← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 72

Sashe 41

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da ruÉ—u Hajiya Muhibbat ta ce"wani irin magana kike faÉ—a haka Altine? Anya ki na cikin hankali da hayyacinki kuwa? A ina kika ji wannan maganar?".
"Hajiya ina cikin hayyacina sannan hankalina ma yana nan tare da ni har ki yi imanin cewar wai ba na cikin hayyacina. Da kunnena na ji Yallaɓai Saif yana tuhumarta akan wannan zancen, kuma shi ma ya san da wannan zancen ga shi a tsaya ki na da damar da za ki tambaye shi idan har ba ki yarda ba".

"Saifullah me ye gaskiyar abin da Altine take faɗa? Shin da gaske ne Amatullah karuwa ce kuma zaman kanta take yi a cikin gidan karuwai da ƴan daudu?". Runtse idanunsa ya yi yana cije leɓansa tare da zuba hannayensa cikin ajihun wandon farin shaddan da yake jikinsa.

"Kai nake sauraro Saif". Maganar da ta yi a karo na biyu ya sanya shi buɗe lumshashshun idanunsa muryarsa can ƙasan maƙoshinsa ya soma maganar a hankali.
"Anty haka ne a cikin gidan karuwai take rayuwa amma akwai wani abu guda wanda ba mu san da shi ba......". Ban bar shi ya ƙarisa ba ta yi wuf na amshe zancen yayin da nake tashi tsaye daga faɗuwar da na yi akan hannuna.

"Kar ki tsawaita bincike a kaina Hajiya don ina da tabbacin binciken ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba, babu komai a cikin tarihin rayuwata face ƙunci, tashin hankali da kuma ruɗani. Ƙaddarar rayuwata ta bambanta da na ko wacce yarinya mai irin shekaruna. Tun kafin na yi girman bambamce tsakanin fari da baƙi na san mene ne baƙin ciki kuma na san ɗanɗanonsa, babu kuskure a cikin dukkan abin da Altine ta faɗa tabbas haka ne a cikin gidan karuwai nake rayuwa kuma zaman kaina nake yi ba a gaban iyayena, ƴan uwa ko dangi nake ba gashin kaina nake ji babu kwaɓa babu mai tsawartawa balle wanda zai kama hannuna ya ɗaura ni a hanyan da take daidai. Sai dai tun da nake ban taɓa aikata zina ban taɓa kusantarsa sai dai na yi imanin cewa dukkanin wani Bawa ba ta taɓa wuce ƙaddararsa".

"Babu wani mai hankalin da za ki faɗa wa wannan maganganun ƙanzon kuregen nakin ya yarda da ke. Ta ya ya za a ce kin rayu a cikin tsakiyar karuwai ba tare da ki na aikata abin da suke yin ado da shi ba, to in ma haka ne ba ki aikata ba ɗin me ye kike zaman kanki?".

Na runtse idanuna da hakan ya ba wa hawaye. Da sur ciki mini kurmin idaniyata damar kwaranya, ina jin wani zafi a cikin raina tamkar ana watsa mini tafashashshen ruwan dalman da ba sirka shi da komai ba a cikin farfajiyar ƙirjina.
"Ban faɗa don neman yardarki ba sannan ban damu da ko wani irin kallo za ki yi mini, Abu ɗaya na sani kuma a kansa zan tsaya har ƙarshen rayuwata shi ne iya gaskiya ta na faɗa muku. Hajiya ina mai ba ki haƙuri akan ɓoye miki gaskiyar wace ce ni da na yi har tsawon wannan lokacin, haƙiƙa a ɗan zaman da na yi da ke na ga zallar ƙauna da tausayinki a gare kwance a cikin idanunki. Ban yi hakan da wani nufi ba kuma Allah shi ne shaida ta akan hakan.....".

"Ya isa haka ya isa Amatullah".

Hajiya Muhibbat ta dakatar da ni ba tare da na gama amaryar da zancen da yake kan harshena ba.
"Mai zaman kanta? Kin san ma'anar wannan kalmar kuwa Amatullah? Kin ba ni mamaki matuƙar ina miki kallon mai hankali da nutsuwa wacce ba ruwanta ashe kallon biri nake yi miki ki na yi min na ayaba. A ƙananun shekarunki har kin san ki sanya ƙafa ki baro cikin gidan iyayenki ki zo inda ba ki san kowa ba kuma ba wanda ya san ki ki fara zaman kanki. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wace iriyar rayuwa ce muke rayuwa a cikin ta haka? Me yasa masifu da bala'i kala-kala ba za su baibaiye al'ummar mu ba?". Ta tsagaita tare da yarce ruwan ƙwalla da ya zubo daga idanunta kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya.

"Daga yau ba na son na ƙara ganin ki a kusa a gidan nan balle kuma ki tsaya a jikin gidan nan, na sallame ki ki ƙara gaba niyyar da taimakon da na yi Allah ya ba ni ladan niyya ke kuma idan mai shiryuwa ce Allah ya shirya ki. Ga kuɗin aikinki". Ta ƙare zancen tana zige jakarta ta ciro wasu kuɗaɗen da ko tsaya wa ƙidaya su ba ta yi ba, ta watso mini su a fuskana.
Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina na cira kai na dube ta sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na sama zarafin magana.
"Duk magangunin akan turban gaskiya kike amma ke ma ina son na sanar da ke wani abun da ba ki sani ba. Kamar yadda rayuwata take cikin hatsari haka ke ma ta ki rayuwar da ta Æ´aÆ´anki take cikin hatsari sanadin yarda da amincin da kika É—aura akan mutane guda biyu da kike ganin sun fi kowa kusanci da ke a cikin wannan duniyar".

