Sashe 49
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna falon qasa bakin dayansu yayinda ta cika musu gabansu da kayan maqulashe,don tasan halin kausar da meela dukkansu babu baya wajen kwadayi,meela ce ta ajjiye meatpie din da ta gutsira tana dubansu
"Wai kunsan meke faruwa kuwa?" Kusan hada baki sukayi wajen fadar a'a
"Wai kishiya fa za'a yiwa sanaya" wata qawarsu ce duk da cewa gaisuwan mutunci suke kawai da rumanan,kausar ce ta fidda idanu dafe da qirji tana duban meela
"Bari don Allah,sanayan?,me sanaya ta rasa da mustafa zai kwaso mata alaqaqai don Allah,innalillahi" tace baki meela tayi tace
"Hmmm,kema dai kya fada,amma haushin da ta bani wai matar nan yadda kika san ba wadda za'a kawowa abokiyar gaba ba,tana zaune hankalinta kwance,wai har kiranta yarinyar take su gaisa" cikin wani zare idon kausar tace
"Sanayar?,anya lafiyarta qalau,ita kuwa me ya sameta haka?" Sai ta waiwaya ga rumana wadda ke zaune tana kallonsu
"Ruma kiji min wannan zance don Allah,kinji sanaya" murmushi ta saki na gefan baki sannan ta gyara zamanta
"Meye to a ciki" cikin mamaki suke dubanta,kusan tare suka furta
"Meye kuma?" Gira ta daga sannan tace
"Eh qwarai,meye,ni kaina ni na hada auren mijina,kwanan nan zaku ji biki ya taso" dariya suka saki su biyun tare da tafawa suka dubeta
"Ki daina yiwa kanki wannan fatar kada mala'ikun rahama su amsa" ta fuskanci wasa suka dauki zancan,hakan ya sanyata hade fuska
"Wallahil azim da gaske nake,kuma raihana ce sisi na in sha Allah".
Wani irin zabura kausar tayi ta gyara zamanta tana duban rumana,yayin da meela ta wamgame baki itama ta zuba mata ido,meela ce ta samu qarfin halin yin magana
" wai wacce raihanan kike nufi?,nidai nasan sisinki guda daya ce,raihana bukar ko?"kai ta gyada
"Qwarai kuwa ita"
"Kut......kina me rumana?,hankalinki daya kuwa?,kinsan ke kike fada?wacce iriyar cakwakiya ce wannan?"
"Tambayar min ita meela" inji kausar wadda keta jujjuya kai cike da ta'ajjubi,murmushi ta kuma yi
"Ras nake,don qila ma na fiku shiga nutsuwa ta"
"Wallahi ba lafiya kike ba ina tantama" cewar meela tana girgiza kai,qaramar dariya ta saki
"Meela,bakisan wace raihana ba a gurina,bakisan me raihana ta yimin ba,bakisan me ta dade tana yimin ba a rayuwa,idan na gaya miki wace ita saiki yanke hukuncin daga baya".
A nutse ta fayyace musu iyakar abinda ya kamata su sami,ajiyar zuciya kausar ta saki
" don ta sadaukar miki da saurayi shine zaki sadaukar mata da miji?maimakon ki sadaukar mata ke da wani abun daban tunda ramawa kike so kiyi"kai ya kada
"Babu wani abu da zan sadaukar mata wanda zaiyi daidai da irin abinda ta yimin,kunsan ciwo da radadin rabuwa sa masoyi kuwa?,course ya rayyan zai tafi na watanni shida na kasa daurewa a lokacin sai da aka daura aurenmu,ina ga ita data shafe wasu shekaru tana dakon son da batasan ina ne makomarsa ba,kada ki manta kausar,raihana na da damar da zata iya bata tsakamina da ya rayyan saboda son da take masa...bata aikata ba,tana da damar da itama zata iya mallakarsa....ta haqura ta barmin ni kadai duk da tsananin son da take masa,ta kare darajata a gunsa da martabata fili da boye,ta qaunaceni daidai da qwayar zarra bata taba sauya matsayina cikin zuciyarta ba,tabbas kishi ba qarya bane abune kuma mai ciwo da wahala,halittar muce haka baki daya walau mutum ko dabba,amma bazan bari son zuciya ya rinjayeni ba,bazan bari son zuciya ya kaini ya baro ba,to idan ma ban amince irin wannan ta zama abokiyar zamana ba wa kuke so na yarda ta zama?,wa kuke so a kwaso min?".
Kai meela kawai ta kada" wallahi duk da haka bakiyi dabara ba wallahi sam,tabdijan,raihanan me,akan me zan bawa wata dama ta shigo min gida haka siddan?"
