Sashe 47
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taku ta sake yi ta qaraso gabanta
"Ruma,aure dai sai da yarda ta ko?,to bana son mijinki bana yi,indai har kina qaunata ki rufe babin wannan maganar"
"Magana kam yanzu babinta ya bude,tunda sadakinki ma na hannun abba" gabanta ne ya wani irin bugawa kamar zai tarwatse data tuna da hakan,ta zaro idonta cikin takaici tana fadin
"Wallahi bana son rumana bana so,alqawari nayi kuma ba zaki karya min shi ba,bana son rayyan bana sonsa rumana don me zakiyi min haka"
"Kamar yadda nima bana sonki ba" suka ji an ambata daga bayansu,rayyan ne yake takowa cikin falon hannayensa soke a aljihunsa,yayin da fuskarsa ta hada ja da alama ya dade yana sauraren abinda ke wakana tsakaninsu,gun rumana ya nufa wadda ke tsaye tana zubar da qwalla jin yadda raihanan ke qaryata kanta tana furta kalaman qiyayya baro baro ga mijinta duk don saboda ita,kamata yayi ya riqe gam bayan ya zuba mata ido
"Kina shirin hada abinda bazaya yiwu ba,na dade da gaya miki cewa na barta har abada,don me zaki tsaya ana gasa miki magana bayan dumbin halaccin da kike son mata?," a hasale raihanan ta dubeshi hawaye itama na fita a idanunta
"Dadin abun bani na buqaci amin halacci ba,ni din ma ba sonka nake ba rayyan,bana qaunarka,ban taba tsanar wani abu a duniya kamar kai ba,kuma wallahi aurenka har abada bada ni ba,saidai wata raihanan...." Sake matsowa tayi gaba rumana tana fatar gaya mata magana koda daya ce wadda zata tunzurata ta rusa abinda ta gina
"Kija wa mijinki kunne saboda da da yanzu ba daya bane,ni a yanzu nafi qarfinsa gwara ki kama mijinki ki riqe,bazanyi zaman kishi da 'yar uwata ba jinina....." Kasa ci gaba da maganar tayi duk da yadda taso ta tunzura rumanan,juyawa tayi a fusace zata fice rayyan din ya fincikota,tayi taga taga kamar zata fadi har sai data dafe kujera,hannayensa ya daga da niyyar saukesu kan fuskarta yaji an riqe hannun nasa,rumana ce tsaye gabansu tana dubansu
"Kada ka taba min sisi,na gode da abinda kuka yimin,na gode qwarai da gaske,wannan shi ya tabbatar min da cewa baku sona,wannan shi ya nunan cewa nice baku buqata a rayuwarku,ni kuke so ma fice daga rayuwarku duk kuwa da yadda kuke da muhimmanci a gareni baki dayanku...to ku sani,wallahi gaba dayanku zaku rasani" ta juya idanunta cikin na rayyan
"Ka tabbatarwa kanka cewa daga lokacin da ka bijirewa auren raihana to ka tanadi takardar ta saki....haka kema" ta fadi tana dubanta
"Bazan zauna cikin gidan nan ba daga lokacin da kika qi wannan auren" sai ta juya ta haye sama ba tare data sake waiwayar kowa cikinsu ba,ta tabbatar hakan da take shine mafita da maslaha a rayuwarsu baki daya.
