← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 72

Sashe 54

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amatullahi mu je na ba ki ruwan sai ki kai mata ta sha". Idanuna cike da hawaye na ɗago kai ina kallon matar Ustazu Abdulwahab da take tsaye a gabana, ta amshi kofin hannuna ta je ta ciko mini shi da ruwa taf ta kawo mini na amsa, motsa leɓena nake yi da zummar son furzar da kalaman godiya gare ta sai dai na kasa. Fahimtar hakan ya sanya ta faɗin"ba damu ba sai kin gode min ba Amatullah, ki yi maza ki kai mata ta sha ga shi har yanzu tarin bai lafa ba". Kaina kawai na jinjina mata na juya da sauri na koma cikin ɗakinmu na ba wa Umma ruwa ta ɗan sha amma duk da haka tarin bai lafa ba.
Jikina yana rawa na soma karanto wani yanki daga cikin yankokin Alqur'ani mai girma tofawa a cikin ruwan kana na ba ta sha. Kamar yankan wuƙa take tarin ya tsaya kamar an yi ruwa an ɗauke, na din ga jeranta mata sannu wani na bin wani tare da gyara mata zamanta tare da sanya mata matashi a bayanta ta yadda za ta ji daɗin zaman.
"Umma haka tarin yake yi miki haka kamar zai raba ki da numfashinki?". Ta gyaɗa mini kanta ta na ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushin ƙarfin hali.

"Umma dole mu tafi asibiti a duba ki, don a gano ainihin abin da yake damun ki. Zama haka ba zai yiyu ba bari na je na dubo Anty Zulaihatu ta zo ta". Na yi zancen ina miƙe wa tsaye zan fice ta riƙo hannuna hakan ya sa na waigo ina kallonta da ido ta yi mini alama akan na dawo na zauna na kuma yi kamar ta buƙata.
"Amatullah ina ji a jikina wannan jinyar ba na tashi ba ne abokin tafiya ne, ki yafe min duk abubuwan da na yi miki, na san da cewar duk halin da kika faɗa ni ce sila DAFIN HARSHEna ne sila. Kaicona! Ba na tunanin akwai wani maganin da zan sha na sama sauƙi ko da kuwa na sama sauƙin ma to iya na gangar jikina ne, amma ciwon da yake cikin zuciyata yafiyarki gare ni kawai zai warkar da wannan gyambon".

"Umma kin wuce komai a wajena haka zalika kin fin ƙarfin komai. Wallahi wani ne ya yi mini ba daidai ba ki ka ce na yafe masa to an gama maganar ke nan balle kuma ke da kanki. Umma na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki ɗaya amma don Allah ki bari a kai ki asibiti, a nema miki magani".

Ina gama maganan na tashi na fita ina fitowa na hango Anty Zulaihatu tana shigo hannunta riƙe da baƙin leda. Na yi hanzarin isa gare ta"Anty Zulaihatu don Allah ki zo mu kai Umma asibiti". Da sauri muka isa cikin ɗakin, muka haɗa muka rawa mu tafi asibiti Umma ta ce ba za ta je ba har Yaya Alhassan muka ƙira a waya ya zo ya saka baki amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda.
Yaya Alhassan ya ce a bar ta zuwa gobe ko za ta sauƙo ko kuma a ƙira likitan ya duba ta a gida, tare da Anty Zulaihatu muka share ɗakin muka tsaftace ko'ina. Muka yi wa Umma wanka muka sauya mata kaya.

Sai dab da magrib Anty Zulaihatu ta koma gida sa boda a ranar mijinta zai dawo. Haka na zauna na Umma na tisa ta a gaba na din ga karato mata karatun Alkur'ani da nufin ko za ta sama nutsuwa a cikin ranta.
"Amatullah Allah ya miki albarka".

Babu shiri na tsaya daga karatun da nake yi ba tare da na zo gaɓar da ya dace na tsaya a ƙa'idance ba.
"Umma me ye ki ka ce?".

"Ce wa na yi Allah ya yi miki albarka".
Ban iya amsa wa da kalaman baki ba, illa jan jikin da na yi na isa kusa da ita, hawayen farin ciki da murna su na zuba daga idanuna, ba zan iya tuna ranar da Umma ta taɓa sa mini albarka a kaf cikin rayuwata ba.
"Umma na gode, ke ma don Allah ki yafe mini kura-kuren da na yi miki". Ta sa hannu ta shafo kaina"ba ki taɓa ɓata min ba Amatullah, Allah ya raya ki".
"Amin ya Allah". Na amsa da shi ina kwantar da kaina a bisa kafaɗunta ina ta sauƙe ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Sanadin albarkan da Umma ta sanya mini na ji na manta da dukkan damuwata har na ji wani nutsuwa ya mamaye mini ruhina. Ina zaune a haka ban san lokacin da bacci ya sace ni ba. Muryar Umma shi ya yi silar farkar da ni daga baccin da ya ci idona.

"Ki tashi ki rufe mana ƙofa, sanyi ya fara sauƙa".

Firgitit! Na buɗe idanuna ina kallon cikin ɗakin da duhu ya mamaye ko'ina alamar dare ya daɗe da yi. Na lalumi wayar da yake wajena na kunna haskenta tare da duba lokaci da ya nuna mini ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare.
"Subhanallahi! Umma kin ga har dare ta yi". Na yi zancen ina tashi na sassauƙe labulen tagogin sannan na rufe ƙofan ɗakin, na zo na zauna a nutse na soma faɗin"ni kuwa Umma ina kayan cikin falon suke na ga har cikin ɗakin babu komai. Daga tabarman nan fa sai ƙunshin kayan sakawanki".

