Sashe 64
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Watarana mu ma haka za a tuna mu, a lokaci da muka gushe daga cikin duniyar".
"Allah ya yi mana mai kyau". Ta furta yayin da take ɗaukar hijabinta ta saka muka fito, a ƙofar gidan muka iske Yaya Alhassan take ya soma faɗan me yasa zan jawo Amira ta fito raka ni alhalin na san ita ta matar aure, sai da na ba shi haƙuri kafin ya saduda ya yi sanyi. Haka muka yi sallama da Amira ba don ranmu ya so ba muka tafi bayan na yi mata alƙawarin ƙara zuwa nan ba da jima wa ba.
Bayan mun koma gida har na yi shirin kwanciya na ji wayata ta soma ruri na yi caraf na ɗaga ƙiran tare da amsa sallamar da ya yi mini na ɗaura da faɗin"ko ba ka ƙira ni ba dama ina da burin ƙiranka yau".
"Ko dai sakamakon jiran da aka ce na yi za a sanar min? Yanzu na tashi na je na yi alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu na roƙi Allah ya ba ni juriyar ɗaukar duk irin amsan da zan ji ya fito daga bakinki".
Na É—an lumshe idanuna kafin na buÉ—e ina faÉ—in"ba abin da kake tunani ba ne, daman ina son ganinka ne gobe akwai maganar da nake son mu tattaunawa da kai".
"FaÉ—a naki cika wa nawa. In sha Allah goben zan zo ni da wuri ma kuwa".
"Na gode Allah ya kai mu".
"Amin". Ya amsa da shi daga muka yi shuru dukkanmu sai can na ji ya ce"Aryan da Ayan su na tambayarki". Na yi firgitit na buÉ—e idanuna da na lumshe su"wai kana nufin har yanzu ba su manta da ni ba?".
"Ƙwarai kuwa don kusan kullum sai sun yi maganarki, tun bayan gano gaskiyan da muka yi game da Altine wanda hakan ya faru ne ta dalilinki. Amatullah kin zama silar bayyanar haske a cikin rayuwarmu kin cuce rayuwar su Ayan daga zalunci, cutarwa da kuma ha'incin da Atline ta daɗe tana aikatawa gare su ta ƙarƙashin ƙasa. Tabbas idan abubuwa ya daidaita ma Anty Muhibbat za ta zo da kanta ta yi miki godiya har gida sai dai a yanzu ta ce kunyarki take yi".
"Wani irin kunya ke nan?".
"Kunyan abubuwan da ta yi miki mana".
Na saki taƙaitaccen murmushin da ya tsaya iya kan leɓena kafin na ce"don Allah ka sanar da ita cewar tarin alkhairan ta gare ni sun shafe komai. Ta riƙe n bisa gaskiya da kuma zuciya ɗaya ba ta taɓa yi mini wani abun cutarwa ba don haka bai kamata ta ji kunyata ba". Da alama ya ji daɗin zantukan da na jero don ina jin yadda yake ta sauƙe ajiyan zuciya wani na bin wani.
"In sha Allah zan sanar da saƙonki a kumnuwanta".
"Amma da san da cewa ka na zuwa gidanmu?".
Cike da ƙwarin gwiwa ya mai do mini da amsa"ƙwarai kuwa hasalima ita ta ba ni ƙwarin gwiwan tunkaranki don ita ma kanta ta yaba da nutsuwa, hankali da kuma riƙon amananki". Lamau na yi tamkar mai bacci har sai da na ji ya ci gaba da maganan"amma ko zan iya sanin dalilin ƙiran da ake yi min na gaggawa kafin goben?".
"Me kake ci na ba ka na zuba? Allah dai kawai ya kai mu goben ko ma mene ne ai za ka ji".
"Haka ne kam".
Mun ɗan taɓa hira kafin muka yi sallama da wuri na kwanta, don ina so na tashi na yi sallan dare kamar yadda na saba. Washe gari ban sanar da kowa zancen zuwan Saifullah sai dai kawai ina zaune a ɗaki Anty Sawwama ta ɗago labulen ɗakin.
"Sai ki fito ki na baƙi". Gabaɗaya na manta da cewar mun yi magana da Saifullah mussamman da na ji ta ce baƙi maimakon ta ce baƙo.
"Wasu baƙi kuwa? Ba wasu baƙin da muka yi da su za su waje na yau".
"In ki ka fito ai za ki gan su, a nan ne za ki gane kin san da zuwansu ko akasin haka". Ta dasa aya a nan ta saki labulen ta yi ficewar ta, ta bar ni saƙa da warwara a cikin raina. Haka na tashi na saka hijabina na fito ina saka ƙafana a cikin falon Ayan da Aryan suka rugo da gudu har suna karo da juna suka rungume ƙafafuna. Tsugunawa na yi a gabansu ina shafa fuskokinsu don tabbas Allah ya jarabce ni da wani irin zafafan ƙaunar yaran wanda hakan ya samu asali daga soyayyar da nake yi wa duk wasu ƴan biyu musamman masu kama iri kwabo da kwabo ɗin nan.
"Yaushe ku ka zo?".
"Ba mu daÉ—e da zuwa ba, tare da Uncle Saif muka zo mu. Kuma Umminma ta ce in mun zo mu gaishe da ke sosai sosai". Aryan ya yi zancen har yana kwaikwayon muryar Umminsu.
