← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 72

Sashe 49

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin ban ƙara sanin takamanmen inda kaina yake ba, ban ƙara fahimtar komai ba haka nan idanuna ba su ƙara gano mini wani haske ba face gilmawar duhu baƙi ƙiri da babu alama ko ɗigon haske a cikinsa. Ban san iya adadin awannin da mintunan da na ƙarar ba na cikin hayyacina ba sai buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske na yi na ganni kwance a cikin wani ɗaki wanda na ƙare wa kallo tsaf na kuma fahimci cewar ɗakin asibiti ne, kamar yadda na ga robar ƙarin ruwa a maƙale a hannuna na yi yunƙurin tashi sai dai kash! Gangar jikina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace.
Ban san sa'ilin da ruwan hawaye masu ɗumi suka soma rige-rigen fita daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin sauƙarsu na yi a bisa fatar fuskana. Abubuwan da suka wakana kafin na tsinci kaina cikin wannan yanayin da nake ciki ya soma dawowa cikin kwanyanta tiryan-tiryan, na cije leɓan bakina ina jin zuciyata tana buga wa ɓat-ɓat tamkar allon ƙirjina zai dare zuwa gida biyu.

Wahalallen numfashi na ja a karo na barkatai na fesar daga bakina yayin da na kai hannu na fincike ƙarin ruwan da aka maƙala mini a hannu. Na tashi na zauna da ƙyar yayin da nake jin kaina ya na sarawa tamkar zai faɗo ƙasa.
Ban yi aune ba na ji hawayen da suke zuba daga idanuna sun ƙara ƙarfin gudu ta yadda suke wanke mini fuskata babu ƙauƙautawa. A bayyane na furta"Yaya Alhassan me yasa kuka bayanna a cikin rayuwa a daidai wannan lokacin? Lokacin da nake dab da cika buri da muradin raina burin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjina. Ba zan iya haɗa ido da ku idan lokacin da ya dace na koma gare ku ya yi tabbas ni da kaina zan kai kaina inda kuke amma ba yanzu ba".
Ina gama zancen na diro daga kan gadon na ɗauki hijabina da yake gefe na mayar da shi kaina na fice daga cikin ɗakin, ina ta faman dube-dube da waige-waige, Allah ya tarfawa garina nono har na fita daga cikin ɗakin ban ga ɗaga cikin waɗanda nake guje musu ba. Daidai na iso ƙofar da zai sada ni da harabar cikin asibitin na ji na yi karo da mutum har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi aka riƙo hannuna na tsaya cak akan ƙafafuna, na dafe ƙirjina sa boda tsananin tsoron da na ji yayin da nake cira kai don ganin wanda ya kawo mini agaji.

Idanuna suka gauraye cikin na Yaya Alhassan da yake tsaye a wajen ya kafe ni da idanu kamar yadda ni ma na kafe sa da na wa idanun, da har suka ƙanƙace sa boda azababben kukan da na yi a cikin ɗakin bakin na fito. Shi ya fara janye idanunsa daga kaina yana riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya yayin da hannu ɗayan yake riƙe da wani ledan baƙa.
Cike da takaici ya soma faɗin"ina kika fito za ki je bayan ke da ba ki da lafiya har an kwantar da ke a gadon asibiti?". Bai jira na ba shi amsa ba ya ci gaba da faɗin"guduwa kika fito za ki yi ko?". Ya jinjina kansa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah me yasa lalle kike son ki ga kin butulcewa ni'ima da ilhaman da Allah Ubangiji ya yi miki ne? Me yasa kike ta ƙoƙarin watsa ƙasa a idanun mutanen da suka ɗaura yarda da amimcinsu kacokam akan ki? Allah ya rufa miki asiri amma ki na ta ƙoƙarin tona wa kanki asiri ga idon duniya, wai ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare ne? Ina wannan ilmin nakin da sanin ya kamata da kowa yake yabanki da shi?. Idan kin zaɓa ki guje mana a wannan karon kam ba zan yi ƙoƙarin dakatar da ke ba, tun da ba ki duba wahala da tudu da gangaran da muka bi kafin har muka gano inda kike rayuwa muka zo domin tsamo ki daga halaka ba, idan a baya mun yi miki uzuri akan duk abin da kika aikata tare da danganta hakan da cewar damuwar da kika tsinci kanki, zafin mutuwar mahaifinki da kuma raɗaɗin kalaman da mahaifiyarki ta furta a gare ki su suka haɗu suka yi taron dangi wajen ingiza zuciyarki har kika aikata abin da kika aikata. Wallahi a yanzu idan kika ƙara gangancin ƙara aikata wani kuskure babu wanda zai yi miki uzuri. Amatullah ba mu zo don mu tursasa ki ba amma tun da har yanzu zuciyarki ta na kitsa miki ki sanya ƙafa ki guje mana ba za mu yi miki tilas ba rayuwarki ce ki na da dama da ikon ki yi duk yadda kike so. Ki na da ikon ki zartar da duk wani hukunci da kike tunanin ya fi dace wa da rayuwarki tun da mai ɗaki ai shi ya san inda yake yi masa yoyo, ga hanyar nan ki tafi duk inda kike tunani da zaton za ki sama kwanciyar hankali daman fatanmu a ko yaushe bai wuce ki yi rayuwa cikin nutsuwa ba, sai dai a duk lokacin da kika nemo mu don mu zame miki gata tabbas za mu ba ki mafaka don na yarda da wannan karin maganan da ake cewa hannun ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Kuma babu inda za ki je ko juyin zamanin da zai sa mu sauya ki daga kasancewarki ƴar uwa kuma jininmu. Don haka zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya".

