← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 72

Sashe 31

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ya gaya miki? Yana da matarsa har da Æ´aÆ´a, sai dai ya ce min matar ba wani son ta yake yi ba don auren ma iyayensu maza ne suka haÉ—a".
Na saki ɓoyayyar ajiyar sa bsa yadda zantukan natan suka daki zuciyata tare da mummunan mini raina, na ji wani takaici yana taso mini tabbas in dai har abin da nake zargi ya tabbata to fa haƙiƙa akwai gagarumar matsala.
"Aikin me ye shi kuwa yake yi haka da yake iya yin kyautar irin waɗannan maƙudan kuɗin, sannan me ye sunansa?". Kallon da ta tsare ni da shi tun kafin na dire zancen ya sa ni fahimtar na zuga wa kwaɓata ruwa kuma na wuce gona da iri don ina ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa. Na ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya? Da hakan ya ba ta damar furzar da zancen da yake cikin bakinta.

"Wannan tambayoyin hakan wani na bin wani sai ka ce jami'ar ƴan sanda. Kin ga ni nan da kike ji da gani an sha ni na warke wallahi, don an yi min cin amana da zangon ƙasan da ba zan taɓa mantawa ba har zuwa lokacin da zan yi numfashin ƙarshe a rayuwata. A cikin gidan nan aka sama wata tsinananniya ta ɗauki lambar saurayina a cikin wayata ta ƙira shi ma da yake mai bakin uwa ne ya biye mata suka ci amanata, har ta kai ta kawo suna haɗuwa a otel ranar da labari ya iske kunnuwana kuwa na shirya na je ni har otel ɗin na gan su da idona. Sai dai ban yi sakaci na bari sun ganni ba, sai da na saita lokacin da suka saki jikinsu shi da ita wani rana ya zo har cikin gidan nan ɗakinta ba tare da sun san da cewar ina cikin gidan nan. Na dafa ruwan zafi na je na sheƙa musu ita da shi".

Tun da ta soma zancen nake bin ta bakinta da kallo har ta kai aya da hakan ya yi daidai sauƙe tagwayen ajiyan zuciyan da na yi ina zame hannayena daga tagumin da na zabga.
A taƙaice na ce"to Allah ya rufa asiri".

"Amin".

Shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"ba ni da saurin yarda da mutum tun bayar faruwar wannan lamarin, haka nan na ƙudurce a raina ba zan ƙara aminta da wata ɗiya mace ba ko da kuwa cikin ɗaya muke da ita. Sai dai ban san dalili tun ranar farko da na fara ɗaura idanuna akan ki a cikin gidan nan na ji kin kwanta min a cikin rai, na kuma ji a raina cewar zan iya aminta da ke har na ja ki a jikina".
Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na ce"me yasa kika yi mini wannan shaidar? Ba kya tunanin ni ma idan kika ja ni a jikin idan tafiya ta yi tafiya zan iya cin amanar da kika ɗauka kika ba ni?".

Wani shu'umin murmushi ta saka kana ta furta"ban ga alamar hakan a tattare da ke ba Amatullah, domin ido ba mudu ba ne amma ai ya san kima". Kaina kawai na jinjina tare da miƙewa tsaye na ce"bari na je na ɗebo ruwa na yi wanka kafin magriba ta yi".Ta yi caraf ta riƙo hannuna.

"Ai dai za ki tsaya na sauƙar da girkin ki ci kafin ki tafi ko?".

Na jijjiga kaina"kar ki damu a ƙoshe nake don ban daɗe da cin abinci ba".
"Ai ko yanzu kika tashi daga gaban kwanon abinci sai kin cin girkina, don haka kawai ki koma ki zauna idan ruwan wanka ne ki sha kuruminki ina da ruwa a É—akina sai na ba ki bokati guda".

"Kin dai matse ne kawai amma ba na jin yunwa".

"E dai na ji koma ki zauna". Ta yi zancen tana jan hannuna na zauna a inda na tashi, mun ɗan taɓa hira da ita kafin abincin ya tahu ta sauƙe ta ce na shirgar da shi ɗakin yayin da ita kuma take kashe ragowar garwashin.
Sai da ta gama ta shigo ta zuba mana abincin muka ci tare, ta matsa mini akan sai na ci gaba yadda take ta ja na da hirar da ba na gane kansa balle gindinsa. Haka muka gama abincin na tattaro kwanunkan zan wanke fafur ta hana ni, ta É—auki ruwa bokati guda ta ba ni na je na yi wanka na yi alwala na fito. Sanda na dawo kawo mata bokatin na iske ta tana waya don haka na ajiye mata na wuce É—akinmu.

Sallan magrib na gabatar na zauna a inda na yi sallan na karato wani sashi daga cikin haddan karatun alƙur'anin da yake kaina. Tunani kala daban daban suka ziyartar kwanyata amma ciki babu wanda ya fi jan hankalina tare da rikitar da ni sama da hoton Abbinsu Aryan da na gani a fuskar wayar Zinariya da kuma kalaman da ta yi mini.
Tabbas indai ba idanuna ba ne suka gano mini abin da ba shi ne ba ko kuma suka sama matsala gabaɗaya Abbinsu su Ayan mijin Hajiya Muhibbat ɗin dai na gani. Sai dai me ye haɗin sa da Zinariya kuma a ina suka haɗu da shi? Idan ban manta ba na taɓa jin Hajiya tana cewar mijinta ba mazauni ba da yake shafe tsawon lokacin ba tare da ya zo gida ba.

