Sashe 9
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To kin ga gidan nan matar gidan ma ba mazauniya ba ce. Aiki take fita daga safe har yamma, sannan kuma ba ta ƴaƴa. Wanki kuwa suna da mai yi musu har da goga idan sun ga dama ma za su iya yin wata guda cur ba tare da an yi musu wankin ba don suna da wadatar suturar. Don haka ki tashi ki bar ƙofan gidan nan tun kafin na sauya miki halittan fuskanki".
Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah a taimaka mini wallahi ina tsananin buƙatar aikin ne, ka ba ni dama na shiga na ga matar gidan wataƙila ba za a rasa wani aikin da za a maƙala ni a gurbin ba....". Kafin na rufe bakina na ji an ɗauke ni da wani gigitaccen mari sai da na zame na yi zaman dirshan a ƙasa sakamakon zafin da ya ratsa har cikin kwanyanta.
"Yau na ga masifa ni Ahmadu. Za ki tashi ki bar nan wajen ko sai na shiga ciki na sincu miki karnuka na fito da su sun yayyaga ki". Yana rufe bakinsa na yi zumbur na yi miƙe jikina har yana rawa na bar wajen ban ƙara waiwayowa ba don daga yanayin furucinsa na tabbatar da cewar zai iya aikata duk abin da ya furta.
Sai da na yi nisa na nema wani dakali na zauna ina mayar da numfashi. Na zabga tagumi da hannunwa bibbiyu tare da faɗa wa cikin kogin tunani, na daɗe zaune a wajen har rana ya iso inda nake ya soma duka na amma hakan bai sa na gusa daga wajen ba, sai da na ji jikina ya soma fitar da zuffa na gumi kafin na tashi na soma tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da yake wajen ya miƙe ɗoɗar, ina tafiya ina haɗa hanya tamkar ƴar maye ban yi aune ba na ji wani abu ya doke ni har sai da na faɗi a kan titin kaina ya bugu da ƙasa.
Na runtse idanuna cikin wani irin mawuyacin hali na runtse idanuna. Dishi-dishi idanuna suke gano mini wata mace cikin shiga na alfarma a tsaya a kaina tana ta jeranta mini sannunku wani na bin wani sai dai na kasa amsa mata.Ta taimaka mini na tashi na zauna.
"Baiwar Allah sannu. Ki na ji na kuwa?". Na yi ƙarfin halin gyaɗa kaina da hakan ya ba ta damar cewa"tashi mu je asibiti a duba ki". Take na watsake na buɗe idanuna tar na ce"a'a lafiyana ƙalau ba sai mun je wani asibiti ba". Na ƙare zancen ina ƙoƙarin tashi tsaye ta riƙe ni"ki koma ki zauna kin bugu fa".
"Ban fa ji wani rauni ba zan iya tafiya. Don Allah ki bar ni na tafi ina da abin da ya fi zuwa asibitin nan muhimmanci". Na ƙare zancen cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan ƙalbina.
Na ɓaɓɓare hannunta daga jikina na soma tafiyata ko sauraron abin da take faɗa ban yi ba. Na ɗan yi nisa da tafiyan ina jan ƙafata da ƙyar saboda buguwan da na yi a gwiwan ƙafan. Na ji ana danna horn a bayana na matsa na yi gefe motan ya sha gabana, aka buɗe aka fito matar da ta buge ni ne ta fito, ina ganin ita ce na ƙara sauri cikin jan ƙafa zan bar wajen ta sha gabana tare da cafko hannuna ta riƙe tamau.
"Baiwar Allah me yasa kike wasa da lafiyarki ne? Shin ba ki lura da yadda kike jan ƙafarki ba ne? Me yasa ba ki bari mu je asibiti a duba lafiyarki ba ko so kike yi wani abun ya same ki ina zaman zamana bakina alaikum ki ja min bala'i".
"In dai don ta ni ne babu wani wanda zai zo ya same ki da batuna balle har a neme ki idan wani abu ya same ni sanadin hakan, don haka ki kwantar da hankali ba ni da kowa a garin nan". Ta yi sakeke tana kallo na ganin yadda na ƙare.
"Ko ma mene ne ki bar ni na sauƙe wannan nauyin da ya rataya a wuyana, na kai ki asibiti a duba lafiyarki sannan na kai ki har gida".
"Idan kika yi hakan za ki bar ni na yi tafiyata?". Ta gyaÉ—a mini kanta cikin tabbatar mini da abin da ta furta ta ce"in sha Allah".
"Shikenan". Na furta a taƙaice ina juya wa na shiga motar ita ta zagayo ta shiga tare da figi motar muka bar wajen tun da muka fara tafiyar ban ce da ita uffan ba har muka isa asibiti. Ta lashe motar muka fito muka shiga ciki aka duba ni tare da yi mini dressing ɗin inda na kurkurje a gwiwana aka ba n wasu magunguna muka fito, sai da muka shiga cikin motar kana ta kallo ni ta furta"zan ɗan biya na yi siyayya ina mai ba ki haƙuri, na san zan ɓata miki lokaci amma ki yi haƙuri". Kaina kawai na gyaɗa mata kafin na ce"ba komai"? Ta ja motar muka bar cikin asibitin a bakin wani ƙaton shago ta tsaya da ake ta hada-hada a ƙofan shagon. Sai yanzu na yarda cewar garin jarafi babban gari ne na bugawa a jarida wanda ganinsa ya zarce jin sa.
