Sashe 1
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*watpadd:safiyya huguma*
© *haske writers asso*💡
(Home of expert and perfect writers)
____________________________
*_BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM_*
*_dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,tsira da aminci su sake tabbata ga shugaban halitta annabi Muhammad S A W_*
*_ina mai farincikin sake haduwa da masoyan rubutu na,sannan ina roqon Allah s w a ya sanya dukkan abinda zan rubuta ya zamo mai amfani mai amfanarwa cikin wannan sabon rubutu nawa_*
*_saidai wannan karon masu karatu sai kunyi min afuwa ba kullum ne ranakun da zan rinqa post ba,ranakun posting sune kamar haka in sha Allahu_*
*lahadi*
*talata*
*alhamis da juma'a*
*Babi na daya*
Tun daga cikin kitchen take iya jiyo muryarta cikin ihun kuka tana dosowa tsakar gidan,da sauri ta ajjiye wuqar hannunta ta fito daga kitchen din da nufin taryarsu tun kafin su su iso mata.
Rayyan ne akan gaba bayansa sabe da school bag dinsa,hannunshi daya riqe da tata school bag din,yayin da daya hannun nashi kuma yake riqe da hannun rumana dake digar jini,Raihana ce ke biye da su a baya itama goye da tata jakar idanunta jage jage da hawaye wanda har ya jiqa medicated glass din dake kan fuskarta.
Da sauri ummu ta qarasa ta karbi hannun rumana dake cikin na rayyan cike da fargaba take tambayar rayyan din wanda idanunshi suka kada sukayi jawur tamkar wanda aka zazzabgawa mari"garin yaya haka?,dame ta yanke?"ummu ta tambayeshi tana qoqarin tsaida jinin.
Daga kanshi yayi ya zabgawa raihana harara wanda jikinta yayi laqwas ta lafe a bayan ummu"raihana mana ummu,wai qawarta ce ta bata ajiyar reza ita kuma rumana ta gani ta karba a gunta zata fiqe pencil,garin fiqewar ta yanke hannu"
"Ashsha,ai na hanaku amfani da reza ko?,tunda dukanku kuna da sharpner"
"Ai tana sane wawiyar yarinya data karbi ajiyar kuma har ta bada wai aro" ya fada yana sake hararta duk da ta buya,ji yake kamar ya janyo raihana ya sake mammarinta kamar yadda yayi dazun.
"To ya isa,rumana kukan ya isa haka mana,dadina dake raaki,kai rayyan maza shiga bedroom dina ka dauko first aid boxs dinku"da sauri ya sabule jakar makarantar tasa ya shige parlour inda daga nan zai sadashi da dakin gadon.
Cikin 'yan daqiqu ya dawo hannunshi dauke da akwatin ya miqawa ummu,ta sanya ruwa ta fara wanke jinin kafin ta saka spirit ta soma wanke mata,aifa rumana an samu abunyi,bare baki tayi sosai ta dinga sharbar kukanta yayin da rayyan da raihana baki daya suka rasa sukuni suka dinga zuba mata sannu tamkar su maido ciwon jikinsu.
Raihana ce ta gaza daurewa tace cikin qwalla" ummu da zafi don Allah ki mata a hankali",da sauri rayyan da ya harde hannayensa a qirji yana kallonsu idanunsa sun kada ya sake zuba mata harara"yi mana shiru,duk bake kika jawo mata ba","rayyan ya isheni haka nan"ummun ta tsawata masa,suna tsayen ta kammala gyara matan rayyan ya janye hannunta zuwa falo raihana ta kwashi jakankunansu tabi bayansu,ummun ta bisu da kallo,idan da sabo tuni ta saba,irin wannan damuwa da sukayi da junansu,cikinsu babu wanda keson wani abu ya samu dan uwanshi kada ma rayyan da rumana suji labari,hakan ya sanya cikin makaranta ko unguwa wasu ke musu laqabi da AMINAN JUNA.
Ciken tray daya ta shirya musu abincin,don ta sani lokuta irin wadan nan tare suke cin abinci,musamman yau da aka jangwale rumanan sarkin raki.
kan kujera kuwa ta tadda rumana a lafe kamar wadda ke ciwon jiki,yayin da rayyan ke gefanta hannayensa dauke da papers wanda da alama na neco da suke zanawa ne yake sake dubawa,ajjiye tray din tayi wanda ke dauke da shinkafa da miya,gefe kuwa hadin salad ne
"A sauko aci abinci maza kada lokacin islamiya yayi"cewar ummu,ai kuwa sai rumanan ta sake lafewa tana ahirin zubda wasu sabbin qwallan,sarai ummu ta fahimci me take nufi tunda tai hakan,ko dama can kullum da daru rumanan ke tafiya makarantar walau islamiyya ko boko,sauqinta daya rayyan da take shakka,duk da sabon dake tsakaninsu hakan baisa ta rainashi ba.
Tana shirin neman raihana sai gata ta fito sanye da unifoarm din islamiyar tasu baqar doguwar riga da farin hijabi,yarinyar na da nutsuwa da son makaranta,sau tari takan fahimci abinda ya kamata tun kafin a furta duk da qarancin shekarun nata da basu shige tara da 'yan watanni ba
"Oya,sauko muci abinci"rayyan ya fada yana duban rumana,ta kyebe baki don babu damar yin musu haka ta janyo jiki ta sauko qasa inda ta tanqwashe qafarta kamar yadda duk sukayi,hannunta ta kalli kana ta kalli rayyan,shima dubanta yayi ba tare da yace komai ba ya soma diba yana bata a baki,ya juya zai dauki ruwa ya lura raihanan ma ba wani cin kirki tajewa abincin nata ba,sai yaji tausayinta ya kamashi da ya tuna marin da ya mata dazu,hannu yasa ya karbe cokalin hannunta ya hadasu duk su biyun ya dinga basu,ummu dake gefe wadda ta idar da sallar azahar tana kallonsu fuskarta qunshe da murmushi,zuciyarta cike fal da farincikin yadda rayyan din ke kulawa da qannen nasa.
