light and dark wanda aka qawata shi da tsadadden dinki na doguwar riga,da takalmi mai tsinin dunduniya tayi amfani mai igiyoyi,wanda ya mata kyau,haka 'yar madaidaiciyar hand bag dinta wadda ta shiga da kayanta da mayafinta dukka irin na wayayyun mata masu aji da tsara ado mai sanyi.

Tana kammala sanya sarqa da dan kunnenta ta dauki turarenta mai taushi da sanyin qamshi ta fesa,kana ta yafa mayafinta ta zari jakarta a gaggauce ta fito saboda tex din rumana da tace mata indai ta wuce sha biyun bata zo ba to wallahi saidai ta kwana.

A kitchen ta tadda ummu ita da lantana tana gwada mata abincin da zata dafa musu da rana tunda su biyu ne kawai a gidan,cike da sha'awa da qauna ummu ta dubi raihanan
"Kinyi kyau diyata,saikim dawo ki gaidasu" murmushi tayi wanda ya fidda fararen haqoranta sannan tace
"To ummu zasuji" sannan ta fice,a harabar gidan ta tsaya ta dauki motarta sannan ta fice daga gidan.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta fara ambata jin motar na shirin tsaya mata,gefe ta samu ta faka ta sannan ta bude murfin ta fito,kusan minti arba'in ta shafe tana tabe tabenta amma ko motsawa motar taqi yi,rufe gaban motar tayi sannan ta koma jikinta ta jingina tana duban titin,hanyar sam bata wucewar jama'a bace,bugu da qari gashi rana a take take,babu yawaitar zirga zirgar motoci.

Motar ta koma ta fiddo jakarta sannan ta kulle ta baki daya ta sake matsowa gaban titin ko zata samu abun hawar da zai qarasa da ita hannunta riqe da wayarta tana neman number din bakaninken dake musu gyara,lokaci bayan lokaci tana daga idonta ta sauke kan titin cike da fatan samun adaidaita ko taxi.

Da qyar ta samu lambar john ya shiga,ta kara a kunnenta suka fara magana,dai dai lokacin da wata doguwar baqar motar mai baqaqen glass data gifta yanzun take ribas tana dawowa da baya,tsayuwar mintina kusan hudu tayi sannan taga murfin baya na budewa lokacin da ta gama wayar ya shaida mata zaizo ya karbi key din gidan rumanan ya duba mata motar.

Tana kici kicin sanyata a jaka hancinta ya soma jiyo mata wani qamshi,ta daga dara daran fararan idanunta suka sauka kan farin matashin wanda ke sanye da baqar kufta ya kafa baqar hular damanga akansa,murmushi ya sakar mata sannan ya tako zuwa inda take
.

Sallama ya mata amma tayi burus kamar bata jishi ba har sai daya maimaita sannan ta amsa a ciki,motar tata ya duba sannan ya kalleta
"Kash,amma wannan mota bata yi adalci na data macewa sarauniyar mata,tayi silar tsaiwarta cikin rana" sai ta daga idonta ta dubeshi kawai,ko waye ya gaya mata mutuwa tayi?
"Ko za'a yimin izinin in duba miki motar ko zan iya tashinta?" Wannan karon ma kallonshi tayi,sam ko guda bai mata kama da wanda zai iya wani aiki ma daya danganci haka ba gyaran mota ba balle tayi zaton ko bakanike ne,zallar hutu ne muraran bayyane a jikinsa
"Waye ya gaya maka mutuwa tayi?"murmushi ya saka sannan yace
" jikina ne ya bani"
"Da kyau,ba mutuwa tayi ba to,kuma koda mutuwar tayi ban tsammanin zaka iya tayar da ita"
"Kika sani ko da bakanike kike magana?" Sai maganar tasa ta bata dariya har ta dan murmusa bata sani ba
"Good,tunda nayi nasarar saka wannan daurarriyar fuskar murmushi nasan ina da sa'a" sai ya dunqule hannunshi guru guda yace
"Don Allah ranki ya dade kada kimin musu,nasan mutuwa motarki tayi,kuma haka qarfen nasara ya gada,kizo muje na saukeki zuwa inda zaki" shiru ta masa don bata da sha'awar hakan,shirunta bai sanya shi fasa roqonta ba,cikin haka aka bude seat din driver,wani kakkauran mutum ne baqi ya fito sanye da kaya wadanda suka mata kama da na dogarawa
.

