Sashe 24
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tayi cikin motar tana jin hira da hayaniyar su zainab din da baaba gana,kanta jingine da makarin kujera tana jin wani bacin rai kadan kadan,tsuwwa wayarta tayi alamun kira ne ya shigo cikin wayar tata,ta daga ta duba sannan daga bisani ta amsa
"Sisi,shine kikayi tafiyarki ki barni ko?"
"Ya zanyi to,inata jiranku shiru baku dawo ba ga lokaci na tafiya" daj shiru rumanan tayi sannan tace
"Sisi ko na bata miki rai ne?,nayi nemanki kan na fita har na gaji ban ganki dole na haqura muka wuce"
Idanunta ta lumshe tana qoqarin tuna me ta gayawa sisinta ne?,a hankali ta saki murmushi wanda har rumanan sai da ta jiyoshi
"Ba wani abu bane ba fa sisi,kada ki samu damuwa 'yar uwa,naga kuna tare da ya rayyan babu damuwa ai ko?"
"Ki dawo yanzu ina son ganinki" taji muryar rayyan maimakon rumana
"Kamar yaya?" Taji tambayar ta subuce a bakinta
"Kamar yadda kika ji" sai kawai ta cire wayar daga kunnenta ta kasheta baki daya don ta fuskanci rayyan so yake ya raina mata hankali
"Ya dai?" Taji baba gana na mata tambayar
"Lafiya lau" ta fada tana yaqe,duk da sanyota da yake cikin hayaniyar sun ta kasa ce musu komai har suka qarasa gurin.
Duk da tarin 'yammatan dake kara kaina a gun da ya qayatu matuqa amma sai ta samu table dake can qurya da dakin taron ta kebe kanta,hakanan take ji rashin sukuni cikin zuciyarta,duk yadda takai ga son sanya walwala cikin fuskarta da zuciyarta abun ya faskara,dole ta dan saki kadan tana maidawa baba gana hirar da yake mata don kada ya tsammaci wani abu ne hakan da takeyi.
Tsawon mintina talatin ana gabatar da abinda ya tarasu a gun,yayin da taci gaba da zama a inda take din ita da baba ganan,daga nan suke hango duka abinda ke faruwa,daga can ta hango rumana na ratsa mutane da teburan dake cike da harabar gun,ido ta zuba mata har ta qaraso inda take zaune,cikin murmushi raihana tace
"Hala yaya rayyan ne ya kawoki ko,irin wannan sauri haka sharp sharp?" Harde hannunta tayi cikin fushin wasa tana daure fuska
"Mu da muka damu dake ai mun biyoki,kije yaya rayyan na kira",kai ta girgiza
"Allah yasa lafiya" hannu ta ware
"Oho,wannan karan kam bazan tare miki ba koda laifi kikayi na gaya miki tunda kika taho kika barni" qaramar dariya raihana ta saki
"To ai ni nasan ban muku laifin komai ba sisi,kije gani nan zuwa yanzun in sha Allah"sai da rumanan ta harereta sannan tayi gaba,dariya raihanan ta bita da ita tana cewa
"afuwa sisi mana,ba haka tsakaninmu".
Hirarsu suka ci gaba da yi da baba gana tamkar ma ta mance da kiran rayyan din,minti kusan goma tsakani ba zato ta tsinci rayyan tsaye gaban table dinsu,sanye yake da qananun kaya t.shirt mai dogon hannu ruwan bula wato dark blue da wandonta,ba qaramin kyau yayi ba,sosai kayan suka haska fatarsa,idanunsa saye da sun glasses mai fadi,yayin da kwantacciyar sumar kansa ta sake yin luf sai sheqi take,ba qaramin daukan idanun 'yammatan dake gurin yayi ba,rayyan din na musamman ne, duk hassadarka dole ka fadi hakan,yanayin qirar da halittar da Allah yayi masa ya sanya yawancin wadanda basu sanshi ba sukanyi tsammani sam baisan wani yare waishi hausa ba,shirun ya faru ne saboda lokacin da ya shigo din gurin ya nutsu ana sauraran jawabi daga bakin abokin ango,domin da dama basu sanshi ba,idanun raihana sun gane mata hakan,sai taji wani abu na taso mata,wanda bata raba dayan biyun kishi ne,saidai kanta takewa kishin ko 'yar uwarta?,wannan ne kuma bata sani ba.
