← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 72

Sashe 33

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko a cikin mungayen mafarkan da na yi sheiɗan bai taɓa kimtsa mini cewar wata rana zan yi zaman kaina ba, balle har na kwana na tashi a cikin gidan karuwa. Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina ina sulale ƙasa na yi zaman dirsham ina wani irin kuka mai rauna zuciyar mai saurare.
Haƙiƙa sai yanzu na ƙara yarda cewar babu abin da ya kai mutuwa tonon silili da ban kaɗo rufaffun sirrukanta ta sanya a faifayi ta raba a duniya. Ina da yaƙinin da Abbana yana raye a cikin wannan duniyar da ban tsinci kaina a cikin wannan rayuwar ba, ko da kuwa ƙaddara ta jawo ni to tabbas ba zan yi nisan zango a cikinsa ba. Tun ina kukan hawaye suna zuba har sai na na koma yin kukan zuci sa boda hawayen sun tsaya sun kafe tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe na tsawon shekaru masu nisan zango.

Jin da na ji ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin shi ya fargar da ni na dawo cikin hayyacina daga na tunanin da na yi nitso a cikinsa. Da ƙyar na iya miƙewa akan ƙafafuna sa boda ciwon kan da lokaci guda ya rufe har ya sauƙar da mini da zazzaɓi mai zafi a cikin jikina. Sai da na wanke fuskana kafin na buɗe ƙofar muka haɗa ido da Altine na yi saurin kasar da nawa idon daga gare ta ina ƙoƙarin fitowa daga cikin banɗakin na ce"ina kwananmu mun tashi lafiya?".
Ban damu da sai ta amsa mini ba na sa kai zan yi wuce ta ta jawo ni na koma da baya.

"Me ye kika aikatawa a cikin banɗakin da kika shiga kika ƙulle ƙofa?".

"Har abun da na aikata a cikin banÉ—akin ma zai na sanar da ke ranki ya daÉ—e?". Ban tsaya na ji amsar da za ta ba ni ba na yi ficewa ta daga cikin É—akin na bar ta tsaye a wajen tana cizon Æ´atsa.
Na iske Hajiya Muhibbat zaune a cikin falon tare da Saif da alama wata muhimmiyar tattaunawa suke yi ganin yadda gabaÉ—ayan su suka tattara hankulansu waje guda.
"Anty lokaci ya yi fa za mu gaya wa Yaya gaskiya abin da yake yi sam bai dace ba. Ta ya ya mutum mai iyali sai tafi can wata uwa duniya ya tare shi kaɗai har ya shafe tsawon wani lokaci mai tsayi ba tare da ys waiwayi amanar da yake kansa ba balle har ya yi ƙoƙarin sauƙe nauyin da Ubangiji ya ɗaura masa ba. Anty idan ma har yanzu wannan abun da ya faru ne a cikin ransa ai ina tunanin za ki ci albarkacin waɗannan ƴaƴan da kika haifa masa ya sauƙo. Ya rumgumi ƙaddara kamar yadda ke ma kika manta da duk abin da ya afku kika amshi a matsayin miji a gare ki kuma uba ga tagwayen ƴaƴanki".

Cike da gajiya da sauraronsa Hajiya ta É—aga masa hannu muryarta tana rawa ta ce"Saifullah ya isa haka ba na son ana tuna min da abin da ya riga ya wuce hakan ya kan jefa ni cikin wani irin hali. Ina yi wa Saddam uzuri akan komai da yake aikata ba wai don ba na jin zafin abin da yake aikata wa sai don kawai É—aurewar zaman lafiya a tsakaninmu da shi tun da ka fi kowa sanin halaye da É—ab'iun É—an uwanka. Babu abin da Saddam zai aikata a gare ni da hakan zai sauya matsayin da yake da shi a cikin zuciyata".

"Anty wai har sai yaushe ne za ki daina yi wa Yaya Saddam uzuri akan rashin adalcin da yake yi a gare ki? Na yarda ki na son mijinki amma don Allah na roƙe ki kar ki ba fi wannan soyayyar ta rufe miki ido, ta ki kasa faɗa masa gaskiya idan ya aikata ba daidai ba. Shi fa zaman aure na mutum biyu ba na mutum ɗaya ba dole sai kowa ya ba da na shi gudumawar kafin abubuwa su tafi yadda ya kamata. Anty ba ni da kowa a duniyar nan da ya rage min face Yaya Saddam shi ne komai na wa, shin ki na tunanin ba na jin zafin abin da yake aikata wa ne? Waɗannan fa ƴaƴansa ne ke kuma matarsa ce wacce ta sadaukar da komai sa bosa shi, ki zaɓi shi sama da kowa. Ki zaɓi ki yi rayuwa da shi har izuwa lokacin da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinki".

"Ya isa haka Saif na ce ya isa haka".
Hajiya ta yi zancen cikin É—aga sauti tana sa hannayenta ta toshe kunnuwanta da su.
"Ka tashi ka fita ka ba ni waje ko kuma ka yi wata maganar amma ba wannan ba. Don ba zan iya juran hakan ba".

