← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 72

Sashe 24

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba-ba-ba-ba-ba babu". Na amsa masa a gajarce ina ɗaukar hanyar barin wajen cikin matuƙar sauti kamar zan tashi sama, har ƙafafuna suna haɗewa cikin doguwar rigan da ta gama jikina tsam tamkar tare aka halicce mu.
Kaina tsaye na wuce ɗakina na zubu akan tabarma ko kukan na kasa yi illa kawai soyar da zuciyata take yi mini. Ƙirjina yana yi mini wani irin zafi tamkar ana watsa wa mini garwashin wuta ta yadda nake jin zafin yana ratsa wa har ta cikin nama da jijiyoyin jikina. Kan ka ce kabo gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi har wani kakkarwa nake yi.
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!".

Shi kaɗai na yi nasarar furta wa kafin zuciyata ta antaya cikin cakwakiyar tunani. Tabbas ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan muryar Muhammad Taukif ne. Mutumin da ba zan iya mance da ranar da na far tozali da shi akan hanyata ta zuwa islamiyya da kuma kalamansa ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi a cikin rayuwata da zuciyata ta sama
nutsuwa da kalamansa tun kafin na san halayensa da ɗabi'un balle har na kai ga sanin haƙiƙanin wane ne shi.
In dai ta tabbata shi ne baƙon da na ji Saif yana batun zuwansa to ina cikin lukutin yanayi. Na yarce zuffan da ya kwanta a saman goshina kana na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba domin kai mata saƙon da aka bayar da sunanta.

Na zauna a ƙasa ina yi mata sannu da hutawa ta amsa tare da zarce wa da faɗin"to ya ya kika gan shi ina fatan ya yi miki?".
Na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ga wannan ya ce a ba ki". Na miƙa ledodin dukka biyu ta amsa tana faɗaɗa annurin fuskarta bakinta har kunne.
"Dukka wannan nawa? Amma mun yi waya da shi kafin shigowar ki ya ce ɗayan saƙon na ki ne. Don haka ga shi ke ma sai ki je ki fantama ki more wa ranki, don na san waɗanda zai ba ki gobe sai sun ci uban waɗannan".

Na girgiza kaina"Hajiya ba zan ci ko naira É—aya daga cikin kuÉ—insa ba. Don bai kwanta mini a raina ba, Hajiya kamar yadda kuka sa na yi abin da kuke so ni ma ina da nawa sharaÉ—in da dokoki. Ba zan fara mu'amala da kowa ba sai wani mutum guda".

"Wane ne wannan mutumin?".

Na ɗan yi jim kafin can na ce"Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe".

Ta dafe ƙirjinta tare da waro idanunta waje"Sheikh Dawood dai da na sani mai tafsirin Alkur'ani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e.
Ta kallo ni da wutsiyar idonta tana faÉ—in"ke yarinyar nan watau bayan taurin kai da kafiyar tsiya tamkar kafiran farko har da hauka ma akwai a cikin kanki. Yo in ba hauka ba ta yaya kike tunanin za a iya jawo hankalin irin wannan mutumin da addini da tsoron Allah ya ratsa jini da jijiyarsa".
"Ba zai yi wahalar shiga hannu ba Hajiya. Ni ko hanya ayi mini na gan shi ni kuma na yi miki alƙawarin sai na jawo hankalinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci"

Ta yi mini wani irin kallo irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce ta ja tsaki ta tofar tana mayar da hankalinta kan abin da take yi ta furta"bari Aminu ya damu mu yi magana tabbas akwai wani abu da yake yawo a cikin wannan kan nakin". Na cira kai na kalle cike da ƙwarin gwiwa na ce"babu komai a cikin kaina Hajiya, ki ba dama ni kuma na yi miki alƙawarin zan jawo shi har ya shigo hannu. Idan na gaza aikata abin da na furta na yarda ki haɗa mini kayana ki ɗaura mini a kaina ki kora ni daga cikin gidan nan sannan ki haɗa mini da ko wani irin wulaƙancin da kika yi niyya".
"Kin san me ye kika faÉ—a kuwa?".

"Ƙwarai kuwa Hajiya".

Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"shi kenan na ba ki dama amma idan kika kasa jan hankalinsa tabbas zan yaga miki rigar rashin mutumcin a bainar nasi, zan wulaƙanki irin wulaƙancin da ko kare ba zai ci ba. Zan tozarta ki irin tozarcin da za ki ƙwammace ina ma uwarki ba ta haifo ki kin zo cikin duniyar na ba. Zan muzanta ki irin muzancin da za ki zaɓi mutuwarki sau dubu akan rayuwarki. Zan jefa rayuwarki cikin ƙunci da takura da har sai kin daina jin daɗin rayuwar duniya sai kin ji a cikin ranki wanda yake kwance a cikin kabari ma ya fi ki ƴanci da walwala".

Ba tare da wani tunani ko dogon nazari ba na amsa da faÉ—in"ma yarda da duk wasu sharruÉ—an da za ki gindaya mini. In sha Allah sai na jawo hankalinsa".
"Kuma babu wanda zai taimaka miki ke kaɗai za ki yi wannan yaƙin. In ma ki ci in ma ki sha ƙasa". Na haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe tamkar ƙasar sahara a lokacin zafi.
"Na yarda da dukkan sharruÉ—anki Hajiya".

