← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 66

Sashe 2

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunsan hali sai yazo daya ake abota,yadda alhj yusuf yake mutum mai matuqar kirki,gaskiya riqon amana taimako da son jama'a haka alhj dalhatu take,nan da nan abota da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakaninsu duk da bambancin nau'in kasuwanci dake tsakaninsu,saboda shi alhj dalhatu yana saida atamfofi ne kala daban daban kaama daga qarama mai sauqin kudi zuwa mai tsada,sau tari alhj yusuf kan karbi atamfofin daga hannun alhj dalhatu idan zai koma qasarsa nijer ya tafi da su ya saida,ko kadan alhj attahiru bai karbar kudin atamfofin daga hannunshi har sai ya siyar ya sake dawowa nijeria duk da cewa bawai baida kudin bane babu ma zancan matsalar kudi tattare da shi da kudinsa a hannunsa,tafi tafi sai Allah ya sanuyawa harkar atamfar tasa albarka wanda babu dadewa ya bude babban shago na atamfofi zalla,ba'a dauki wani dogon lokaci ba shagon ya karbu cikin garin diffa da sauran maqwaftan garin,don wani lokaci wasu tun daga dosso tillaberi niamy ko zinder zaga ga sun shigo sari,hakan ya sanya ya sake bude wasu shagunan cikin wadan nan garuruwan,wadansu nashi shi kadai wadansu kuma shi da alhj dalhatu ne.

*Alhj dalhatu*

Haifaffen qasar nijeria ne cikin garin kano qaramar hukumar kano municipal,kowa ya sani cewa 'yan cikin gari a kano irin unguwannin da suka hada zage,daneji,marmara aisami,qoqi makwarari da sauransu mafi yawancinsu kasuwanci shine babbar sana'arsu,to haka yake ga alhaji dalhatu shima kasuwancin ya gada daga wajen mahaifinsa alhj attahiru,alhj dalhatu shine da na hudu a gidansu a cikinsu su goma da Allah ya bawa mahaifinsu wanda yake da matan aure guda biyu,maza su shida mata hudu,wannan kenan.

*alh bukar ibrahim*

Shima haifaffen nijeria ne cikin garin maiduguri qaramar hukumar kwaya kusar,familynsa asalinsu iyali ne ga malam muhammad al'amin elkanemi wanda ake kira da shaihu laminu wanda asalinsu daga yankin larabawa ya fito ya zama kuma ya zauna a kukawa,babban malami ne da ya taimakawa barno tun zamanin da fulani suka zo yaqar bare bari,mutum ne da ya bada gudun mawa mai yawa cikin qasar borno baki daya,daga baya ne da zuri'ar tayi yawa aka samu sauyawar muhalli gun wasu daga cikin zuriyyar tasa.

Shi din ma kasuwanci ne yake kawoshi kano,yana kusuwancin huluna ne cikin kasuwar kwarin,wanda ya zama tamkar shi dila ne na huluna,yana rabasu ga manya da qananun 'yan kasuwa,to shi din ma dai karamci da mutuncin alhj dalhatu yasa yake sauke kayansa a rumfar tasa kafin ya gama rabawa wanda zai bawa din,anan tasu tazo daya su ukun baki daya,alhj dalhatu alhj yusuf da kuma alhj bukar.

Duk alaqar da aka ginata domin Allah to da ikon Allahn kuwa shike riqe da ita,babu wani abu da zai bata ta,hakanne kuwa ya kasance tsakaninsu,aminci mai sunan aminci,shaquwa mai sunan shaquwa da yarda da juna ita ta wanzu tsakaninsu,mutanen da suka sansu daga baya da yawansu sun dauka 'yan uwane na qut da qut,tunda ba zaka kallesu kace mahaifiyarsu daya ba saboda bambancin harshe da siffa.

Shi alhj yusuf fari ne tas har yellow yake,sumarsa a kwance take kamar ta larabawa,hakanan harshensa ya dan karye wanda dole idan yana hausa ka fuskanci ba tsantsar bahaushe bane,yayin da alhj bukar ya kasance wankan tarwada,fuskarsa na dauke da tsagu qwaya daya daga hancinsa zuwa goshinsa irin na bare bari,shima alhj dalhatu baqine kamar yadda akasan ainihin kalar fatar bahaushe na usuli.

