← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 72

Sashe 68

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni dai kam ba zan iya daina yi miki godiya ba, kuma ina so na ƙara tabbatar miki da cewar abokina yana yi miki ingantacciyar soyayya ina ji a jikina shi ne mijin da ya dace da ke, don haka ina fata da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku".
Ban iya amsa wa da baki ba sai a cikin zuciyata na amsa. Har ya tashi ya fita daga cikin falon yana tsokalan Saifullah ban É—ago kaina ba.

"Amatullah". Na tsinkayo muryar Saifullah a kunnuwana, ban amsa ba illa É—aga kai da na yi ina kallon sa ido cikin ido a karon farko a cikin rayuwata. Kamar an buÉ—e fanfo na ji hawaye suna zuba daga idanuna.
Da ƙyar na buɗe bakina na yi magana"ina ta jir ƙiranka shuru idan na ƙira kuma ba ya tafiya, ka san girman tashin hankalin da na shiga kuwa?".

"Ban sani ba sai dai yanzu ki sanar da ni". Babu shiri na watsa masa harara da wutsiyar idona ina goge hawayen idona.
"Afuwan ranki ya daɗe na san na aikata gagarumin laifi. Tashin hankalin ganin Sultan cikin halin da ya shiga shi ya hana ni kunna wayata, Sultan ya shiga tashin hankalin da ko maƙiyinsa ne sai ya tausaya masa har ma ya zubar masa da hawaye, don har kwanciya ya yi a gadon asibiti ya shafe kwanaki uku ba tare da ya san inda kansa yake ba. Wannan tashin hankalin shi ya hana ni samun lokacin wayata balle har na ƙira ki, amma yanzu na kawo kaina a yi min ko wani irin hukuncin da ya dace da ni". Ban iya cewa da shi komai ba illa kukan da na ci gaba da yi, ban yi aune ba na gan shi zaune a gabana dan da ni ina ɗago kai muka haɗa ido da shi.

"Don Allah ki daina wannan kukan idan ba so kike yi ni ma na fara hawayen ba". Yadda ya furta zancen ya sanya jikina gabaɗaya sanyaya tabbas yadda na ga idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ga jijiyoyin kansa sun fito sun yi ɓaro-ɓaro a saman goshinsa hawayen ma idan ya yi ba zan yi mamakina.
Ba don na daina jin zafin da nake ji a cikin ƙirjina ba na kai hannu na goge hawaye fuskana, ya furzo mini iska daga bakinsa a fuskana da har sai da na lumshe idanuna.
"Yauwa ko ke fa, to yanzu an yafe min ne ko kuma?".

"Ai daman babu abin da ka yi".

"Ni dai ki ce kin yafe min sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa".
"To shi kenan na yafe maka, Allah ya yafe mana baki É—aga".

"Amin ya Allah".

Daga haka na yi shuru har sai zuwa lokacin da ya ce"to yanzu kuma me ye ya rage?". Na ɗage masa ido ɗaya alamar rashin fahimta da hakan ya sanya sa faɗin"ko sai na tuna miki alƙawarin da kika yi kafin ku fuskanci idan maganan tawa ta dosa?".
Numfashi mai nauyi na sauƙe kafin na sama zarafin cewa"na ba ka dama Saifullah ka turo iyayenka gidanmu, don su nema maka aurena". A kunyace na ƙare zancen ina rufe fuskana da tafukan hannayena.

"Alhamdulillah".

Ya furta yana yin sujudul shukur ga Ubangiji, ya É—ago ya É—aga hannayensa sama yana addu'a cikin tsananin farin ciki.
"Allah na gode maka bisa wannan damar da ka ba ni. Ina roƙonka ka ba ni ikon killace soyayyarta a cikin zuciyata ba tare da na haɗa ta da wata ɗiya mace ba, Allah ka ba ni ikon riƙe ta bisa amana na kuma inganta rayuwarta ta hanyar da ta dace. Ka hana ni yi mata kishiya har abada". Ganin na yi shuru ban amsa ko ɗaya daga cikin addu'o'insan ba ya sanya faɗin"ba ki amsa ba ke nan?".

"Na amsa a cikin zuciyata".

"To ki amsa da bakinki na ji". Na taɓe fuska ina faɗin"na amsa a cikin zuciyata fa".
"Na amsa a cikin zuciyata fa". Ya yi zancen cikin kwaikwayon muryata da salon yadda na yi zancen, sunkuyar da kaina ƙasa na yi sa boda kunyar da ya lulluɓe ni.
"Wai kunya kike ji? Uhmm! To yanzu idan kin shiga ciki ki sanar da su cewar iyayena za su zo jibi in sha Allah".

Babu shiri na ɗago kaina"da sauri haka?"? Ya ɗage mini giransa ɗaya"to me ye za a jira". Ya ƙare zancen yana sunkuyo da kansa daidai saitin fuskana. Babu shiri na tashi na yi ciki da sauri sa boda kunyan da ya gama ba ni. Ɗakina na nufa na zauna na tsawon awanni ji nake yi saƙayau duk wani damuwana ya hau, zuciyata ta yi fes yayin da raina ya yi tas, haka na wuni cikin karshashi da ƙwarin gwiwan da ya zagaye jikina da yamma muka yi waya da Amira na sanar da ita komai ta taya ni murna matuƙa, ita ta hanyar ni shawaran na ƙira Anty Zulaihatu na sanar da ita zancen zuwan iyayen Saifullah jibi na yi na'am da shawaranta. Mu na gama waya da ita na ƙira Anty Zulaihatu na irge masa komai, Baiwar Allah har da kaddara kafin ta shiga rero mini ruwan addu'a ta kuma shaida mini a ranar za ta ƙira Anty Sawwama da Yaya Alhassan ta shaida musu zancen.