Taku yake irin na cikakkun matasa har ya iso inda suke zaune din,tun dazun ta ganshi amma sai ta dauke kai kamar bata ganshi ba,kallo daya tayi masa taji yayi mata kwarjini,jikinta sai ya mutu laqwas tayi,duk wani kuzari da karsashinta ya fice lokaci guda tamkar wadanda sukaji tsoron ganin rayyan din,fuskarsa a hade ba tare da ya dubi baba gana ba yace da ita
"Wuce muje"ya sanya hannu yana daukar jakarta daje ajjiye saman kujerar shuru tayi ta dan dubi baba gana,ita yake kallo ba tare da yace komai ba,ta sake maida idonta ga rayyan yana tsaye qyam cike da wata iriyar izza da isa,sai ta kasa cewa komai face miqewar ta dubi baba gana
"ina zuwa"
"Ba damuwa" shima ya amsa mata a taqaice.
"Wannan saunan shi ya hanaki zuwa ko kuwa da zan kiraki sama da minti talatin ina jirankin?" A dan rude ta waiwaya tana fata Allah yasa baba gana baiji sunan da rayyan din yayi kiransa da shi ba,tana gaba yana binta a baya,ya wani hade rai yayi kicin kicin,yayin da idanuwa sukayi yawa a kansu,kowannensu dacin rai ya kama shi,shi yana kishin mazan dake gun yayin da ita ke kishin matan.
Ajiyan zuciya ta saki a hankali data fuskanci kamar baba ganan baiji ba
"Ai ya isa ne,ko ka manta dan uwa na ne"
"Ni kuwa nasan hakan,amma kuma baiyi isar da zan kiraki ya tareki ba,kada ki yarda ki sake maimaita irin wannan kuskuren" baki ta murguda kana ta turo shi gaba lokacin da suke ficewa daga hall din
"Ni kike murgudawa baki,kinsan kadan daga aiki na cinyeshi yanzun naga na rashin kunya nan gaba?" Ya fada cikin dinkakkiyar fuska tare da jan tunga ya tsaya yana dubanta bayan ya zare gilashin fuskarsa yana duban nata qwayar idon dake cikin medicated glass dinta,rasa abinda zata ce tayi,ga mari ga tsinka jaka?,kawai ji tayi hawaye na shirin zubo mata
"Ka daina min abinda kake min ya rayyan"
"Sonki ne,kuma bazan daina ba yanzu na fara" ya fada tare da jan gefan mayafinta,tasa hannu ta janye mayafin sannan taci gaba da binsa
"Bakajin kunya ne yaya rayyan?,gani ga rumana,kana son 'yar uwarta ba tare da saninta ba,shin da wanne irin ido kake iya kallonta ko kum......" Shiru tayi saboda ganin sun iso bakin motar,hannu ya sanya ya bude mata gidan baya tare da maida mata da amsa
"Ku mata ku kukasan wannan,mu muna duba abinda yake daidai ne ba abinda ya dace ba" ya fada yana watsa mata wani irin kallo,dole tayi shiru saboda idanun rumana wadda ke zaune gaban motar,a hankali ta sanya jikinta cikin motar sannan ta kwashe qafafunta da sukayi sanyi ta shigar da su suma har lokacin idanunta mai cike da qwalla na kansa wai ko zai duba rauninta ya janyr qudurinsa,saidai ki kadan batasan wano saqo take aikama ruhi da gangar jikinsa ba,wasu abubuwa yake sake gani tattare da ita dake sake tafiyar da shi sosai,yana jin wani irin so mai qarfi na fisgarsa.