A lokacin daga bukar har dalhatu babu wanda yayi aure a tsakaninsu sabanin yusuf da yake da aure a lokacin har matarsa ma na dauke da juna biyu wanda take 'yar garinsu ce yarensu kuma daya.

Yau da gobe sai kasuwancinsu dukka yayi qarfi cikin kano,hakanne ya sanya tilas alhj yusuf ya dauko matarsa fatimatou suka dawo nijeria kuma cikin garin kanon tunda shi yafi alhj bukar nisa,alhj dalhatu yaso ya samu gida nan kusa da shi saidai hakan bata samu ba kasancewar yawancin cikin gari a cike yake,babu wani fili da zaka iya siya,saidai kasai gida ka rushe idan kana so kayi irin ginin da kake so,to ko samun gidan ma aiki ne don yawanci basa yarda su siyar din,ba don sansu ba ya samu gida cikin unguwar sharda mai kyau da girma ya ajjiye fatima a ciki.

Basu cika shekara a nijeria ba fatima ta haihu ta samu yaro namiji,santalelen yaro kuwa wanda ya kwashe kamannin fulanin buzaye da kuma kakarsa rahinatu wadda ta fito cikin jinsin larabawa,jajir da shi suma har goshi,fafin irin murnar da alhj dalhatu da bukar suka nuna bata baki ne,kusan sunfi ma uban dan doki da murna.

Sosai yusuf ya rufe idonsa shi da mai dakinsa fatima suka dinga yi musu gori don suji haushi suyi aure suma,don tace ta gaji itama tana da buqatar qawaye(wato matan da zasu aura din kenan)dariya suka dinga yi suna fadin su sha kuruminsu sun kusa ai.

Allah bai nufi auren nasu ba sai bayan shekara biyar da haihuwar RAYYAN wanda yaci sunan mahaifin kakansa,kusan tsiran wata guda ne tsakanin auren dalhatu da bukar,dalhatu ya auri rabi'atu bukar ya auri fanna,duk da a maiduguri akayi bikin hakan bai hanasu zuwa ba dukkansu.

Sai da suka shekara bibbiyu sannan sukayi haihuwar fari,rabi'atu ta samu UMMA RUMANA fanna ta samu RAIHANA,shekarar rumana hudu rabi'ah ta kuma haifa ,yusuf suna kiransa khalifa da abubukar(bukar) suna ce masa amir,fanna ma ta sake haihuwa ta haifi diya mace wadda zainaba,fatima ce tun daga kan rayyan haihuwar bata kuma tsaya mata ba,ta haihu sau hudu maza biyu mata biyu amma dukkansu mutuwa suke,tun tana damuwa har ta miqa lamarinta ga Allah,hakanne ya sanya ta janye umma rumana wanda ya kasance duka weekend din duniyaa gidan takeyi,bata komawa gida sai ran monday,idan aka daukota daga makaranta sai a wuce gida da ita sai kuma wani qarshen makon.

Zumunci ne sosai tsakaninsu har ma da matansu da 'ya'yan nasu,musamman gidan alhj dalhatu da gidan alhj yusuf,kasancewar alhj bukhar sunyi nisa saidai saqon gaisuwa da waya a tsakaninsu.

Sannu a hankali arziqinsu ke dada yalwata wanda hakan ya sanya tilas alhj bukar ya dawo kano shima kusa da 'yan uwansa a lokacin raihana da umma rumana na da shekara takwas a duniya rayyan na da sha biyar,unguwarsu daya da alhj yusuf saidai akwai 'yar tazara tsakaninsu.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*watpadd:huguma*

© *haske writers asso*💡
(Home of expert and perfect writers)

*Manzan Allah S a w yace:duk wanda yayi salati a gareni sau goma da safe sau goma da yamma cetona zai riskeshi ranar qiyama*

_duba sahihut targib wat tarhib mujalladi na daya shafi na 372_
____________________________

*Babi na uku*

Mai glass shine sunan da rumana ta fara kiran raihana da shi da fari farkon tarewarsu,kasancewar da glass din raihana take zuwa makaranta saboda lalurar rashin ganin abun da ke can nesa da kyau da take fama da shi.