Daren ranar mun fi awannin biyar muna waya da Saifullah yayin da na ji ya ƙara shiga cikin raina sosai, ya ba ni Hajiya Muhibbat muka gaisa a waya har da kukanmu ni da ita. Washe gari tun da asuba Anty Sawwama ta ƙira don ta ji daga gare ni akan abin da Anty Zulaihatu ta ƙira ta sanar mata, na kuwa tabbatar mata da zancen ta yi hamdala tare da yi mana addu'a. Take aka soma shiri da shirye-shiryen tarban iyayen Saifullah gobe ranar Anty Zulaihatu a gidan ta kwana, washe gari da yamma lilis magabatan Saifullah suka zo su gidan Anty Sawwama neman aurena a hannun Yaya Alhassan aka kuma ba su tare da sanya auren nan da sati huɗu masu zuwa. Ranar wuni na yi da zazzaɓi da boda fargaba da zulumi da dare muka sha kukanmu tare da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu sa boda tuno Abba da muka yi da hashashen irin farin cikin da zai yi don ganin wannan ranan in da yana raye.
Bayan kwana biyu Amir ya ɓullo da wani zancen wai na je na yi gwajin genotype, Anty Sawwama ta yi kai da fata ta ce ba zan je ba, har da faka hujja da cewar su a lokacinsu duk ba a yin wannan gwaji ga shi kuma har suka gama haihuwarsu lafiya sumul, daga su har ƴaƴan. Sai da ta ga shi ma kansa Saifullah ɗin ya goya bayan a je a yi gwajin sa boda gujewa afkuwar matsala, sannan ta saduda ta zubar da makaman yaƙinta. Muka cire ranar da za mu je mu yi gwajin lokacin ana sauran sati uku bikin, duk da tun kafin lokacin shi Saifullah ya shaida mini cewar na shi AS ne don ya daɗe da sanin hakan.
Rananr gwajin tare muka je da Anty Zulaihatu da kuma Umar muka je aka yi mana gwaji ni da shi, aka je mu É—an jira kafin sakamakon ya fito haka muka jira aka fito sakamakon Saifullah da Umar suka shiga amsowa.

Babu jima wa suka fito ba su ce da mu komai ba muka shiga mota muka tafi, maimakon mu koma gida sai muka ƙara wuce wa wani asibitin, Anty Zulaihatu ta gaza jurewa har sai da ta tambaya ko lafiya suka ce da ita lafiya kawai su na so tabbatar da wani abu ne.
Wani gwajin aka ƙara yi mana, kamar karon farko Saifullah da Umar ne suka shiga suka also sakamakon. A wannan lokacin yanayin da suka shiga ya yi muni sosai haka muka shiga mota zuwa gida ya faka a ƙofar gidan, ya ce mu shiga ciki ga shi nan shiga wa, haka muka sauƙa ni da Anty Zulaihatu muka shiga cikin gidan, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa.
[12/27, 5:50 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

______________________________________

Page 8️⃣1️⃣

Tun da muka shiga cikin gidan na kasa zaune balle tsaye ɗaki na shiga na yi ta safa da marwa, yayin da tunani kala-kala suke ziyartar ƙaramar curin kwanyata. Cikin wannan halin Anty Zulaihatu ta shigo ta ƙira ni ta ce na zo falo ana nema na, haka na biyo ta a baya har suka iso cikin falon inda muka iske Umar da Anty Sawwama zaune a cikin falo. Muka ƙariso ciki muka zauna.
"Da kuke asibitin ya ya aka yi? Na ga kamar gabaɗayanku hankalinku ba a kwance yake ba. Ko dai wata cutar aka ce ɗaya daga cikinku yana ɗauke da ita?". Anty Sawwama ta yi tambayar tana kafe Saifullah da ido da ya kasa cewa uffan illa sadda kansa ƙasa da ta yi. Anty Zulaihatu ne ta yi magana a madadinsa"wallahi Umma mu ma ba mu san abin da yake faruwa ba, sun dai ce mu shigo ciki ne kawai ba tare da sun sanar da mu komai ba".

Takardan sakamakon gwajin Saifullah ya miƙa wa Anty Zulaihatu ta amsa yayin da yake koro jawabansa.
"Mun je asibitin farko aka yi gwaji inda sakamakon ya nuna cewa ni da ita Amatullah gabaɗayanmu AS ne, daman ni na san nawa na zo ne don a ƙara tabbatar wa, ban yarda da sakamakon don a wasu lokutan ana samun matsala dangane da kayan aikin gwaji ko kuma daga su kansu ma'aikatan hakan ya sa muka ƙara zuwa wani asibitin aka ƙara gudanar da wani binciken, nan ma ba a sama canji daga wancan gwajin na farkon ba. Tabbas ta tabbata ni da Amatullahi dukkan mu AS ne".

"Me ye hakan ke nan ya ke nufi É—an nan? Shi AS É—in mene ne aibunsa? Ni fa shi yasa tun farko ban yarda aje a yi wannan gwajin ba sa boda gudun wanzuwar matsalolin da wannan nan mutanen masu jajayen kunnuwan nan suka kawo".
Chapter 68 · 0% Book details