Sashe 37
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni fa yanzu ba aure ba ne a gabana Amatullah, kuma ke ki na tunanin aure a cikin wannan lokacin abu ne mai sauƙin da kike ta faman faɗinsa haka? Duk wacce ta sako ƙafarta ta tako cikin gidan nan da zummar shigowa harkan bariki to kafe ta ake yi, su shanye ta ta yadda ko ta so fita daga harkar ba za ta iya ba, wannan dalilin ne ya sanya da yawa daga cikinmu ko mafarkin fitan ma ba sa ya yi balle su yi wani yunƙurin ganin hakan ya faru. Wasu ma da suka riƙa a cikin harkan har ƙungiya ne da su da zaran kin yi yunƙurin fita za su sanya miki wani cutar da za ki yi ta fama da shi har sai kin gwammace mutuwarki akan ci gaba da rayuwa. ko ma su haukata ki gabaɗaya wasu ma idan kika yi karo da masu rangwamen imani sai sun yin sanadin rayuwarki. Kin ga duk wacce ta yi gangancin barin cikn gidan iyayenta ta bijire musu ta zaɓi ta yi nisa da su har tsautsayi ya sanya ta sako ƙafafunta cikin harkar bariki sai dai a fitar da gawarta ba daidai ta sauya sheƙa ba".
Kalamanta suka sanya ni faÉ—a cikin tunani mai zurfin haske sai na É—au wasu mintuna kafin na magana a hankali.
"Ki na nufin matan cikin gidan nan ma duk Hajiya Babba ta kafe su ke nan? Ko suna son barin wannan harkar ba za su i ya ba?".
Maimakon ta amsa mini sai kawai ta fashe da dariya mai matuƙar sauti har tana shiɗewa ta kwanta akan katifar tana dariyar. Na tsaya kawai ina ta kallonta cikin al'ajabi da mamaki.
"Ki gwada ƙoƙarin fita ki ga ni sai ki zo ki ba wasu labari". Ganin ta mayar da abin shiririta ya tursasa mini yi wa bakina linzami sai dai giyar mamaki da al'ajabin da zantukanta suka shayar da ni bai sake ni har yanzu wannan lokacin.
Jiya ina jin hayaniyarku da Shaaqana ikon Allah. Kin yi min daidai don tun kallon farko da na yi wa yarintar na ji ba ta kwanta min a cikin rai ba, ita ba kyau ba, ita ba kyakykyawan sura balle giri haka nan babu murya mai daÉ—in sauraro uwa uba ga duhun fata tamkar bayan tukunya".
"Ta kai ni maƙura ne amma ni ma hakan ba halina ba ne".
"Ai babu abin da bariki ba ta saka mutum ya yi duk wani halin da bai kasance naka ba dalilin bariki da rayuwar jikinta, za ta sanya ki fara É—abi'antuwa da shi ba tare da ita ma kanta ta sani ba. Kin ga bariki da kike gani kike raina wa awwbillahillazi babu abin da ba zai sa mutum ya yi ba, take za ki rikiÉ—e ki soma sauya launi tamkar hawainiyya".
"To Allah ya kyauta".
"Amin". Ta amsa da shi a taƙaice tana tashi ta zauna daga kwanciyar da dariyar da take yi ya tursasa mata yin sa.
"Yanzu dai za ki raka ni kasuwar ne ko ƙaƙa?".
Ta É—an yi shuru kafin na yi tunanin abin da zan faÉ—a"sai dai mu yi wani abu ki ba ni gishiri na ba ki manda".
Ta bi ni da ido"yi min yadda zan ga ne".
"Zan raka har sai kin gama duk siyayyar da za ki yi ko da kuwa za mu kai dare a can. Amma ni ma fa za ki taimaka mini ta wani fannin don cimma wani daÉ—aÉ—É—an burin raina".
"Wani buri ne wannan haka? Kuma ta wani hanya zan iya taimaka miki?".
Na gyara zamana kafin na hau zazzago mata bayani ina zuba tamkar bishiyar magarya.
"Akwai wani mutumin da nake son ko ta wani hali ne na gan shi ya ganni ko da kuwa na minti guda ne. Sai dai kasancewarsa babban mutum kuma mai kima da daraja a idanun mutane hakan yana neman ya gagare, idan har kika taimaka mini ki ka yi mini hanyar ganinsa kin gama yi mini komai a cikin rayuwar nan". Cike da zaƙuwa ta ce"wane mutum ne haka?".
"Sunansa Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe, amma na ji a garin nan ana ce wa da shi ba baƙin balarabe". Tun kafin na gama zancen ta waro idanu waje tare da dafe ƙirji"anya kanki ɗaya kuwa kin san abin da kike faɗa? Duk da ban cika sauraron wa'azi da halattar inda ake faɗin Allah ya ce Annabi ya ce ba, tabbas wannan sunan ba ɓoyayye ba ne ga kunnuwan kowa da yake cikin garin na babba da yaro. In ban yi ƙarya ba a iya sani na shi ɗin babban Malamin addini ne da aka yi masa shaidar dukkanin halaye da ɗabi'u na ƙwarai. In kin haɗu da shi me ye za ki ce masa ke kuwa?".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na soma kora mata bayani daki-daki ban ɓoye mata komai tun daga farkon haɗuwarmu na kwashe na sanar da ita.