Sai data qule ya janye idanunsa ya dora su kan raihana da tsayuwa ta gagareta sai hannun kujerar ta samu ta zauna dafe da kanta wanda take jin kamar zai rabe biyu,yatsunsa biyu ya hada ya murza wadanda suka bada sautin d'as d'as kana ya nuna ta
"Kiyi addu'ar kada wani abu ya samu matata" a zafafe ta kalleshi
"Kayi addu'a kaima kada wani abu ya samu 'yar uwata wallahi,idan kaine ma ka gayawa rumana batun ka sani wallahi Allah burinka bazai taba cika ba" ta miqe jiri na dibarta ta fice daga falon,da gaggawa ya haura saman ya isketa a bedroom dinsu
. tausayinsu ne fal cikin zuciyarta,ta tabbatar da cewa kowannansu na qoqarin nuna mata kaara ne,kowannansu na qoqarin bata farinciki ne alhalin su suke sa buqatar hakan fiye da ita basu san cewa wannan ce kadai hanyar da zata samawa rayuwarsu nutsuwa kwanciyar hankali da farinciki ba duka su ukun,wadan ne irin 'yan uwa Allah ya azurta ta da su haka?,masu zuciyar fifita buqatar dan uwansu akan tasu,tabbas banu shakka tarbiyya ce tsantsa da suka samu,aka rainesu kuma kan halak da tsoron Allah,aka horesu da kyawawan halaye da aikata ayyuka nagartattu,madalla da uwa irin ummu mai fidda iri mai kyau,madalla da iyaye irin abba bukar abba yusuf da daddy dalhatu.
A qafa ta dinga tafiya kamar wata zautacciya,tafiya tayi mai nisa kafin wani mai adaidaita sahu ya sha gabanta yana tambayarta ina zata,sai data hau ta iya gaya masa inda zai kaita.
Bataci karo da kowa ba balle ya tsaidata,dakinta ta nufa bayan ta saka muqulli ta rufe ta fada kan gado,zuciyarta ta dade tana mata suya da radadi kafin kuka ya qwace mata,kuka ta dinga yi na haqiqa,tausayi da qaunar 'yar uwarta na sake kamata,haushin rayyan ya mamayeta,tana kyautata zaton saga gareshi ta samu labari,idan bashi bane ma waye?,ta tabbatar cewa duk duniya daga ita sai shi suka san da maganar,ta jima tana kuka har sai data gaji da kanta.
Ganin tara har tayi ya sanyata miqewa tana ambatar hasbunallahu wa ni'imal wakeel tuna cewa ko sallar magariba bata yi ba balle isha'i,ko cikin sallar ma kuka ne yaci qarfinta,yayin da tunani yaci galaba akanta har sai data sauya wata sallar,rumana ta qulleta tako ina,zance ya riga yaje ga na sama da su tuni,ta yaya zata iya kallon idanun abba bare ummu tace bata son dansu,mutanen da haihuwarta ne kadai basuyi a rayuwa ba?,bama wannan ba,da ace ita ce silar fitowar sisinta daga gidan aurenta gwara Allah ya dauki ranta kafin lokacin,a yadda rumanan ta hasala itama ta sani cewa tsaf zata bijirewa zaman gidan nata,taurin kanta da kafiyarta yafi gaban hakan,tunanin ta kaf ya qare kan yadda zata balle wannan daurin na rumana.
Kasa tashi tayi daga kan abun sallarta,tunanin yadda ta baro sisin nata ya cikata,bugun qofarta da akeyi ne ya sanya ta dawowa hayyacinta,ta miqe a hankali ta zare muqullin,lantana ce
"Dama ummu ce tace na dubaki ko har yanzu baki dawo ba"
"Na dawo lantana,gajiya ce ta sanyani ka dan kwanta"
"To dama abinci tace na gaya miki yana kan teburi an shirya" don kauda zargi sai tace
"Ok,samu plate kawai ki zuba ki kawon daki daga na gama ci bacci zanyi yau da wuri" ita kanta tasan ta fada ne kawai,cikin mintina qalilan lantana ta kawo mata,ta karba ta turashi can gefe ta koma saman abun sallah.
Har dare ya fara tana zaune gu daya,a hankali ta saki ajiyar zuciya sanda wani tunani ya fado mata,a tunaninta tana zaton duk yadda 'yan uwan rumana zasu sota ai bai kai yadda zasu so rumana ba tunda jininsu ce ita daga tsatsonsu ta fito,take ta yanke ma ranta gobe zata je gun hajiya babba ta tabbata cewa komai zaya zo qarshe,wannan tunanin shi ya dan kwantar mata da hankali har bacci ya samu nasarar saceta
.
