← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 72

Sashe 46

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In sha Allah babu abin da zai faru". Ya jinjina kansa alamar shi ma haka yake fata.
Muka tashi muka shiga wajen rukunin ɗakunan otel ɗin, shuru wajen yake don an sallame mi kowa babu wanda za a ƙara ba wa ɗaki a cikin VIP site ɗin har sai shi da tawagarsa sun tafi. Ya buɗe mini ɗaki yayin da Zinariya ta miƙo mini jakan jakan da yake hannunta wanda har da babban waya a ciki da ta sayo shi sabo dal da ta fita ciro kuɗi. Muka rumgume juna da ita tare da yi mini fatan alkhairi.

Na ƙarewa ɗakin tsallon tsaf tabbas ya tsaru iya tsaruwa, don babu wani abun buƙatan bisa mutum zai nema a cikinsa ya rasa. Na fito da kayan zan sauya daga cikin jakan, na ajiye shi a ƙasan gadon na shiga cikin banɗaki kamar yadda muka tsara.
Wanka na yi ƙirjina ya na buga wa duk kyawu da tsaftan banɗakin amma hakan bai hana ni ƙanƙaninsa ba, haka na yi wankan na gama na saka wani doguwar riga da ya kama jikina tam sai dai ya sauƙa mini har ƙasa na ɗaura ɗan mayafinsa a kaina. A ƙalla na yi mintin talatin a cikin banɗakin kafin na ji alama an buɗe ƙofar ɗakin an shigo, na yi maza na soma aiwatar da shirinmu na jawo towel ɗin da na gani lanƙaye a cikin banɗakin na ɗaura a kaina ina yi kamar ina tsane sumar kaina, na buɗe ƙofar na fito daidai lokacin da ya waigo muka haɗa ido ni da shi.

Tabbas shi ɗin ne tsaye a gaba ba gizo ba kuma ba a cikin mafarki ba, duk da har yanzu zuciyata ta na buga amma na dake na ci gaba takuwa cikin ɗakin yayin da duk ɗaga ƙafar da zan yi na sauƙe sai ya bi ni da kallo.
Gaban madubi na je na zauna ina kallonsa ta cikin madubin da har yake tsaye inda yake bai ko motsa ba, na sakar masa da wani laulausan murmushi mai kashe zuciyata kana na juyo ina yi masa wani shu'umin kallo.
Ya nuna ni da Æ´atsansa zai yi magana na yi caraf na mashe zancen cikin faÉ—in"Amatullah".

"E na gane ki, amma me ye kike yi a nan? Ta ya ya kika shigo cikin É—akin nan? Sannan mafi muhimmanci ma ya ya aka yi kika san da cewa ina cikin otel É—in nan har kika gano É—akin da nake?".

Na ƙara yin wani murmushin a karo na biyu kafin na ce"ban yi zaton waɗannan tambayoyin ne za su fito daga bakinka ba". Ya katse ni"wani tambayoyi ke nan kike so ji?". Ya ɗan ja numfashi sannan na furta"na za ta tambayata za ka yi shin dama har izuwa wannan lokacin ban mance da kai ba".

"Ina cikin da aka ce ki na É—auke da shi?".

Ba tare da tunanin komai ba na ce"na zubar don zai hana ni rawan gaban hatsi ya kuma kawo mini cikas wajen cin duniyata da tsinke". Ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"me yasa kika bar gida? Sannan da kika bar gidan ina kika koma da zama?".
Na kashe masa ido É—aya kafin na ce"bariki na shigo ta yadda zan sama cikakken Æ´ancin kai".
Muryarsa babu alamar wasa ya ce"tashi ki fita daga cikin ɗakin nan". Na tashi daga inda nake zaune na iso gabansa na riƙe ƙugu ina faɗin"ai na ga waje babu inda zan fita". Bai ce da ni komai ya wuce ya shiga banɗaki da alama wanke fuskarsa ya yi ya fito ya ɗan yi turus da ya ganni har yanzu ina cikin ɗakin.

Ya nufi wajen wayar talhon da yake kan teburin ɗakin yana faɗin"bari na ƙira otel ɗin na ji uban waye ya buɗe miki ɗakin nan har kika sama damar shigowa". Na yi hanzarin miƙe na riƙe wayar"kar ka yi hakan don kamar ka ɗauki wuƙa ne ka daɓawa cikinka". Ina rufe bakina aka soma buga ƙofar ɗakin a hankali kuma a nutse, muka haɗa ido da shi"ana buga maka ƙofa ka je ka buɗe ko kuma ni na je na buɗe". Ya yi banza da ni da hakan ya ba ni damar juya wa da nufin zuwa na buɗe ƙofar ya yi hanzarin shan gabana.

"Me ye haka za ki yi?".

