← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 72

Sashe 23

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin sa a cikin kunnuwana kafin ta furta"ina kuwa zan iya tambayanki bayan kin gama shayar da ni giyan mamaki. Ba ni labari me ya faru don na ga kin ma dawo da wuri ai". Na fesar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na juye mata duk abin da ya faru.
"To yanzu wani shawara kika yanke barin aikin ke nan za ki yi, ko kuma ya ya za ki yi?".

"Da farko na yi tunanin na haƙura da aikin amma tun daga lokacin da Baba Mai gari ya sanar da ni wace ce Altine, da kuma salon nau'in munafurcinta sai na ji na ƙara son aikin a cikin raina, zan shiga cikin Hajiya sosai har sai na fahimtar da ita wace ce Altine na kuma fito da ainihin halinta kowa ya gani. To daga wannan ranar zan bar aikin".

"Tabbas kin yi tunani mai kyau".

Kafin na ba ta amsa wata budurwa ta shigo cikin ɗakin ta jefo miji baƙin ledar dake hannunta.
"Ga shi in ji Hajiya kayan sakawa ne ta ce ki saka su. Don baƙonki yana hanya". Na tsaki wani murmushin da ba shi da haɗi da nishaɗi kafin na ce"to ina godiya saƙo ya iso. Tabbas Hajiya tana ƙoƙarin sangarta ni a cikin gidan nan, har kaya take saya mini". Na ƙare zancen ina bin budurwar da kallo da take ta cika ta na batsewa da tun a tashin farko na fahimci a cikin biyu dole akwai ɗaya. Ko dai baƙon da zai zo musamman domin ni take baƙin ciki da zuwansa ko kuma kayan da Hajiya ta ba ni ne ya baƙanta mata rai.
Tsaki ta tsirtar mai dogon zango tare da faɗin"har ina abin yake wai maye ya ci jajiri? Ke kar kin sa ki shiga sahun matan da Hajiya take ji da su a cikin gidan nan? Ko da yake ai an ce na kwance bai ga gari ba". Ta na gama zancen ta juya ta fice na taka ta da dariya da ina da tabbacin hakan ya ƙara ƙular da ita matuƙa. Na ɗaga muryata na ce"a sauƙa lafiya".

"Ke Amatullah wai ke ce kuwa?". Furucin La'aniyatu ya sa ni waigo wa ina kallonta.
"Me ye kika gani?"
"Na ga kin tsiri wasu É—abi'un da ba na ki ba kin lafawa kanki".

"Yanayi ne yake sauya wasu abubuwan La'aniyatu. Wani lokacin mutum ya kan sauya na tare da shi kansa ya fahimci hakan ba". A raunane na yi zancen ina jin ruwan hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata.
"Bari na bar ki ki shirya". Tana zancen tana miƙe wa ta bar cikin ɗakin a ƙalla na ɓata mintuna talatin zaune a wajen ban motsa ba, kafin na zazzage ledar ina kallon kayan ciki. Doguwar riga ce irin da aka watsa mata duwatsu masu ƙyalla da haske sai kuma mayafinta da ba shi da girma wanda bai zarce girman kallabin da yake kaina ba. Sai kuma turare su kenan a cikin ledar na ɗaga rigar ina kallo tare da sauƙe tagwayen ajiyan numfashi.
Na saka rigar na ga ya kama mini jikina sosai har da ƙyar nake numfashi, duk wata surar jikina ta bayyana musamman ƙirjina. Na ɗaura kyallen a kaina na saka hijabina don na ba zan iya fita haka ba, feshi biyu na yi a turaren na ajiye don ya yi ƙarfi da yawa har yana hawa kai.

ÆŠakin Hajiya Babba na nufa na shaida mata na shirya ta bi ni da wani irin kallo har na zauna.
"Wannan hijabin fa?".
"Hajiya ba zan iya fita da wannan kayan ba ne, shi yasa na sanya hijabin". Za ta yi magana wayarta ta soma ruri ta ɗaga na ji ta tana ba da umarnin shigowa. Tana ajiye wayar wani mutum ya shigo cikin falon ya sha manyan kaya shadda fara tas mai ɗaukar hankali ya murza hula zanna bukar ga ƙamshin da yake tashi a jikinsa tamkar an yi ɓarin durum ɗin turare a jikinsa. Ya zauna a kujerar da yake kusa da wanda Hajiya take zaune a kansa suka gaisha kafin ya ce"Hajiya Allah ya sa wannan ce wacce aka ajiye min ɗin. Don tun da na shigo na ji ta sama matsuguni a cikin raina".

Ta saki shewa"me kake ci na baka na zuba Alhaji Manga? Ai dai duk saurin ungozama za ta jira a haihu".

"Fara ba ni amsar tambayata tukunnan ita ce ko ba ita ba ce?".

"Ita ce sai aka yi ya ya?".

Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe su yana cewa"ba ki taɓa zaɓo min wacce ta dace kamar wannan ba dole na ninka abin da na saba biya sau biyar. Sai dai kuma yanzu akwai meeting ɗin da za mu yi da abokan sana'ata a cikin daren nan. Don haka gobe zan dawo sai na ɗauke ta hakan ya yi?".