Ta jima zaune gaban hajiya babban tana sharar hawaye bayan ta gama fede mata abinda ke tafe da ita,tamkar hajiyan ba zata ce komai ba tana ci gaba da goga goronta a jikin magogi,sai data tara shi turmus sannan ta daga kai ta dubi raihanan
"Wai nikam azumi saura kwana nawa ne?" Cike da mamakin tambayar wadda take ganin bata da alaqa da maganar data zo mata da ita tace tana goge qwallar fuskarta
"Saura wata biyu"
"Sati takwas kenan?"
"Eh" ta fada tana gyada kai
"Masha Allahu,to kije ki ci gaba da lissafi,sune kwanakin da suka rage a daura aurenki,in sha Allah a dakin rayyanu zakiyi azumi" a razane take dubanta,waau sabbin hawayen suka fara sintiri
"Amma hajiya yanzu fa na......."
"Kinga dakata" hajiyan ta tsaidata fuskarta a murtuke
"Wato kinzo kin gayan ne a matsayina na dangin rumana mu hadu mu tayata kishi ko?,to ba haka nake ba,ba zama muka zo duniya ba,ibada ce ta kawomu,bari kiji na baki wani gajeran labari" hajiyan ta fada rana gyara zamanra tare sa tattare goronta guri guda
"Ni da kike gani na nida sahura(tana nufin hajiya qarama)maqoftan juna ne,baban su dalhatu ya hadamu ya aura 'ya'yan abokai ne kamar yadda kuke,marabar kawai ba tare aka rainemu ba,tunda muke da ita bamu taba nunawa juna yatsa ba,saidai sabani na tsakanin harshe da haqori shi din ma ba mai tsanani ba,duk sanda suka samu sabani ita da baban su dalhatu ni nake zuwa na dawo da ita,nike biko ko bai yarda ba,idan ma yace bai yarda ba gidan su nake binta muyi zamanmu,randa zai dawo da ita ya dawo damu tare(wannan a gaske ya faru),saboda haka indai wannan maganar zamuyi da ke tashi kije" baki ta sake budewa zatayi magana kuka yaci qarfinta,hanya hajiyan ta nuna mata
"Kinga,tashi ki tafi,yau ko hirar tsiya bazamuyi dake na bare ta arziqi,tashi ki bani guri,kada Allah yasa ki haqura,ku jimin ja'iran yara,kun maida kanku wasu sakarkarun qarfi da yaji" tana ji tana gani hajiyar ta korata,mantawa tayi shaf cewa kuka ta kawo gidan mutuwa,hajiyan tun can dama ita ta fara sha'awar hadata da rayyan din.
Cikin kwanakin baki daya ji take duniya ta mata daurin huhun goro,duk wata walwala da nutsuwarta ta kau,tana daki kwance ko yaushe,wani lokaci kuka wani lokaci tunani,makaranta ma tuni ta ajjiyeta gefe,abun mamaki ummu ma babu abinda tace da ita,batasan hajiya ce ta kirata tasa mata takara ba itama,abinda ta fuskanta shine da gaske ne fa,shirye shirye take gani ana yi wanda babu ko tantama suka fi kama da na biki,sai rumana tazo gidan bata sani ba sai ta tafi lantana ta gaya mata,duk da cewa dukkansu suna cikin ran juna,kowa tausayin dan uwansa yake.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_______________________
*Manzan Allah S A W yace "haqiqa Allah madaukakin sarki tsarkakakkene,kuma baya karba sai mai tsarki"*
_______________________
*Babi na talatin da hudu*
Idanunta qyar kan mukhtar,ta zaqu taji me zaice?,meke da akwai
"Bana zaton duk duniya akwai wanda ya kaini qaunar ya rayyan,hakanan babu wanda zai kai ni son ya samu lafiya,maganar ma idan ina sonshi bai taso ba mukhtar,ka gayan kai tsaye meke damun ya rayyan dina".
Kai yake girgizawa,a nutse ya fara bayyana mata duk wani abu da ya sani dake tsakanin rayyan da raihanan,tun idanunta na bude tana saurarenshi har ta lumshe ido tana ci gaba da sauraren nasa,kafin ya kammala tuni hawaye ya jiqe idanunta.