Lokaci lokaci raihanan na zuwa gidansu rumanan,musamman idan abbansu ya kaisu ko kuma mamansu zata je,hakanne yasa suka dan saba da rumanan duk da rashin son magana irin na raihana,yarinyace da bata qiriniya ko rashin ji ko kadan,hakanan surutu bai dameta ba,iyakacinta da abu kallo sai ko murmushi,sabanin rumana dake da surutu rawar kai tsokana da rashin ji,hakan ya sanya tun a lokacin hajiya yaaya kakarsu rumanan wadda ta haifi alhj dalhatu tasu tafi zuwa daya da raihana,don lokaci lokaci itama suna zuwa mata

Sam bata damu da zuwa gidan alhj yusuf ba duk da cewa suna kusa,hakanan ko rumana taje weekend bata damu da zuwa gidan ba,haj fatimatou takan alaqanta hakan da ko don bata da 'yar budurwa ne sai rayyan kadai dake gabanta.

Yawan zuwan rumana gidan hakan na yiwa rayyan dadi da debe masa kewa,don lokacin ne yake samun abokin hira da wasa kasancewarsa ba mai son yawace yawace ba ya sanya bai da wani aboki,hakanan yanayin unguwar tasu ma bai wani jama'a ta cika ba,jama'ar da take da ita kuwa kowa na qule cikin gidansa ahi da nasa iyalin.

Wannan shine musabbabin shaquwa mai qarfi da ta shiga tsakanin rayyan da rumanan,wanda har takai ta kawo odan bata zoba shi yana zuwa gidansu yayi weekend dinsa hankalinsa kwance kasancewar gidansu rumanan akwai yara ba kamar nasu gidan ba da yake shi daya qwal

*dukkan mai rai mamaci ne*

Wannan haka yake kuwa,domin alhj bukar bai wuce shekara daya da zuwa dawowa garin kano ba Allah ua yi masa rasuwa,a lokacin duka duka shekarun raihana tara a duniya.

Hakan ya faru ne sakamakon hadarin mota da ya samu daga hanyar mai duguri zuwa kano,wanda dama yakan je garin nasu lokaci lokaci yaga dangi kuma ya karbo huluna gurin mutunen da yake siya a gurinsu,basu kai ga qarasowa ma cikin garin kanon ba lamarin ya afku,wanda sai gawarsu aka qarasa da ita asibitin koyarwa na malam aminu kano.

Mutuwar ba qaramin girgiza zuriyar uku tayi ba baki daya,kada ma mai dakinsa alhj dalhatu da alhj yusuf suji labari,kai kace mahaifansu ne suka rasu,sunyi matuqar gigita,to amma ya aka iya da lamarin ubangiji tilas suka haqura suka rungumi qaddarar ubangiji.

Bayan share makoki ne 'yan uwan fanna sukayi niyyar tafiya da ita amma alhj yusuf da alhj dalhatu suka kafe kai da fata kan cewa a barta a dakinta tayi takaba kamar yadda addinin musulunci yafiso,tunda dai gida na bukar ne mallakinsa ne,sanin irin alaqar da take tsakani suka janye qudurinsu ba haufi suka barta a gidanta tayi takaba,sun barta da 'yan uwa mutum biyu masu tayata zama.

Cikin zaman takabar ta ta qara yadda da jadda da girman abota dake tsakanin wadannan mutane guda uku,don babu wani abu da wani cikinsu zai siya bai hada da gidan bukar ba,ficika basu bari an taba cikin dukiyar bukar din ba da nufin a ciyar da iyalinsa,babu abinda suka rasa bangaren ci sha sutura da buqatun rayuwa na yau da kullum,haka matansu ma kullum suna tafe,banda rashin mai gidan da sukayi babu wani rashi da suka dandana.
Chapter 2 · 0% Book details