Ta yi shuru tamkar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"to ke yanzu ta ina za ki fara neman sa? Sannan in kin yi dace kin gan san ma me ye za ki ce da shi har ki ja ra'ayinsa? Wallahi da gwamma garin nan kika yi wannan alwashin akan sa sai na ce da ke hakan zai ya fi miki sauƙi n akan wannan da kika yi".
"In dai har na gan sa ɗin to haƙiƙa na yi mai wuyar".
Ta yi shuru tare da zabga tagumi tana kallona kafin ta ce"tabbas ba ki da hankali". Ta yi zancen tana ƙoƙarin tashi ta fita na yi hanzarin cafko hannunta.
"Ina cikin hnakalina sai dai ku da kuke yi mini kallon zautacciya ku ya kamata a bincike ƙwaƙwalwarku. Ke dai inda taimakon da za ki iya yi mini kawai ki yi mini inda babu taimakon da za ki yi mini kuma to ki bi ni da fatan alkhairi".
Sai da ta ƙare mini kallon tsaf irin kallon da mai hnakali yake yi wa zautacce kafin ta ce"ban san me ye zan ce miki ba Amatullah". Ta koma ta zauna kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya.
"Taimako É—aya zan yi miki shi ne na haÉ—a ki da wata mata da take ba ta sirrin mallaka da karkato da hankali mutum zuwa gare ka, shi ma kuma fa sai ku na garin É—aya ta yadda za ku dinga haÉ—uwa har aikin ya ci".
Na jijjiga kaina"ba na son na jawo hankalinsa ta hanyar asiri. In dai kawai in akwai hanyar da za ki yi ki taimaka mini ki yi amma ba wannan ba". Ta yi shuru na tsawon mintuna har sai da na karaya kafin can ta ce"na san otel ɗin da tawagarsa suke sauƙa idan suka zo gabatar da wa'azi a ciki garin nan, sai dai in daga nan za mu sama ƙarin bayani. Don na taɓa ganinsa sau ɗaya a otel ɗin lokacin da ya zo gabatar da wa'azi a cikin tsakiyar watan Ramadana. A lokacin an ce babu yadda mai martaba Sarki bai yi da shi ba akan ya sauƙa a can masarautar amma ya ƙi a lokacin har Gwamma sai da ya saka ba ki amma bai amince ba, dalilin hakan ranar aka yi kora a otel ɗin babu wanda aka ba wa ɗaki sai shi da tawagarsa".
Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina hamdala a cikin zuciyata. Farin ciki ƙarara ya bayyana a bisa fuskata da har sai da na kasa magana.
Sai da na yi da gaske na sama zarafin faÉ—in"to yanzu yaushe za mu je mu tambaya masu otel É—in?".
"Mu je ina otel? Ce miki aka yi haka siddan ake zuwa otel ɗin a soma tambayan ma'aikatansu bayanan kwastomominsu? Ai hakan ya saɓawa ƙa'idar ko wani irin aiki kawai taɓarɓarewar ƙasar nan ya jawo haka. Yanzu dai akwai wani da na sani ma'aikaci ne a otel zan tuntuɓe mu ji abin da zai ce".
"Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Na yi zancen ina rumgume ta tsam a jikina tsabar murnar da ta soma ni a cikinsa kacokam. Mun ɗan tattaunawa da ita kafin mu farga har aka yi ƙiran sallan magrib hakan ya tursasa masa haƙura da zuwa kasuwan sai gobe.
Har na tashi zan fita na ce"yau na girki ne?".
Ta murmusa kafin ta ba ni amsa da faÉ—in"yau ina da fitan dare shi yasa ban yi girki ba".
"Fita zuwa ina ke nan?".
Ta yi fari da idanuna kana ta furta"na yi wani sabon kamu ne ina so na je mu ƙarƙare ta da shi. Na fi so na gama da kowa kafin na yi wannan gyara jikin don idan na yi san na fi son Ogana ya fara shan romonsa". Na bi ta da kallo ina mamaki da juyayin furucinta.
"Ai kuwa ba ki yi masa mai kyau ba a Ogan nakin, tun da kin kasa killace masa kanki a shi kaɗai". Ina gama zancen na fice daga cikin ɗakin ina jin dariyar zancen nawan da ta fashe da shi yayin da nake fita daga cikin ɗakin. Sai da na yi alawan sallan magrib kafin na shiga ɗaki, na gabatar da sallan cikin nutsuwa da daidaituwa bayan na iddar na ɗaga hannuna sama da zummar zan yi addu'a ina buɗe bakina kawai na ji wani kuma ya ƙwace mini. Jikina har wani karkarwa yake yi tamkar ana jona mini wutar lantarki, na haɗa kaina da gwiwa ina rero kukan don na gaza samun ikon sarrafa kaina.
Sosai nake kukan har sai da gabaÉ—aya jikina ya É—auki zafi gau.
"Indan kin gama kukan sai ki tashi je Hajiya Babban tana ƙiran ki da gaggawa". Na tsinkayo muryar an yi zancen cikin ɗaga amo, ko da na ɗaga ido har an juya an fita daga cikin ɗakin, da ƙyar na tashi na tsaya akan ƙafafuna sa boda rawar da ilahirin gaɓoɓin jikina yake yi. Haka kawai na ji ƙirjina yana buga wa sa boda na san babu alkhairi a cikin dukkan ƙiran da Hajiya Babba za ta yi maka.
[12/11, 3:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 6ï¸âƒ£6ï¸âƒ£