← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 72

Sashe 59

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaina na jinjina da ƙyar na furta"to in sha Allah". Sai da na yi masa sai da safe kafin na tashi na tafi ɗakina ina shiga na zube akan katifar ina kuka mai ci rai, gabaɗaya jikina ya yi la'asar na rasa gane abin da yake damuna haka na kwana idanuna biyu ba tare da na runtsa ba. Washe garin ranar na tashi tamkar majinyaci komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar da shi.
Ina zaune a waje na tisa kwanon karin kumallo a gaba na ka sa kai ko da loma guda cikin bakina, Anty Sawwama ta fito har ta tsaya a kaina ban sani ba har sai da ta yi magana kafin na dawo cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da nake yi.
"Amatu lafiya kuwa? Kin tisa abinci a gabanki tun ɗazu kin kasa ci. Ke ba ki ci ba ke ba ki tashi ba". Sai na haɗo jarumta na yaɓawa kaina kafin na iya raba tsakanin leɓena na ce"babu wani damuwa Anty". Daidai lokacin da Yaya Alhassan da Amir suka suka fito daga cikin ɗakin kwanansu duk da kaina ya na ƙasa hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsa suna kaina ni yake kallo har zuwa lokacin da suka durƙusa suka gaishe da Anty Sawwama ta amsa musu cikin sakin fuska da kuma tarin albarka gare su.

"Alhassan ka zo ina son magana da kai". Anty Sawwama ta yi zancen idanunta akan Yaya Alhassan da ya amsa da to yana tashi ya bi ta suka shiga ciki. Zaman da Amir ya yi kusa da ni yana jan kunne abincin gabansa shi ya tursasa mini ɗago kaina ina kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce"abincin ne bai yi miki ba, ko kuma dai yanayin ne kawai?". Sai da na tsame hannuna daga cikin kwanon abincin kafin a taƙaice na furta"na ƙoshi ne".
"Me kika ci da har kika ƙoshi? Za ki zage ki ci abincin nan ko kuma sai na yi ɗura miki da ƙarfin tsiya". Na ɗago kai muka haɗa ido ya kashe mini ido guda yana yalwata fuskarsa da kyakykyawan murmushin da har sai da dake tsakanin haƙwaransa suka bayyana. Murmushin dole na sakar masa ina tsoma hannuna a cikin abincin muka soma ci tare da shi mu na ci yana ja na da hirar da amsana ba ya wuce uhm ko hmm haka har muka gama cin abincin na ɗauki kwano na je na wanke na dawo na zauna.
Ina zama Yaya Alhassan ya fito daga ganawan da suka da Anty Sawwama na bi shi da kallo na ga idanunsa gabaÉ—aya sun haÉ—a sun yi jajir gabaÉ—aya yanayinsa ya sauya haka ya fice daga cikin gidan ba tare da ya yi mana kallo azurki ba balle ya ce da mu wani abun.

Muka taka shi da kallo daga ni har Amir har ya fice kafin Amir ya furta"an ya lafiya kuwa? Na ga ya fito duk yanayinsa ya sauya". Na É—age kafaÉ—una alamar ban sani ba.
"Bari ki ga na bi shi na ji ko lafiya". Ya yi zancen yana miƙe wa ya bi bayan Yaya Alhassan, numfashi mai nauyi na sauƙe ina ɗan lumshe idanuna. Haka aka yi sati biyu a jere ba ranar da za ta fito ta faɗi Yaya Alhassan bai tambaye ni akan na goge sautin murya da hotunan nan ba, na kan ce da shi na yi hakan duk da kuwa har zuwa wannan lokacin na gaza goge su.
Ba na manta wata ranar juma'a wanda daga wannan ranar tubalin baƙin ƙaddarar rayuwata ta soma, da yammacin ranar Anty Zulaihatu ta zo ta gidan tare da mijinta Mu'azzam domin duba Anty Sawwama kasancewar ba ta ji daɗi a cikin kwanaki, ina ɗaki na ji shigowarsu na fito na gaishe su. Tun da na fito na lura da wani kallon ƙyaman da Yaya Mu'azzam yake yi mini har wani taɓe baki yake yi tamkar wanda ya yi arba da kashi, haka kawai na ji gabaɗaya jikina ya mutu murus har ya tashi ya fita akan zai je da dare ya dawo ya ɗauki Anty Zulaihatu na kasa ɗaga kaina. Zuwan Anty Zulaihatu ya ɗebe mini kewan da nake cikinsa sa boda ba na fita ko nan da can kullum ina cikin ɗakin.

Bayan sallan magrib Yaya Mu'azzam ya ƙira ta yana sanar da ita ba zai sama daman zuwa ya ɗauke ta ba, ta hau adaidaita kawai ta koma gida. Ƙarfe takwas saura na dare na fito na raka ta domin ta hau adaidaita muna tafe muna ɗan taɓa hira har sai da muka iso bakin titi kana ta sama abin hawa, muka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zuwa gidanta cikin kwanan nan.
Sai da na ga wucewan mai adaidaitan kafin na juyo domin komawa gida. A hankali nake tafiyar kaina a ƙasa tamkar wacce take neman wani abu a ƙasan haka har na iso ƙofar gida ina ɗago kaina na ga an dalle mini ido da hasken mota har sai da ya kai munzalin da na kai tafukan hannuna na kafe idanuna. Sai da aka kashe hasken na ga motar ta nufo inda nake na cira kaina ina kallonta sai dai na kasa gane inda na san motar.