"Kema kya fada meela,ban taba zaton baki da wayau ba rumana sai yau wallahi" fuskarta ta hade tsaf ta dubesu
"Idan meela ta fadi haka zan iya mata uziri da cewa ita din bare ce bata dadin da saninmu ba,amma kekam kausar bazan iya miki wannan uzurin ba,son kai da sin zuciya shike mana jagira agaba zuwa ga kogin nadama" sai ta dubi meela
"Meela,inaso ki tsaya iya matsayinki kada ki taka shingen da ba naki ba,kinsa me zaki dinga furtawa kanmu ni da raihana,matuqar babu wadda zata bani shawara ta gari kota agaji zamanmu da addu'a to bana maraba da ita" ta fada tana maida numfashi,sai suka kalli junansu sannan suka fara lalubar mayafansu suka miqe,meela kam ta kasa magana kausar ce tace
"Eh da alama bare bari sunyi aikinsu,bayin kanki bane rumana,ban taba ganin saunar matar da tayi aiki irin naki ba,mudai gaskiya ce ba zamu daina gaya miki ba ko zaki tsiremu" ta kama hannun meela wadda har waiwayen rumana take cike da al'ajani suka fice
Kai tsaye gidan rumana tayi bayan dogon fushi da dauke mata wuta da tayi na daina zuwan gidanta,wanda rabonta da gidan tun ranar da sukayi fada da rayyan din randa ya kawota.
Jin tashin maganganu kamar fada fada shi ya tsaifata tana fatan ba rigima sisinta keyi da wasu ba,cikin qanqanin lokaci jikinta ya dauki bari
.
Wani tashin hankali ya garzayo ya rufar mata,me kunnuwata ke jiye mata?,yaushe rumana tasan da maganar?,me yasa zata kuma dauki irin wannan hukuncin,me yasa.
Karo suka kusa yi sanda suke qoqarin ficewa ita kuma na qoqarin fita,hankalinta ba'a gurin yake ba saboda haka gaba tayi kausar ta bita da wani malalacin kallo,meela ce ta damqi hannunta
"Kinga zo mu wuce saura qiris a kira magariba" ta fada tana janta,ita kanta kawa mazewa tayi.
Tana tattare kayan da su meela suka gama amfani da su taji takun mutum,a hankali ta daga kanta,raihana ce tsaye hawaye na bin fuskarta,gaban rumanan ya dan fadi,sai ta ajjiye farantin hannunta ta taka inda take tsaye ta kama hannayenta
"Subhanallah,lafiya sisi,me ya faru?" Kai kawai take kadawa,cikin murya mai cike da rauni tace
"Me yasa zaki aikata haka rumana,me yasa zaki karya alqawarin da na daukarwa kaina?,me yasa kike son mu zauna qarqashin mutum daya ni da ke rumana,bayan na daukeki matsayin 'yar uwata ta jini wadda suka kwanta a mahaifa guda,me yasa rumana?" Kai itama take girgizawa,idanunta fal qwalla
"Saboda hakan shine adalci,haka shine daidai,sakamakon kyakkyawa da kyakkyawa raihana,bana son kice komai raihana,babu abinda baki bani ba a rayuwata matuqar na nuna ina so tun daga zamanin quruciya har kawo yau,wannan ne karo na farko da zan sadaukar miki nima da wani abu mai muhimmanci tattare da ni,kada kice a'ah don Allah" murmushi ta saki mai ciwo
"Rumana,tamkar fa kina cewa na auri mijin zainab qanwata ne,tamkar fa kina son halastamin abinda na jima da haramtawa kaina,bana buqatar wata sadaukarwa daga gareki rumana,'yan uwantakarmu ta isheni,za kuma taci gaba da gamsar da ni,bana buqatar qari kan hakan" .
Kai ta sake girgizawa"bazai yiwu ba,dole zuciyarki ta samu abinda take so kamar yadda kika bani abinda nima nake so"idanunta ta bude sosai kan rumanan
"So,so fa kike cewa,a da kenan,tuni na jima da shafe babinsa daga rayuwata indai akan rayyan ne,na jima da koyawa kaina mantawa da duk wani abu da ya shafe shi,babu wannan cikin raina ko kadan,labarin da ne wannan ba na yanzu ba" dariya ta saki wadda ta sanya raihanan tsayawa kallonta
"Haba raihana,kada fa kimanta rumanan bata jiya bace,tasan so,tasan nacinsa tasan masifa da jarabarsa,so na haqiqa baya taba gushewa cikin zuciya komai tsananin wahala dadewa ko tsawon shekaru,mamaki kika bani ma raihana,baki dauke ni ni da ke duka daya bane da har kika kasa sanar da ni mekw damunki tun wancan lokacin,da sanarmin kikayi da kinfi burgeni fiye da sadaukarwar da kika yimin,kika so jefa rayuwarki cikin matsala,me kike tunani da kun samu zuri'a da ammar?,me kike tunani da ammar ya samu nasarar lalata rayuwarki?,kina zaton zan iya yafe miki da kika baiwa wani damar wargaza rayuwarki saboda ki bani farinciki.....raihana.....aurenki da rayyan ya zama wajibi,ko don na ceci rayuwarsa wadda take gab da tarwatsewa matuqar yaci gaba da rasa abinda yake kwadayin samu" idanu take bin rumanan da shi,ta fuskanci babban qalubale ne a gabanta,halin rumanan ke shirin motsawa na rigima kafiya da taurin kai,taga alamar idan na wuta wuta tayi mata ba ta daura damarar kawota gidan rayyan a matsayin matarsa ta biyu.