"Ina amsa wa ni ma in kun koma ku ce ina gaishe ta". Kansu suka gyaɗa mini alamar sun ji da hakan ya sa ni tashi tsaye na riƙon hannunsu muka ƙarisa cikin falon, Yaya Alhassan ne da Umar sai kuma Anty Sawwama yayin da gefe guda kuma Saif ne zaune Muhammad Taufik yana kusa da shi suke ke nan a cikin falon. Sai da na zauna na gaishe su suka amsa take na ji tausayi da tunanin halin da Muhammad Taufik zai shirga bayan na aikata abin da zuciyata take ingiza ni na yi. A zahiri hankalina yana kan su Ayan da suke ta zuba mini suturu sai dai hankalina yana kan hirar da su Yaya Alhassan suke yi, har zuwa lokacin da Saif ya ce zai je ya kai Muhammad Taukif filin jirgi don jirgin ƙarfe goma sha ɗayan rana zai bi zuwa cikin Abuja.
Ya yi sallama da Anty Sawwama yayin take ta sa masa albarka da yi masa addu'ar Allah ya sauƙe shi lafiya.
A nutse muyarta can ƙasan maƙoshina na furta"Allah ya sauƙe ku lafiya mun gode da ziyara". Caraf idanuna suka sauƙa cikin na Muhammad Taukif, shi ya fara janye na sa idanun ya na amsa da kalmar Amir yayin da suke fice wa daga cikin falon.
Na kwashe su Ayan muka shige cikin ɗakin har muka fito na ɗaura girkin rana na gama na yi alwalan sallan zuhur na yi sallan, ina zaune kan sallayan yayin da su Ayan suke gefe na suka cin abincin da na saka musu. Na ji wayata ta soma ruri na yi hanzarin ɗauka tare da ɗaga ƙiran, maimakon amsa sallamar da na yi sai ji na yi an sauƙe ajiyar numfashi mai ƙarfin sauti.
"Ina ga dai matar nan kin manta da cewar ki na da baƙo ko?". Na dafe goshina kafin na ce"afuwan na ji tunanin ba ka dawo ba ne ai".
"Na dawo ina ƙofan gida ina jiranki za ki fito ne ko kuma na shigo?". Da sauri na ce"A'a ka tsaya a nan zan fito". Sai da na yi maganan sai kuma ni da kaina na ji kunya na katse ƙiran na tashi na je wajen ajiye kayana na ɗauko jakar da na sanya memory card ɗin nan a cikin na ɗauka.
"Ku zauna a nan ba ri yanzu na je na dawo kun ji".
"To". Suka haÉ—e baki wajen amsa wa da hakan ya ba ni damar fita, ban iske kowa a falo ba hakan ya ba ni salama da nutsuwar fice wa wajen kaina tsaye. Ina fitowa na hango shi tsaye a jikin motarsa yana latsa wayarsa. Da sallama É—auke a bakina ya amsa mini yana É—ago kai tare da kafe ni da ido bayan ya mayar da wayan cikin aljihunsa.
"Ki bar Bawan Allah Saifullahi marayan Allah yana ta jiranki a cikin rana".
Na sadda kaina ƙasa"ai ka dawo da ka shigo ciki".
"Kayya! Wallahi kunyar Anty nake yi shi yasa kawai na tsaya a nan, yanzu dai ina sauraronki don jiya na kwana cikin zaƙuwa". Na ɗan tsagaita kafin na miƙa masa memory card ɗin da yake hannuna ya karɓa yana jujjuya shi a hannunsa.
"Wannan fa na mene ne?".
"Ina so idan ka je gida ka nutsu ka saurare abin da yake cikinsa da zaran ka gama saurara sai ka ƙira ni mu yi magana".
Shuru ya yi kallona kamar mai nazari ko kuma son gano wani abu, sai can ya ce"to shi ke nan ba matsala". Ya ƙare zancen yana cira wa a cikin aljihunsa.
"Yanzu za ku wuce ne?".
Ya waro idanununsa tar a kaina"to fa! Kora da hali ake yi mana ke nan? To shiga ki kwaso min su mu wuce". Kunya ya lulluɓe ni har sai da na rufe fuskana da tafukan hannayena.
"Ba fa haka nake nufi ba, na ga su Ayan abinci suke ci ne shi yasa na tambaya".
"Su sun sama karramawa ke nan tun da har girki aka yi musu. Saɓanin ni ɗan marayan Allah da aka shanya ni a tsakiyar rana aka manta da kashi na".
"Wallahi Yaya Saif ba haka ba ne ban san ka dawo ba ne.....". Ban ƙarisa zancen ba sa boda yadda ya tsare ni da idanunsa har sai da na ɗan tsorita na ce"lafiya kuwa?".
Ya ja dogon numfashi mai nisan zango kana ya furta"don Allah ƙara ƙiran sunan na ji, sai na ji kamar babu wanda ya kai ki iya furta sunan daidai. Ban taɓa jin an ƙira sunan da na ji daɗinsa irin haka ba, don Allah ki ƙara faɗa ko sau ɗaya ne".
Na ɗaga ido na saci kallonsa daidai lokacin da yake ƙara faɗin"Please mana".
"Cewa na yi Yaya Saif". Ina furtawa na juya da sauri na shige cikin gida muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana ƙoƙarin fitowa da mashin ɗinsa na yi saurin ja da baya na ba shi hanya yayin da kunya ya gama mamaye ni har na kasa ɗago idanuna, sai da ya gama fito da mashin ɗin na sama hanyar shiga ciki.
Na koma wajen su Ayan na iske su har sun gama cin abincin, ina zama ƙiran Saif ya shigo cikin wayata na ɗaga ƙiran na ba wa Aryan na ce ya yi magana.