Na ƙara taku uku na matso kusa da ita sosai da tun da na soma maganar take bi na da kallo cike da maɗaukakin mamaki da ya haɗu da al'ajabi. Kafin na yi magana ta ri ga ni.
"Wasu mutane biyu kike magana a kai?".

Na saki wani bushashshiyan dariyar da ba ta da alaƙa ta kusa ko ta nisa da nishaɗi kafin na furta"mutum na farko shi ne mijinki wanda a tsakanin gobe da jibi zai shigo cikin ƙasar nan ba tare da saninki ba, kuma ina da tabbacin har ya zo ya koma ba zai nema inda kike ke da ƴaƴanki ba. Sannan mutum na biyu ba kowa ba ne face Altine ƴar aikin da kika riƙe tamkar ƴar uwa kika busa mata iskar ƴancin yayin da ita kuma take amfani da yardar da kika yi mata take cutar da ke, ke da ƴaƴanki". Na ƙare zancen ina yi mata nuni da Altine da ƴar manuniyar ƴatsata.

Ban gama rufe bakina na ji sauƙar wani gigitaccen mari a bisa kuncina har sai da na soma ganin gilmawar baƙin duhu a cikin idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi da ƙyar na iya sarrafa kaina na tsaya akan ƙafafuna. Ta cakomo wuyar hijabina ta riƙe tamau.

"Ke har me ye kika sani akan mijina da za ki faɗa wannan maganar akan sa? Sannan yaushe kika zo cikin gidan nan da za ki gaya min wace ce Altine? Babu wani halinta wanda ban sani ba ta kai ta kawo ko ba ta furta magana da bakinta ba ina ya fahimtar abin da take nufin. Ina kika sama ƙwarin gwiwar nan?".

"Tabbas ban san mijinki amma a yanzu na san abubuwan da ke ma kanki ba ka sani ba game da halinsa. Idan ba ki yarda da abin da nake faÉ—a ba za ki iya samunsa ranar juma'a a babbn otel É—in da ke cikin garin Abuja. Batun Altine kuma za ki iya tambayar Æ´aÆ´an idan tsoro bai hana su faÉ—a ba".

Mamakin furucina ya sanya sakar mini hijabina da ta riƙe.
"Saifullah ka kawar min da yarinyar daga gabana, tun kafin zuciya ta É—ebe ni na lahanta ta na kashe banza na kashe wofi. Ba na son na buÉ—e idona na gan ta a gabana".

Sai a lokacin Saif ya yi magana da tun É—azu yake tsaye a wajen yana bin mu da kallo ba tare da ya ce uffan ba.
"Anty don Allah ki kwantar da hankali, mu saurare abin da za ta ce wataƙila mu dace da wani ilmin da mu kanmu ba mu san shi ba".

"Saif babu wani mahalukin da zai tsaya a gabana ya sanar da ni wani hali na Saddam wanda zai Muhibba ban san shi ba, a cikin tsawon zaman da muka yi da shi. Balle kuma Altine duk ranar duniya take muke kwana mu tashi a cikin gidan nan, ka fitar min da yarinyar nan daga cikin gida".

Cikin in-i-na Altine ta ce"wallahi ƙarya ma take yi min ba ni da wani mummunan halin da na ke ɓoye miki shi".

Cikin ba da umarni Saif ya ce"Altine É—auki su Aryan ki shiga ciki da su".

"To ranka ya daÉ—e". Ta amsa da shi cikin bin umarni da girmamawa, ta kwashe su Aryan suka yi cikin gida. Zai yi magana na tar numfashinsa.
"Zan fita ba sai ka fitar da ni ba, Hajiya ko ba ki ce da ni kar na ƙara zuwa cikin gidanki ba ni ma daman ina da niyyar sallamar kaina daga wannan aikin, sai dai ina mai ba ki shawara da ki nutsu ki yi nazarin abubuwan da na sanar dake yanzu. Ko ba daɗe ko ba jima watarana za ki neme ni ki kuma gode mini". Tas na ji ta kuma ɗauke ni da wani marin mai matuƙar sauti a karo na biyu.
Na kai hannuna na dafe kuncina ina cije leɓena sa boda zafin marin da ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina ya kuma raunana ƙarfin jiki da zuciyata.

"Na gode ranki ya daɗe, na gode bisa halin girma da karamcin da kika nuna mini". Ina dasa aya a nan na sunkuya na kwashe kuɗin da ta watsa mini don na san su ɗin haƙƙina, na raba biyu na ɗauki ɗaya na damƙa mata ɗayan.

"Na ɗauki iya haƙƙina ga ragowar dukiyarki".

Ban jira abin da za ta ce mini ba na fi tafiyata ina tafe hawaye duk yadda na so sarrafa kaina wajen ganin na tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga kurmin idanuna lamarin ya gagare ni. Na buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin zan fita muryar Baba Mai Gadi ta tilasta mini dakatawa.

"Ƴar nan kar ki tafi ba tare da kin warware min ƙullin zantukan da na ji ku na musayarsu ba. Shin da gaske ne abin da Altine ta faɗa akan ki? Da gaske ke ɗin karuwa ce kuma zaman kanki kike yi?".
Chapter 41 · 0% Book details