"Tashi ki je na sallame ki"

Ban ce da ita komai ba na tashi na bar cikin ɗakin na koma ɗakinmu, na zauna na buga wani uban tagumi ina jin gabaɗaya duniyar ta yi mini zafi na ja numfashi na furzar ya fi sau shurin masaƙi. Hawayen idanuna sun kafe ƙaf tamkar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe na tsawon shekaru masu yawan gaske, sai yanzu ma yarda tabbas wani tashin hankalin ya wuce a yi masa hawaye sai dai kukan zuci wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi.

A firgice Anty Sawwama ta farka daga baccin da ya cikakken ɓarawo har ya yi nasarar sace ta duk da girman tashin hankali da damuwar da yake cikin ƙalbinta da ta gama raunana. A tare Yaya Alhassan da Umar suka shigo cikin ɗakin, Umar ya kunna wutan lantarki take haske ya gauraye ko'ina.
"Umma lafiya kuwa me ye yake faruwa?". Kasa magana ta yi illa zuffan da ta ci gaba da haɗa wa tamkar wacce aka sheƙa wa ruwa ya yi mata jilif.
"Umar samu ruwa yanzu-yanzu". Da sauri Umar ya fita ya je ya ɗebo ruwan ya dawo ya miƙa wa Yaya Alhassan ya karɓa ya yi tufin wasu addu'o'i a cikin ya ba ta ta sha sannan ya shafa mata ragowar a fuskarta, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani. Umar ya riƙo hannunta ya sanya cikin nasa yana murza wa a hankali.

"Umma lafiya kike? Ki na jin abin da muke faÉ—a?".

Kanta ta gyaɗa alamar e tana zarce wa da faɗin"lafiya ƙalau wani mafarki kawai na yi da ya tsora ni ainun".
"Wani irin mafarki ne haka Umma?".
"Umar mafarkin nan dai da na saba yi a duk sa'ilin da na kwantar da haƙarƙarina da sunan bacci".

Cike da damuwa Yaya Alhassan ya ce"mafarki kike yi da Kawu Manniru ya zo yana tambayarki amanar Amatullah da ya ba ki ko?". Cikin sanyin jiki ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa har ta kai ta kawo ba na ƙaunar na kwanta bacci ko da kuwa na minti ɗaya ne. Ban san ina zan je da girman alƙawarin da Manniru ya bar min ba, Amatullah ina kika shiga ne a cikin duniyar?".

"Umma don Allah ki rufa mana asiri ki cire wannan damuwar daga cikin ranki kar wani jinyar ya same ki a dalilin hakan. In Sha Allah Amatullah za ta dawo gare mu cikin aminci da yardan Allah, ina ji a jikina duk inda take tana hannu mai kyau kuma ba za ta taɓa aikata abin da Allah zai yi fushi da ita ba, don duk cikinmu babu wanda bai yarda da tarbiyyan Amatullah ba. Ƙaddarar ta ce kawai ta zo a irin wannan sigar wanda babu yanda muka iya ba za mu iya guje mata ba balle mu sauya mata fasali. Har yau ba mu fasa neman ta ba ina da yaƙinin duk wani mai nema watarana zai dace Umma don haka ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe".
Numfashi mai zafi ya ja ta furzar daga bakinta kafin ta sama lasisin faɗin"hakan nake fata da buri Alhassan. Allah ya yi muku albarka ya jiɓanci lamuranku yadda kuke ƙoƙarin yi min biyayya ku ma Allah ya azurta ku da ƴaƴan da za su yi muku fiye da haka". Cike da jin daɗin furucinta suka amsa da amin, Yaya Alhassan ya sa Umar ya zuba mata ruwa a cikin buta ta je ta yi alwala kana su ma suka je duk suka yi alwalan, Yaya Alhassan ya ja su limanci suka gabatar da sallan raka'a biyu na
nafila suka miƙa ƙoƙon baran su zuwa ga sarkin da ba shi da abokin tarayya, Sarkin da ba ya ce a roƙo zai amsa.

Ba su bar cikin ɗakin ba har sai da bacci ya ɗauke ta suka kunna karatun alƙur'ani a waya suka ajiye a cikin ɗakin. Yaya Alhassan ya tisa ta a gaba yana kallon ta tamkar bai taɓa ganin ta ba. Umar ya dafo kafaɗarsa cike da kulawa yake faɗin"Yaya Alhassan ka kwantar da hankalinka komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba. Watarana sai dai labari".

"Umar idan na ce ba na cikin damuwa haƙiƙa ma yi ƙarya mai girma, tun ranar da Amatullah ta ɓace ban ƙara samun kwanciyar hankali ba, ban ƙasa kasancewa cikin daidaitacciyar nutsuwa ba. Kullum a cikin fargana nake da fatan Allah ya sa tana cikin hannu mai aminci".

"In Sha Allah za ta dawo gare mu cikin aminci. Ina ji a jikina Amatullah ba za ta taɓa sauƙa daga kan turban da muka san sa ta ba".

"Allah ya amsa".

"Amin ya Allah yaya Alhassan".

Kashe wutar ɗakin suka yi suka koma nasu ɗakin cikin jimami da tarin damuwar da yake danƙare a cikin zuciyoyinsu.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________________

Page 5️⃣7️⃣
Chapter 24 · 0% Book details