"Buɗe ƙofar mana zan yi". Na ba shi amsa cikin halin ko ina kula.
"Koma zan je na buɗe". Ya yi maganar a gajarce yana nufar ƙofar ya buɗe abinci aka kawo ya ƙarba ya shigo da shi ya ajiye akan teburi, muka tsaya mu na kallon kallo ga juna.
Ganin ba shi da niyyar jin komai ya sa ni zaunawa na soma bubbuɗe abincin, ya fi minti goma ya na kallona kafin ya koma cikin banɗakin. Hakan ya ba ni damar tashi na yi wuf na je na ɗauko jakar da na ajiye na ɗauko wannan ƙwayar da wannan wayar na ɓoye ta a jikina, na zo na jefa ƙwayar maganin a cikin ƙaramin flask ɗin ruwan shayin da aka haɗo tare da abinci na jijjiga kana na ajiye, na ja plate ɗaya na ajiye gabana na soma ci, a haka ya fito daga banɗakin ya same wannan karon da alama wanka ya yi don ya fito yana tsane fuskar da wani ƙaramin towel.

Ya zauna a kujerar da take saitina da na É—ago kai muka haÉ—a ido sai na sake masa murmushi na ci gaba da cin abincina.
Sai da ya gaji da kansa ya ce"me ya kawo nan? Me ye kike nema daga gare ni?".
"Ka ci abincin tukunna sai mu yi magana".

"Na fi buƙatar amsar waɗannan tambayoyin fiye da komai a yanzu".

"Ko kaɗan dai ka ci sai mu yi maganar". Ina gama maganar na ɗauki kofi na tsiyaya masa ruwan shayin wanda ina da tabbacin shayi ne na musamman kuma na girma aka yi masa. Na miƙa masa kofi ya ƙi karɓa ban yi ƙasa a gwiwa ba na ajiye masa a gabansa na koma na ci gaba da cin abincina.
A ƙalla ya yi mintuna ashirin kafin ya ɗauki kofin shayin, nan ma sai da ya daɗe da shi riƙe a hannunsa kafin ya kai bakinsa ya kurɓa, na ji wani sanyi a cikin raina tare da wani nutsuwan da ya yi bake-bake a cikin ruhina.
Sai da ya kusa sanye wa kafin ya ajiye kofin ya na kallona ya ce"ke nake sauraro".

Na ajiye cokalin da nake cin abincin da shi na É—auki gorar ruwa na kora na yi hamdala kafin na dawo kan kujerar da yake kusa fuskantar wanda take zaune a kai na zauna.
[12/17, 4:47 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 7️⃣1️⃣

Tagumi na zabga tare da zube idanuna akan sa yayin da shi É—in ma ni yake ta faman kallo, cikinmu babu wanda ya ce uffan illa murmushin da yake ta sakar mini na lura izuwa lokacin maganin da na sanya masa a cikin lemon ya fara aikinsa a cikin jikinsa.
"Ka na ta kallona ba tare da ka ce wani abu ba, ahalin ka san cewa kai nake sauraro". Na yi zancen muryata can ƙasa ina sarrafa harshena cikin salo da hikima. Sai da ya lumshe idanunsa kafin ya cikin wani irin yanayi ya ce"Amatullahhhh".
"Na'am ya Sheikhi". Na yi caraf na amsa ina ka she masa ido guda da hakan ya ba shi damar soma zuba tamkar bakin indararo, hakan ya sa na yi wuf na fito da wayar da take jikina na danna recording na soma naÉ—ar muryarsa.

"Amatullah na neme ki sosai bayan da na sama tabbacin cewar kin ɓace watau kin gudu daga cikin gidanku, kin bar gaban iyayen da danginki kin shiga duniya. Na ba za mutane ta yadda na ba da aikin nemanki a ko'ina sai dai har zuwa wannan lokacin babu wanda ya zo min da wani labari game da ke. Tun ranar da na fara ganinki a ciki wannan tashar ki na tallan kunu na ji cewar kin kwanta min a cikin raina, na ƙudurce cewar komai runtsi komai tsanani sai na cimma buri akan ki sai dai ke ce mace ta farko da kika fara karya alƙadarina da kuma ikirarin da nake yi wa kaina na cewa duk abin da na sa a gaba da niyyar mallakarsa babu makawa sai na same ko da kuwa nisan da yake tsakanina da shi ya kai tafiyar dake tsakanin nan inda muke zuwa cikin birnin sin. Tabbas a zahiri ni malamin addini ne a idanun duniya, ilmina ya jawo min girmamawa da mutuntawa daga wajen mutane da yawa wanda ko da a cikin mafarki ma ban taɓa tunanin zan ina saka kafata a inda suke ba balle har su ba ni wannan girman da mutuntawa, a idanun mutanen ƙasar nan ni mutum ne mai gudun duniya da kuma ruɗin da yake cikinta ni mutum ne kamili da duk wani abun cikin duniya bai dame ni ba balle ya ɗaɗani da ƙasa. Duk da kasancewa ta ba ɗan siyasa ba ne kuma ba ni da haɗi da gwamnatin da ayyukan da take yi amma ganin kimata da darajata da duniya take hakan ya jawo min kusanci da gwamnoni bila adadin ta yadda nake iya ganawa da su a duk sa'ilin da nake so, babu wata buƙatar da zan je da ita gabansu ba tare da sun kawar min da ita ba".
Chapter 46 · 0% Book details