Sai da suka qoshi su duka kana ya tasa rumana a gaba ta shirya fuskarnan babu digon annuri don kada ta kawo wargin cewa ba zata je ba.
Hakan bai sanyata tayi shiru ba lokacin da taga ya sanyasu a gaba suna qoqarin ficewa a gidan ba tare da shi ya sanya nashi unifoarm din ba,fuska a narke tace"ya rayyan....yauma mu kadai zamu je kai ba zaka je ba?"dariya ce taso kubce masa ya dan dake"amma da karatu ne wannan rumana yaci kin dade da haddaceshi,wata na nawa da yin sauka aka sallamemu?,ranar saukan ba ke na bawa ajiyar zayyanata ba?"shiru tayi ba tare da tace komai ba tana mai ci gaba da son zubda qwalla,"kinayin kuka ni da raihana ba ruwanmu da ke,ke bakyason kema wataran ace kinyi saukar kamar ni?","inaso mana ya rayyan" xto dole ki dage da zuwa makaranta kinji ko?"
"To amma ya rayyan idamukayi sauka shikenan mun daina zuwa ko?"
"Qwarai ma kuwa my angel"da yake wani lokaci haka yake kiranta,murna ta soma yi jin ance sun daina zuwa da sunyi sauka harda rawa da yake ba baya ba wajen son rawa,shi da raihana na gefe na kallonta raihana nata dariya,da haka ya kada kansu suka fice yana jansu da labarai masu dadi dasa dariya don su kuma sakewa har ya kaisu qofar makarantar dake bayan layinsu ya juya ya komo gidan don yayi wanka
*mrs Muhammad ce*
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*watpadd:huguma*
© *haske writers asso*💡
(Home of expert and perfect writers)
*_An karbo daga uwar mumunai ummu abdullahi wato nana Aisha R.A tana cewa:Manzan Allah S a w yace "haqiqa dukkan ayyuka basa yiwuwa sai da niyya,kuma kowane mutum akwai abinda ya niyyata"(ma'ana ladan aikinka da sakamakon da zaka samu ya ta'allaqa da irin niyyar dake zuciyarka akan aikinka,irin niyyarka irin sakamakonka agun ubangiji)*
_ruwayar bukhari_
______________________
*babi na biyu*
Hikimar ubangiji ce haduwar jini qauna da shaquwa tsakanin wane da wane,yakan sanya irin wannan jituwar da qaunar juna tsakanin bayinsa,hakan itace ta kasance tsakanin wadan nan bayi nasa guda uku wadanda suka fito daga mabanbantan yare har ma da qabila,wanda daya daga cikinsu ma suka samu banbancin qasar haihuwa a tsakaninsu
*Alhj yusufa adamu*
Haifaffen jamhuriyar nijer,cikin garin DIFFA,garine dake da qarancin jama'a cikin duka qasar ta nijer,tattalin arziqin yankin ya ta'allaqa ne kan noma da kiwo,mazauna garin sun hada da hausawa,fulani da larabawa.
alhj yusufa na daga cikin jinsin fulani wadanda a nan mukafi kira da sadakar yalla,duk da yake ruwa biyu ne shi,saboda asali mahaifiyarsa na daya daga cikin larabawan dake zaune cikin yankin wanda auratayya ta hadata da adamu mahaifin alhj yusuf.
Bai fuskanci wani qalubale wajen samun auren rahinatu ba saboda suna da wani yanki na sarautar garin diffa,mahaifin adamu a lokacin shine wazirin sarkin garin na diffa wanda ko bayan rasuwarshi sarautar bata bar gidansu ba adamu dinne yaci gaba da jan ragamar,kasancewarsa d'a na fari kuma babba a gurin mahaifinsu.
Yusuf tun yana qaraminsa zuciyarsa da tunaninsa sunfi ta'allaqa ga harkar siye da siyarwa wato kasuwanci,wanda hakan shi ya zama sanadiyyar haduwar jininsu da qanin mahaifinsa muhammadou wanda ke kasuwancin dabino da cukui tsakanin nijeria da niger.
Yadda ya lura da hazaqar yusuf da qulafucinsa na son kasuwanci yasa ya fara daukarsa rakiya zuwa nijeria tun shekarun yusuf din basu taka kara sun karya ba,cikin qanqanin lokaci sai ga yusuf din ya zama cikakke kuma gogaggen dan kasuwa tsakanin nijeria da nijer.
Tun zuwan yusuf na farko qasar nijeria ta burgeshi,yanayin garin al'ummarsa wayewarsu da kuma mu'amalarsu da jama'a,musamman da ya soma shiga garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa,wanda da iyakacinsu sokoto katsina,harkarsa a kano sai tafi garawa ta kuma fi bada armashi kasancewarta cibiyar hada hadar kasuwanci,hakan ya sanya bayan cukui da dabino sai yake hadawa da mazarqwaila da sauran abubuwa da mu bamu da su.
A lokacin cikin kasuwar kwari suke sauka inda anan ya hadu da alhj *dalhatu attahir* wanda yake da makekiyar rumfa,nan cikin rumfar tasa yake ajjiye kayansa idan yazo kafin ya rarrabawa 'yan kasuwa da masu sara.