Ta gyara zamana ina ƙara yin zurfi cikin tunanin da nake yi tare da yin nisan kiwo cikin nazarin. Ta ina da zan fara wannan yaƙin balle har na ci galaba? Akwai tarin abubuwa a gabana da nake son cimma a cikin rayuwata, haƙiƙa sai yanzu na yarda da karatun da Amira take bi ya know na cewar dukkan maza halin su guda ne wanda hakan yake nufin ko wani gauta ja ne sai dai wanda bai ji rana ba. Na tashi na gabatar da sallan isha'i na zo na yi shirin kwanciya sai dai baccin ya ƙi zuwa haka na yi ta juye-juye har izuwa lokacin da bacci ya yi nasarar sace ni.
Kamar a mafarki na ji soma jin tashin sautin yana tashi daga cikin ɗakin, wanda hakan ya tilasta mini buɗe idanuna tare da sauƙe su akan Sha'awanatu da muke ɗaki ɗaya da ita.
Zaune take akan katifarta tare da wani saurayi suna manne da junan tamkar za su haɗiye junansu, kankana ne a gabansu yana yanka da wuƙa yana ba ta a bakinta yayin da take wani lumshe idanuna tare da gantsarewa.

Tsam na tashi tsaye ina rarumo hijabina na mayar da shi jikina da hakan ya sanya hankalinsu karkaro wa gare ni, Shaawanatu ta buga wani uban tsaki tare da kawar da kanta gefe.
"Wane ne wannan Sha'awanatu kika shigo mana da shi har cikin É—aki?".
Kamar wacce take jira na ce kule ta ce as, ai kuwa ta miƙe ita ma tana mayar mini da martani a zafafe"amma dai ai kin san da cewar ina da cikakken iko a cikin ɗakin nan, tun da kuɗi nake biya na kaya ba kyauta nake zaune ba kuma ba alfarma aka yi min ba. Yadda kike zaman kanki haka ni ma nake zaman kaina babu ruwa wani da wani kamar yadda babu ruwan biri da gada. Ina da ikon na kawo duk wani wanda nake so cikin ɗakin nan a duk lokacin da nake so kuma a duk sa'ilin da na ga dama idan buƙatar hakan ta taso".

Kalamanta suka É—ura mini takaici a cikin raina na cika na yi fam.
"Au! Haka ma za ki ce? Amma kin san da cewa ai ba ke ɗaya ba ce kike da iko da ɗakin. Akwai hakkina da hakan zai tauye mini shin ba ki yi tunanin hakan ba? A lokacin da ƙaramar curin ƙwaƙwalwar kanki take yi miki saƙa da mungun zare".

"Su haƙƙin manya. To ke ki na tunanin har wani haƙƙin kike da shi a cikin gidan nan? Ai yanzu kuɗinki shi ne mutumcinki tun da biya nake yi kamar yadda ke ma kike biya don kana ina da lasisin kawo duk wanda nake so".
Kalamanta suka sanya zuciyata ƙara tunkura raina ya ci gaba da tafasa na cije leɓena kafin na ce"ai kuwa zan ba ki mamaki, don wannan ƙatoton gardin ba zai kwana a cikin gidan nan ba. Idan suna son ku aikata baɗalarku ku tafi can wani waje ku je ku yi amma ba a cikin ɗakin nan ba".

"Ai kuwa kin yi kaɗan ki korar min kwastoma. Ko don ki na baƙin ciki da farin jinina ban kasance irin karfa ba da kare ba ya zuwa cikin ɗakin nan da sunan ya zo wajenta".

Ban tanka mata ba na soma waige-waige can na da hango wuƙar da suka yanka kankanan na yi hanzari na je na ɗauke ta.
"Ka za fita daga cikin É—akin nan ko zai na yi maka mummunan lahanin da ko uwar da ta haife ka in ta ganka ba za ta shaida ka ba. Ku je can wani wajen ku haÉ—u amma cikin É—akin nan kam sai dai gani sai dai hange".

"Ke Amatullah anya ki na da hankali kuwa? Wuƙa ce fa kika ɗauka".

Na juya ina nuna ta da wuƙar hannuna"idan kika ƙara ɗaga ƙafarki ki ka yi taku ɗaya sai na ɗaba masa wuƙar nan, ke ma na yi miki rauni sannan daga ƙarshe ni ma na kashe kaina. Dukkanmu mu ukun mu yi asarar rayuwarmu".
Cak ta tsaya a inda take ba tare da ta motsa ba ganin yadda na furzar da zancen babu alamar wasa a tattare da ni. Na nufin Saurayin na tan da yake tsaye cike da tsoro yana ta ƙif-ƙifta idanu tamkar shege a yayin rabon gado, yana ja baya ina nufar sa gadan-gadan har sai da ya kai ƙarshen ɗakin.
Sha'awanatu ta É—aura hannu a kanta ta soma kurma ihu da kururuwar neman agaji, kan ka ce kabo mutane suka cika gidan har da Hajiya Babba.
Chapter 31 · 0% Book details