"Bari na shiga yanzu na fito". Kaina kawai na jinjina mata da hakan ya ba ta damar fita daga cikin motar ta fita, na zuba idanuna ta tagan ƙofan motan ina ƙarewa mutanen da suke wucewa kallo. Jin an buɗo ƙofar an shigo an zauna shi ya dawo da ni cikin hayyacina. Muka haɗa ido da ita ta sakar mini da murmushi ba tare da ta ce da ni komai ba. Sai da muka fara tafiya kafin ta kallo ni ta ce"ina muka nufa ne, ina ne gidanku?". Na rusunar da idanuna ƙasa kafin na ce"ki sauƙe ni a duk inda titin ya tsaya".
"Ban gane ba?".
"Ba za ki gane ba ko na yi miki bayani".
"Kin yi min bayanin ta ko ya ya ne zan fahimce ki. Me yasa kika gararamba a kan titi a irin wannan shekarun nakin da ya dace a ce ki na makaranta ko kuma wajen koyan sana'ar da za ki dogara da kanki".
Na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya kafin na ba ta amsa da faɗin"aiki na fito nema".
"Wani irin kike nema?".
"Ko wani irin aikin ƙarfi inna samu zan yi sa. Ko wankau ko raino". Ta ɗan yi shuru na wasu daƙiƙu kafin ta ce"za ki yi aikin cikin gidan kamar su shara, mopping da girki?".
Na cije leɓena kana na ce"zan yi idan na samu sai dai an ce da ni samun irin wannan aikin da wuya don gidajen da suke da halin ɗaukar mai aiki yanzu Abuja suke zuwa su je kamfani a kawo musu duk kalar wacce suke so su zaɓa. Ba sa ɗaukar ya ku bayi irin mu".
Ta saki dariya mai ƙarfi daidai lokacin da take karya kwana ta ce"waye ya gaya miki hakan? Tabbas akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu da suke da rajista da gwamnati da suke samowa mutane masu aiki, sai dai ba kowa ba ne yake da irin wannan ƙa'idar. Idan za ki iya yin aikin da na lissafa zan ɗauke ki aiki a gidana". Babu shiri na ɗago ido ina kallon ta"ranki ya daɗe don Allah da gaske kike wannan zancen?".
"Me ye zai hana na yi miki wasa akan abin da na san kin É—auke sa da muhimmanci. Da gaske na ke yi zan É—auke ki aiki idan har kin amince yanzu ma sai mu wuce gidan ki gani".
Ta sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da cewa"na amince na gode sosai Allah ya saka miki da alkhairi".
"Amin ya Allah, to ni dai sunana Hajiya Muhibbat na yi aure shekaru biyar da suka wuce ina zaune da mijina cikin farin ciki da ƴaƴa biyu tagwaye. Ni ƴar kasuwa ce da take harkan sayar da atamfofi da haɗa kayan lefe, ina da manyan shaguna har guda uku a cikin ƙwaryar garin nan. Mijina yanzu haka ba ya ƙasan nan ina zaune ne tare da ƴaƴana da kuma ƙanin mijin nawa Saifullah".
"Allah ya yi wa rayuwa albakar ya ƙara muku kwanciyan hankali da son junanku".
"Amin ya Allah". Ta amsa cikin jin daɗin da ya bayyana har a bisa fuskanta daidai lokacin da muka iso bakin gate ɗin wani gida madaidaici sai dai tsarin ginin ya ƙawat matuƙar gaske, ta yi horn aka zo aka buɗe gate ɗin ta shiga ta yi parking ɗin motar a filin da aka tanada mussamman domin ajiye motoci.
Ta fito tana gaba ina bin ta a baya har cikin gidan. Muka yada zango a falo ta zauna a bisa kujera yayin da na zauna a ƙasa ina sauraron abin da take faɗa.
"To kin ga dai inda nake zaune nan ne gidan mijina wanda na riga na yi miki bayanin komai. Tagwayena suna gidanmu wajen mahaifiyata za su yi hutun ƙarshen mako a can, ƙanin mijina kuma Saifullah ya tafi wajen aiki, engineer ne amma yanzu haka yana harkar siye da siyen filayi da gidaje ne. Zan yi magana da mijina zuwa anjima da yamma sai ki dawo ki ji yadda muka yi da shi".
"To ranki ya daÉ—e na gode sosai Allah ya saka da alkhairi".
"Amin ya Allah. Ɗauki wannan ledodin naki ne". Ban ce komai ba na ɗauki ledar maganin zan fita ta dakatar da ni"sauran ma dukka na ki". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu"kin gan ni nan ba na magana biyu, a ke na saya don haka ki ɗauka domin ni ba na buƙatar su".