*mrs muhammad ce*
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Daga abdullahi dan abbas R.A.M yace:manzan Allah S A W ya la'anci namiji mai kamantuwa da mata (dan daudu),da mace mai kamantuwa da maza,kuma yace"ku fitar da su daga gidajenku"*
_bukhari ne ya rawaito_
_______________________
*Babi na ashirin da daya*
Cikin wata iriyar kasala ya maida murfin motar ya rufe kana ya zagaya mazauninshi ya zauna
"Ina ga sisi dai kora da hali kawai kike mana mubar muku garinku ko?"
Rumana ta fada tana danna wayarta,wani abu ya tsirgawa raihana,sai taji wani iri,irin abunda bai taba shiga tsakaninta da rumana ba wato sabanin fahimta,Allah sarki,wannan shi ake kira da rashin sani wanda yafi dare duhu,duka abinda take yi tana yinsa don rumanan ba tare da ita rumanan ta sani ba,bata san cewa qoshi ta samu kuma take kwanan yunwa ba duk don saboda farincikin ta,tana gujewa tarayyarsu su uku ne lokaci guda kuma a tare don gudun faruwar wani al'amari,rayyan nason haifar musu da jirkicewar kyakkyawar DANGANTAKAR dake tsakaninsu kenan?,murya a sanyaye raihana tace
"Haba sisi,bai kamata ki fadi haka ba,kinfi kowa sanin wace raihana ko?"
"Afuwa sisi na,nima ba wani abu nake nufi ba tsokana ce dai kawai irin ta sisinki 'yar tsalle" inji rumana ta fada tana dariya,itama dariyar tayi duk da batakai har cikin zuciyarta ba.
Kiran amir da ya shigo wayarta shi ya katse sauran maganar tasu,tana sane yau ta sauya wani salo na daban saboda rayyan din,ta wani saki jiki tare da narkewa ta dinga zuba masa hira mai dadi,ta kuwa qona rayyan din sosai,zuciyar 'yan maza ta motsa,ya dinga fidda numfashi mai zafi shi kadai,wani kishi mai zafi ya dinga diga tsakiyar zuciyarsa,yana jin cewa ya kamata ya kawo qarshen alaqar dake tsakaninsu don ya samu damar cimma burinsa,yayin da ta sake dilmiyar da amir cikin tafkin qaunarta,ya sake susucewa don bai taba samun haka daga gareta ba,a nan yake gaya mata antynsa(matar babansa da yake a hannunta yake)tana son ya kawota ta ganta su gaisa,babu musu ta sanar masa cewa tana dawowa daga maiduguri zata sanar masa ya sanya musu rana,sai da taga rayyan din na parking qofar wani babban super market alamar nan suka zo sannan tayi sallama da shi,ta kashe wayar ta maida cikin jaka.
Shi da rumana na gaba yayin da tabi bayansu har suka shiga ciki,bangaren kayan maza yayi yace su zabi duk abinda suke so kafin ya kammala,rumana ta narke tace sai ta bishi ta tayashi zabi,bai ce mata komai ba sabida zafi da ranshi keyi yayi gaba ta bishi bayan ta juyo tace da raihana ta zaba musu abinda taga ya dace da su ta bita da to,kujera ta samu tayi zamanta tana kalle kallenta,bata da niyyar daukar kada tsinke ne.
Kusan minti talatin suka kwashe sannan taga bullowarsu,turus rumana tayi
"A'ah,ya na ganki a zaune sisi?,banga alamun kin dauka mana komai ba fa?" Rayyan dauke kansa yayi tare da yin gaba abinsa kamar bai gane meke faruwa ba,kama hannunta rumana tayi suka fara kewaye gurin.
Laffaya ta daukar musu masu bala'in kyau mai tsada ta barebarin asali kala bibbiyu sai jaka da plate mahadin lafayar din takalmi duk iri daya,ita kanta raihana kayan sun burgeta don ta sani sisinta dama ba daga baya ba wajen iya zaban abu mai kyau dan yayi,a gun biyan kudi suka taddashi aka hada da nasu aka lissafa ya biya,a kan hanya ya tsaya wani restaurant mai kyau ya siyi take away sannan suka isa gida.