Sa sassarfa ya qaraso gabansa ya rusuna yace
"Ranka ya dade ya yallabai ya sanya anata kira,yana ta fadan rashin isowarmu kan lokaci" wani kallo ya masa sai kawai ya jinjina kai ya juya ya koma cikin motar.

Ganin bazai daina roqonta ba,kuma ita dinma idan tace zata ci gaba da jiran abun hawa tabbas zata iya kaiwa azahar a gun ya sanya ta amince,da kansa ya bude mata ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga,sanyi da qamshin motar ya ratsata.

Shiru ne ya biyo baya sannan daga bisani taji yace
"Na gode da kika yimin alfarama na rage miki hanya,duk da baki tambayeni ba suna na sultan abdul_ra'uf ahmad,ni haufaffen garin azare ne,anan aka haifeni nayi karatu na primary da schdry nayi jami'a ta a south africa,mahaifina shine wazirin sarkin azare,wannan ne tarihina a taqaice,bazan boye miki ba,ganin farko da nayi miki naji kin kwanta min a raina,zuciyata kuma ta gayan ma samu macen aure,Allah yasa bazakice nayi miki tsufa ba" ya fada da yana shafa sajensa da salon tsokanarshi data fuskanci halayyarsa ce,dariya ya bata sosai har sai data murmusa,jin tayi shiru bata ce komai ba yace
"Uhmmm,baki gayan wace ke ba,hakanan baki fadan matsayin da kika dauki maganata ba"
"Nikam an riga an badani" abinda tace dashi kenan.

A hankali ya qaraso cikin kitchen din,yana sanye da long sleeve t.shirt ja da farin wando wanda tsahonsa iya qaurinsa yake,bata kula sam da saukowarshi ba hankalinta yayi gaba wajen ganin ta kammala girkin,yaci gaba da takawa a hankali har ya isa bayanta,yasanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam,da fari ta dan tsorata,amma qamshi da taushin fatar data ji su suka sanar mata ko wanene,ba tare data juyo ba ta sake narkewa ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanu
"Ka bani tsoro abban islaha"
"Ayimin afuwa,mun gaji ne da jira ni da islaha,kin shanyamu a sama kinzo kin tashi dukka hankalinki cikin kitchen"
"Ayyah kuyi kin haquri ai na kusa kammalawa yaya na"
"Mukam indai don mune mun yafe,kizo kawai muje mu huta,yaufa weekend ne"
"Ku qara min minti ashirin na kusa gamawa,bana son sisi na tazo ban gama abincin tarbarta ba" sai ya sanya hannayenshi kan kafadarta ya juyo da ita yana fuskantarta
"Wai kina nufin kice min baqi zamuyi yau din ma,bayan wancan weekend din ma babu islaha mu biyu ne kawai,wannan karon kuma da muke ku ukun kice zamuyi baqi?" Sai ta narke fuska"sisi na ce fa,ai ita ba baquwa bace"
" a gurinki"
"Har da kai din ma" sai yayi shiru ganin yadda take dubansa,kai ya dan jinjina sannan ya sakar mata kafadar yana fadin
"Ok,bari naje na samo credit zanyi waya da mukhtar,kafin na dawo ki tabbatar kina sama"
"In sha Allah" ta fada tana juyawa da sauri sauri tana qarasa hada abinda bata hada din ba.
Chapter 40 · 0% Book details