"Na sayar da komai da yake cikin ɗaki da falon nan, duk kuɗin su ƙare akan jinyata kafin Alhassan ya kawo min ɗauki. Amatullah tabbas Sawwama da ƴaƴanta su cika cikakkun masoya a gare mu, don ba kowa ba ne za a yi masa abin da na yi Alhassan kowa har ya dube ni da idon rahama a lokacin da nake buƙatar taimako daga gare sa". Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau na taƙaita zance ta hanyar gyara mata wajen da za ta kwanta na kwantar da ita bayan na yi mata alwala da ruwan goran da Yaya Alhassan ya kawo mana ɗazu da ya zo shi, na shafe mata jikinta da addu'a ni ma na kwanta a gefenta. Sai dai bacci ya ƙi ziyartar idanuna haka na yi ta tunani masu nauyi, kafin wasu hawayen tausayin kanmu da yadda rayuwa ta mayar da mu ya fara zuba daga idona.
Ina ma wanda ya mutu yana dawowa tabbas da sai na bayar da duk wasu abubuwan da na mallaka a cikin duniya, don kawai Abba ya dawo ya ga tsantsar nadama da dana-sanin da yake kwance a cikin idanun Umma, zan zo ya dawo ya ga yadda ta yi kewarsa a duniya yayin da ta soma amfani da tarin nasihohin da yake yi mata, Allah mai iko wai yau bakin Umma yake furta mini kalmar Allah ya yi miki albarka.

Ban iya runtsawa a wannan daren ba har aka ƙiran sannan asubahi na tashi na yi alwala na yi sallan, sannan na zo zan tashi Umma don na yi mata alwala ta yi na ta sallan na ji shiru, na soma ƙiran sunanta ina bubbuga matashin da kanta yake kai nan ma ba ta tanka mini ba. Nan fa ido ya raina fata na soma jijjiga ta ina ci gaba da ƙiran sunanta amma har yanzu shuru.

"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umma don girman Allah kar ki yi mini haka. Ki yi wa Allah ki buɗe idanunki". Na yi furucin cikin tsananin kiɗima da ruɗewa, ganin zaman ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sa na na baza ma waje, ɗakin Umman Amira na nufa ina buga mata ƙofa tare da ƙiran sunanta amma ba ta amsa wa, babu abin da nake iya furtawa illa kalmar innalillahi wa inna ilahirin raji'un. Na daɗe buga ƙofan kafin Baba Habu mijinta ya shigo da alama daga masallaci yake.

"Ke lafiya?". Ya watsa mini tambayar cikin zafin rai.
"Daman jikin Ummata ne ya tashi shi ne na zo ƙiran Umman Amira, ta taimaka ta zo mu je ta duba ta".

"Wani irin ta duba ta? Likita ce ita ɗin ko kuma da na ilmin sanin jinya? Warin da yake fita daga jikin Hafsatu da matata ta shaƙa jiya shi kaɗai ma sai da ya haddas mata cuta, daren jiya ba mu runtsa ba. Haka ina zaman zamana aka sa ni kashe ƴar dubu uku ta na sayo mata magunguna shi ne fa har ta sha ta kwanta yanzu da zan fita Masallaci. Don haka ba za ta je ko'ina ba idan jikin ya yi tsanani ki ɗauke ta ki kaita asibiti likitoci su duba ta".

Cike da mamaki na ce"Baba ni ce Amatullahi, ko ba ga shaida fuskata ba ne?".
"Na shaida ki tsaf fuskarki ai ba ɓoyayyiyar fuska ba ce a cikin unguwan nan, na gane ki sarai ko ba Amatullah ɗiyar ba ce Malam Manniru da ta yi cikin shege har hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa ba, sannan ko kwanaki arba'in bai cika a ƙasa ba kika sanya ƙafafunki ki ka gudu daga gida kika bi Saurayin da ya yi miki cikin ku ka je can ku ka ci gaba da baɗalarku ba". Yana gama zancen ya zo ya buɗe ƙofar ɗakin ba ko kusa ban yi tunanin a buɗe take ba ya shige abin sa.
Har ƙasa na durƙushe akan gwiwoyina ina ta wani irin haki tamkar wacce ta fafata a gasar tseren gudu a matakin duniya gabaɗaya.

Ina cikin wannan halin Ustazu Abdulwahab ya shigo cikin gida ya dawo daga masallacin sallan asuba, ya tambaye ni me ke faruwa? Cikin sanyin amo na zayyana masa komai ya ce mu je ya duba ta. Na yi gaba ya na bi na a baya muka ka isa wajen Umma.
Ya kai minti biyu yana kallon fuskarta sa boda tun da na tashi na kunna hasken wayata na ajiye. Sai can ya tsuguna a gabansa tare da kai hannunsa daidai hancinta hakan bai yi masa ba sai da ya riƙo tsintsiyar hannunta na ɗan danna yatsansa kafin na ga ya jijjiga kansa.

"Don Allah me yake samun ta? Tun É—azu fa ban ga ta yi motsi ba. Shi yasa tun jiya nake ta ce mata mu je mu asibiti".
Chapter 54 · 0% Book details