Yana rufe bakinsa daidai lokacin da Amir ya iso wajen duk ya bi mu da kallo kafin ya ce"Yaya ya na ganku a nan a tsaye? Ko dai an sallame ta ne?".
"Ba a sallame ta ba Amir ta dai sallama kanta ne, tun da har ta na ƙoƙarin guduwa".
"Guduwa kuma? To in ta gudu ta je ina?"
Cikin da takaicin da ya haɗe da tarin baƙin ciki Yaya Alhassan ya ɗage kafaɗunsa alamar mai sani ba a hankali ya furta"ga ka ga ita sai ka tambaye ta, ta ba ka amsa don ni kam na gama magana da ita sai dai na saurari hukuncin da za ta yanke". Yana dasa aya a zancensa ya juya ya koma cikin asibitin na lura kafin ya gama maganar har sai idanunsa suka kawo ruwan ƙwalla. Na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna yayin da na fashe da wani kuka mai rikitarwa da narkar da zuciyar mai saurare. Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da Amir ya saka kafin ya soma magana cikin sanyin jiki da na murya.

"Amatullah rayuwar da kika zaɓa wa kanki ke nan kuma ki na tunanin wannan hanyar da kika kai hanya ce mai ɓullewa?. Tun ranar da muka wayi gari babu ke tun daga wannan ranar ba mu ƙara yin bacci cikin salama ba, duk ranakun duniya kanmu muke zargi akan duk wani halin da kika tsinci kanki a ciki, kan mu muke ɗaura laifi tare da lashen takobin nemo a duk inda kike a cikin duniyar nan matuƙar ki na numfashi". Shi ma ya dasa aya a zantukansa ya juya ya bi bayan Yaya Alhassan ransa a matuƙar ɓaci idanunsa sun kaɗa sun yi jajir da su tamkar wanda aka watsa masa tsakin garin niƙaƙƙen barkono a cikin idanunsa.
Ji na yi kaina ya yi dum tamkar wacce aka ɗaura wa dutsen zuma. Na soma kokuwa da numfashina da yake maƙale mini a ƙirjina da na ji kamar an sanya taɓarya an tokare mini ƙirjin, jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa dole na tashi daga wajen sa boda hanya shiga da fita da mutane suke ta zirga-zirga a wajen. A hankali na soma tafiya bayan na ɗauki hanya komawa cikin ɗakin da na fito yayin da zantukan Yaya Alhassan suke yi mini amsa-kuwwa a cikin kunnuwana tamkar a lokacin kalaman suke ratsa tsakanin leɓɓansa suka fitowa a wannan lokacin.

Ko da na iso ƙofan ɗakin sai na dan yi jim ina daidaita nutsuwata kafin na turo ƙofar ɗakin na shiga bakina ɗauke da siririn sallaman da ya tsaya iya kan leɓena.
Ba su amsa mini ba illa zuba mini ido da suka yi kaman yau suka fara ganina kaina na rusunar ƙasa sa boda na rasa ƙarfin gwiwan da zan iya haɗa ido da su. Jikina ya soma rawa da hakan a tursasa mini durƙushewa akan gwiwoyina ina wani kuka mai tsananin ƙarfi duk yadda na so na yi magana bakina ya ƙi haɗin kai wajen lanƙwansa harshena balle har sautin maganan ya fita ta yadda za su iya ji abin da na furta.
Gabaɗayansu suka yi shuru babu sautin da yake tashi a ciki ɗakin face sautin kukan da nake yi mai matuƙar cin rai na ɗau lokaci ina kukan tamkar raina zai yi bankwana da gangar jikina kafin can na tsinkayo amon muryan Yaya Alhassan a kaurare ciki tsare gida babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da shi.

"Ki hanzarta ki sanar da mu hukuncin da kika yanke, don mu ma mu san inda dare ya yi mana".

Sai da na ja dogon numfashi mai nisan zango kafin na sama zarafin raba tsakani haƙwarana da suka manne da juna tamkar waɗanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu.
Cikin raunin da yake fito wa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ba tare da wani shamaki ba na ce"don Allah ku yi haƙuri ku yafe mini na san na baƙan zuciyoyinku....". Ya ɗaga mini hannu alamar ba ya son jin wani abu daga gare ni.
"Ba wani dogon jawabi muke buƙatar ji daga gare ki ba Amatullah. Hukuncin da kika yanke kawai muke son ji shin kin zaɓa ki ci gaba da rayuwa a nan inda muka same ki, ko kuma za ki haɗa kayanki mu koma gida gaban iyayenmu mu rayu cikin farin ciki da sanyawar albarkarsu a gare mu? Don ke yanzu ba yarinya ba ce babu wanda zai yi miki dole balle har ya tursas ki ki aiwatar da abin da ba kya ra'ayinsa". A kufule ya ƙare zancen cikin zafin rai tamkar zuciyarsa za ta fito waje tsabar tafasar da take yi, lamarin da ya ƙara azalzalan ruhina hawayen da nake yi suka ƙara karfin gudu suna zuba daga cikin idanua tamkar bakin indararo.
Chapter 49 · 0% Book details