Miƙewa tsaye ya yi jikinsa gabaɗaya ya mutu murus kamar wanda aka zare wa laka. A hankali yake motsa leɓansa yana faɗin"shi kenan Anty ba zan ƙara yi miki wannan maganar ba. Daman na shigo na sanar da ke cewar ɗazu na kai Muhammad Sultan filin jirgi, mun zo tare zai yi miki sallama kuma na ga ba ku buɗe ƙofa na ƙira wayarki ba ki ɗaga ba, ya ce a yi miki godiyar irin ɗawainiyyar da kuka yi da shi a tsawon kwanakin da ya yi a cikin wannan gidan". Yana dasa aya a zancen ya juya ya fice daga cikin falon, da hakan ya sanya Hajiya dafe kanta cike da damuwar da ya gauraye da tsananin tashin hankali.
Saɗal-saɗal na ja ƙafafuna na bar cikin falon na wuce cikin kicin na tarar da babu wani alamar an ɗaura girki, na nema waje na tsaya na rumgume hannayena a ƙirjina kafin na soma safa da marwa a cikin kicin ɗin.

"Saddam".

Na maimaita sunan a bayyane ina sauƙe wani gwauron ajiyar zuciya mai nauyin kilo ɗari da ɗoriya da ƴan kai. In dai ta tabbata cewar wanda na ga a fuskar wayar Zinariya shi ne Saddam mijin Hajiya Muhibbat ya yi wa Zinariya alƙawarin durowa cikin ƙasar nan a yammacin ranar juma'a.

"Kai kawon me ye kike yi? Ba ki fara haramar É—auka abin kari ba?".

Na tsinkayo muryar Altine ya sauƙa a cikin ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu. A ɗaga kai ina dubanta cike da son ƙarin bayyani, fahimtar abin da nake nufi ya sanya ta faɗin"ƙwarai ai kin ji abin da na faɗa, da can waye kike ajiye da kike tunanin zai ɗaura miki girkin ki zo ki ɗiba ki je ki baje akan katifa?".

Ban ce da ita komai ba na wuce na soma kici-kicin ɗaura girkin, ɗan wake na yi mai rai da motsi. Na yanda kabeji, tumatur da kokanba na soya mai ya soyu rafai. Na haɗa komai na jere su akan dinning table kana na zo na durƙusa a gaban Hajiya.
"Hajiya ga abin karin kumallo a gama".

"Amatullah ba na jin zan iya cin komai, ba na jin sha'awar cin dankalin nan a dai kawo min ruwan shayin na sha kawai".

"Ba dankali ba ne ranki ya daÉ—e, É—an wanke ne".

"ÆŠan wake?". Ta maimaita na gyaÉ—a mata kaina alamar e.
"Ai kuwa na kwana biyu ban ci É—an wake ba. Tun wani lokacin da muka je gidan Hajiyata ta sa aka yi mana rabona da cin É—an wake. Kawo min nan mu ci tare da su Ayan sai ki kai wa Saif na shi don na san yanayin da ya bar nan ba lalle ya shigo yanzu ba".

"To".

Na amsa da shi a taƙaice tare da tashi na je na kawo mata komai gabanta, na haɗa na Saif kamar yadda ya faɗa na fita zan kai masa, ina ta jeranta sallama a ƙofar falon amma ba a amsa ba kamar yadda ba a fito an buɗe ƙofar ba. Sai can aka zo aka buɗe ƙofar na tura ƙofar na shiga cikin bakina ɗauke da guntun sallama.
Yana kwance akan doguwar kujerar zaman mutum uku ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman ƙirjinsa yayin da hannu ɗayan ya dafe goshinsa da shi, idanunsa suna lumshe amma na tabbatar da cewar ba bacci yake yi ba. Na ajiye tray ɗin abincin akan teburin da yake gabansa na juya zan fita.
[12/6, 1:28 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 6️⃣3️⃣

Har na kai ƙofar ficewa daga cikin falon na tsinkayo muryarsa a dake yana faɗin"dawo ki ɗauke abin da ya kika ajiye".
"Me yasa?". Ya yi banza da ni ba tare da ya ce da ni ci kanki ba, shurun sa bai hana ni ƙarisa zancen da na ɗauko ba"Hajiya ce ta ce a kawo maka idan ba za ka ci ba ita ya kamata ka ƙira ka sanar da ita, faɗa nata ne ni kuma ci kawa nawa".
Ina dasa aya anan na juya na fita daga cikin falon a hankali nake taka ƙasa ina ɗaga ƙafafuna da ƙyar na koma cikin sashin Hajiya suna zaune tare da su Ayan suna cin abinci sai dai ita juya cokalin kawai take yi ban ga ta kai ko da loma guda cikin bakinta ba.
Na rusuna na yi mata sannu ta amsa mini tare da cewa"ki dafa min shayi ba na jin daÉ—in jikina ba zan iya cin komai ba".

"To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice cikin bin umarni da girmamawa. Na wuce cikin kicin ɗin na dafa mata shayin da ta buƙata babu ɓata lokaci na kammala na kawo mata. Tana zaune akan kujera ta jingina bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanunta ta dafe goshinta da hannayenta da hakan ya taimaka wajen fito da damuwar da take cikinsa ƙarara.
"Hajiya lafiya kuwa kike?".
Sai a lokacin ta buÉ—e lumshashshun idanunta na kuma fahimci lumshe su da ta yi ashe kuka take yi.
"Subhanallahi! Kuka ku ma Hajiya me ya yi zafi haka?".
Chapter 33 · 0% Book details