Hakan ya sa ni soma tafiya zan shiga cikin gida na ji an ambaci sunana cikin sakakkiyar murya.
"Amatullah". Da hanzari na juya don tabbatar da mamallakin muryar take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saifullah da yake tsaye jikin motan yana kallo na kamar yadda ni ma na zuba masa idanuna. Ya tako ya iso inda nake tsaye.
"Kin wuni lafiya?". Bambarakwai na ji tambayar tasan wai na miji da suna Hajara, na ja dogon numfashi na fesar a ƙoƙarin daidaita nutsuwata kafin na ce"idan wajen Yaya Alhassan ka zo to bai dawo gida ba tun da ya fita sallan isha'i". Tun kafin na dire zancen ya katse ni"wajen ki na zo".

"Waje na kuma?". Na maimaita zancen ina yi masa nuni da kaina.
"Ƙwarai kuwa wajenki na zo ni Amatullah, idan da hali ma magana nake so mu yi mai matuƙar muhimmanci. So samu ma mu nema waje mu zauna".

"Ka faÉ—i duk abin da za ka faÉ—a, ina sauraronka".

"Ki yi haƙuri mu shiga cikin mota sai mu yi maganar". Na ɗaga masa hannuna"ka gaggauta faɗin abin da ya kawo ka, idan kuma ba ka shirya to ni zan koma ciki don ina da abin yi". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kafin ya ce"Amatullah ban san yanda za ki ɗauki maganar da zan furta miki a yanzu ba, amma ina so ki sani duk abin da zai fito a bakina a yanzu to daga ƙasan zuciyata yake fitowa kai tsaye kuma iya tsagwaron gaskiyata nake sanar da ke. Tun ranar da na san wace ce ina nufin asalinki da kuma tarihin rayuwarki tausayinki ya maƙale a cikin raina, a duk san da na zauna ba na komai to tunaninki ne da irin abubuwan da na aikata miki yake addaban raina. Yau na zo ne don na furta miki kalmar da ban taɓa furtawa wata ƴa mace ba tun da nake a rayuwata".

Cike da ƙosawa da sauraronsa na ce"ka tafi kai tsaye ga zancen da kake son furta wa".
Ya ɗan yi jim tare da sadda kansa ƙasa yana murza zoben azurfan da yake saƙale a ɗan yatsan hannunsa kafin can ya ce"Amatullah ina sonki, ina fata da burin ki kasance mata a gare ni sannan uwa ga ƴaƴana". Tun da ya soma maganar na kafe shi da idanuna ina ganin tamkar mafarki nake yi ba a farke nake ba.
"An ya ka san abin da bakinka yake furtawa kuwa? Ko kuwa dai ka mance wacce take tsaye a gabanka ne?". Ban jira amsar da zai ba ni ba na ci gaba da zancena cikin ƙonar zuciya da tafasan rai.
"Idan ba ka gane ni na yi mata tuni ni ce fa Amatullah wannan É—iyar da ka zargi tarbiyyarta. Wacce ta yi ciki ba tare da aure ba wacce ta tafi can uwa duniya ta yi rayuwa ba tare da tsawatarwan iyayen ba. Wacce ta yi zaman kanta a cikin tsakiyar gidan karuwai ta ci gashin kanta da kanta. Wannan yarinyar da ta mayar da É—akin otel tamkar É—akin kwananta, wannan yarinyar marar tarbiya da nutsuwa. Wannan yarinyar da kake shakku da kokonton kasancewar ta kusa da ahalinka". Na saki murmushin takaici kafin na ci gaba daga inda na tsaya.

"Shin ko ka manta ku rayuwarku a tsaftace take? Ba ku da wani abun aibu a tattare da ku shin ka manta ikirarin da ka yi na cewar Allah a raba ku da kaidina?. Yadda kake mutumin ƙwarai kuma kamili ai da matar ƙwarai ka dace wacce ta fito daga gidan tarbiya da halin girma. Saifullah kar ka yaudari kanka da neman soyayyarta domin bayan rashin dacewan da muka yi da juna ba zan taɓa iya cusa sonka a cikin zuciyata da ka zama silar raunatata ba. Na roƙe ka idan ma ɓatan hanya ka yi ko kuma tuntuɓe harshe ka samu to kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan, babu wani abun da ya rage tsakanina da ku". Na ƙare zancen cikin rauni ina haɗe hannayena wajen guda alamar, zai yi magana na katse masa hanzari.

"Don Allah ka bar ƙofar gidan nan wallahi ba na ƙaunar ganinka. Ka yi wa girman Allah ka bar ƙofan gidan nan".
Chapter 59 · 0% Book details