"Ai duk yadda ka ce haka za a yi ranka ya daÉ—e, ina godiya".

"Da kin gaya min irin wannan surar zan zo na tarar ai da na aika wani ya wakilce ni a wajen meeting ɗin. Amma yanzu ma dai bai ɓaci ba zan dawo ko na aiko a zo a ɗauke ta, yarinya ya ya sunanki?".

Muryata a shaƙe na ce"sunana Amatullah".

"Amatullah Amatullahi baiwar Allah. Ni kuma sunana Alhaji Manga, yanzu za mu je da ke waje ki karɓo saƙo ki kawo wa Hajiya".
Na gyaɗa masa kaina ina satan kallon Hajiya na ga ta ɗage mini gira alamar na bi shi. Suka yi sallama ya fita na bi shi a baya, tun da muka fito daga ɗakin ƴan matan gidan suke ta kai masa gaisuwa yana ɗaga musu hannu. Muka fita waje inda ya ajiye motarsa ya buɗe gidan baya ya ɗauko wasu baƙaƙen ledodi guda biyu ya miƙo mini.
"Wannan ta ki ce É—ayar kuma na Hajiya ne sai ki kai mata. Kafin na zo goben ko ban zo ba ma zan yi aike".

"Mun gode". Na furta a gajarce.
"Ki saki jikinki da yarinya kin ji ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar shiga cikin motar ya ja ya tafi. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina bin ledar da ya ba shi da kallo.

"Har kin sallame shi kenan?".

Na yi figigi na É—ago kaina don gani mamallakin muryar, sai da na firgita don ban yi tsammanin ganinsa a nan kuma a irin wannan lokacin ba.
"Saifullah kuma?". Na furta a cikin zuciyata ina jin ƙirjina yana tsananta bugu ba tare da na san dalili ba
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________________

Page 5️⃣6️⃣

Duk yadda na so na furzar da zallan mamakin da ya ganin sa ya ƙunsa mini bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace, da ɗago idona ina kallonsa na ga ya watsa mini wani mummunan kallo da ban san sa'ilin da na rusunar da idanuna ƙasa ba. Sa boda cika ido da kwarjinin da yake da shi.
"Zan jira ki a wajen motata ba zan iya tsayiwa a nan wajen ba". Yana gama maganar ya bar wajen ya nufi inda ya ajiye motar da yake can farkon layin na bi shi a baya zaƙwai-zaƙwai har muka isa ya jingina bayansa jikin motar tare da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa idanunsa a kaina ya furta"Anty ce ta ce a zo a duba ko lafiya kika tafi ba tare da kin yi mata sallama ba. Sai dai zuwan da na yi da kuma abin da idanuna suka gane min ya tabbatar min da cewar lafiya kike tun da har za iya fitowa ki gana da saurayi cikin wannan daren har da guzurin saƙo niƙi-niƙi a leda".

Jikina ya yi sanyi ƙalau wasu hawaye suka kuma ciko mini idanuna sauran ƙiris su zubo na kai hannu na tare su.
"Lafiya ƙalau kawai ba na jin daɗin jikina ne shi yasa na dawo. Amma ina sha Allah gobe sammako zan yi na zo.....". Tun kafin na kammala ƙarshen zancen ya tari numfashina.
"Ba ma buƙatarki don haka ki yi zamanki. Idan ma ya zama dole to za a nema wata".

"Ba kai ka É—auke ni aiki ba ranka ya daÉ—e don haka ba ka da hurumin dakatar da ni, Hajiya ce kawai take da wannan ikon".

Tabbas na hango mamakin zancena kwance a cikin idanunsa ya sauƙe numfashi da har sai da na ji sautin fitarsa.
"Repeat yourself please".
Duk da na fahimci abun da ya furta amma sai na sauya akalar zancen"a gaishe ta kuma a isar mata da saƙona". Ina gama furta haka na juya zan tafi na ji wata murya ta sauƙa a ƙofofin kunnuwana, muryar da ba zan taɓa manta tasirinta a cikin rayuwata ba. Muryar da ko ina gangaran mutuwa in na ji ta haƙiƙa zan gane amonta. Muryar da ta sama matsuguni ta zauna a cikin kwanyata ba tare da biyan tara ko haraji ba. Cak na tsaya jikina yana wani irin rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki haƙwarana suka datse harshena wanda ina da tabbacin har sai da ya fitar da jini.
"Saif wai me ye yake faruwa ne? Ina ne nan wajen kuma?".

"Ba komai Taukif shiga motar mu tafi kawai".

"Wannan yarinyarta fa me ye haÉ—inka da ita? Na dai san ba ka zuwa ire-iren wajajen nan. Ke zo nan".
Take ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau goma sha tara, zuffa ya soma tsantsafo mini sa'ilin da na ji takun tafiya ana kusanto inda nake tsaye har ƙamshin turaren jikinsa ya riga sa isowa gare ni.

"Ke yarinya me ye kike yi a nan wajen?".
Chapter 23 · 0% Book details