Sashe 2
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba ta ciki kuma Umma?". Yaya Alhassan ya yi zancen yana faÉ—awa cikin É—akin, shi ma babu inda bai duba ba amma wayam babu ko alama haka ya fito jikinsa a sanyaye aka karaÉ—e ko'ina a cikin gidan. BanÉ—aki, kicin, É—akin ajiya babu inda ba duba ba.
Suka tsaya cirko-cirko kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa.
"To Umma ko ta fita ne ba mu sani ba?".
"Amir ina za taje? Wani gida ta sani a cikin unguwan nan? Wajen waye za ta fita ta je ta?".
Cikin damuwa Yaya Alhassan ya ce"Umma ki kwantar da hankalinki in Sha Allah babu wani abun da zai faru, bari mu fita mu duba. Da yarda Allah Amatullah za ta dawo cikin aminci". Ya juya yana kallon Umar"ka zauna tare da ita bari mu je da Amir".
Yana gama faÉ—in haka suka fita, haka suka karaÉ—e cikin gari duk inda suke tunanin za a dace sai da suka je amma ba yi dace ba. Bayan sallan asr lilis suka dawo gida.
Anty Sawwama tana ganin shigowan su ta miƙe"ya na gan ku haka ina ita Amatullah ɗin?".
Ba su amsa mata ba sai da suka ƙariso suka zauna suna. Duk su biyun suka kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi.
"Alhassan ka buÉ—e baki ka yi min magana mana. Ina Amatullah take?".
"Umma babu inda ba mu duba ba amma ba mu same ta ba. Duk inda muke tunanin da a dace mun je, kaina gabaÉ—aya ya kulle ina Amatullah za ta je wanda ba za ta iya sanar da É—aya daga cikinmu ba?".
Da hanzari Amir ya ce"to ko wajen Ummanta ta je?". Anty Sawwama ta jijjiga kanta alamar a'a"ba ta je wajen mahaifiyarta ba don wannan ƙawar tatan da suke gida ɗaya Amira ta zo nan gidan wajen ta. Wanda hakan yake nuni da cewar ba ta je can ba, kuma na ƙira Zulaihatu ma ta ce ba ta je wajen ta".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! To ina Amatullah ta shiga?".
Haka suka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa, babu abin da Yaya Alhassan yake yi face ƙiran wayan dangi yana tambayar su ko suna tare da Amatullah. Amma duk wanda ya ƙira ba a dacewa. Ya sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya yana zare wayan daga kunnensa tare da faɗin"Umma ba a dace ba, ba ta je wajen su ba".
"Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umar É—auko min hijabina na fita neman yarinyar nan don zama bai kama kama ni ba".
Da sauri Yaya Alhassan ya riƙo hannunta ya zaunar da ita"don Allah Umma ki kwantar da hankalinki kin san fa kina da hawan jini. Bai kamata ki fita ba a wannan halin da kike ciki, ki bari mu mu je mu nemo ta a duk inda ta shiga". Ta kafe shi da ido"Alhassan jiya cikinku akwai wanda ya yi magana da ita ne?". Ya sadda kansa ƙasa"ni ne na yi magana da ita ƙarshe".
"Wani magana suka tattaunawa da ita?".
"Umma maganar da muka yi da ke ne. Kuma ban mata dole ba na ba ta daman ta je ta yi tunani kafin ta yanke ko wani irin hukunci".
Ta É—an jim kafin ta ce"Allah ya sa ba abin da nake tunani ba ne ya faru".
"Umma me ye kike tunani?".
"Wataƙila ta gujewa aurenka ne Alhassan".
Ya waro idanunsa waje"me ye zai sa Amatullah gujewa aurena? Umma shin ina da wani aibun ne?". Ta dafa kansa"ba ta da wani aibu Alhassan amma wannan hashashe ne kawai na zuciyata wanda ba na fatan hakan ya kasance". A sanyaye ya furta"to Umma bari mu je mu ƙara duba. Amma don Allah ki kwantar da hankalinki". Murmushi kawai ta sakar masa suka tashi suka fita ba su dawo ba sai bayan sallan isha'i suka shigo cikin gidan cikin mutuwar jiki.
"Ba a gan ta ba ko?". Anty Sawwama ta furta yayin da suke shigowa cikin gidan. Sai da suka zauna kana Amir ya yi ƙarfin halin faɗin"Umma ba a dace ba". Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin ta ce"Amatullah amana ce a gare ni ba zan so duk abin da zai cutar da ita. Yanzu ban san halin da take ciki ba".
"Umma ni babu abin da nake tunani ma kamar tijarar da mahaifiyarta za ta yi mana idan ta ji wannan maganar". Amir ya yi zancen cikin tashin hankali. Haka suka kwana a zaune yadda suka ga rana haka suka ga dare.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
©ï¸Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 4ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
Washe garin ranar da ƙyar nake iya buɗe idona na jigata na zama majinyaciya tuburan ko yatsan hannuna ba na iya ɗagawa, duk yadda na so na tashi na gabatar da sallan asubahi na kasa tashi haka na ci gaba da zama yashe a wajen numfashina yana fita da wani irin sauti mai ban tsoro da haifar da firgici.
"Ya Subhanallahi! Lafiyarki kuwa?". Na yi an jefa mini tambayar lokaci guda ana É—ago n daga inda nake yashe, dishi-dishi idanuna suke gano mini wacce ta takaima mini daren jiya ta nuna mini banÉ—aki.
"Lafiyar ki kuwa ki na ji na?". Ta ƙara watsa mini tambayar tana riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali. Da ƙyar na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna tamkar wanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu na furta zancen can ƙasan maƙoshina.
"Don Allah ki taimaka mini da ko ruwa ne na sha, kar yunwa da ƙishirwa su yi ajalina".
Ba ta amsa mini ba ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta miƙo mini buredi da shayi. Ban yi wata-wata ba na karɓa kofin na kafa bakina sai da na sha kusan rabi kana na dire kofin, na soma yagan buredin ina ci hannu baka hannu ƙwarya. Take na ji cikina ya murɗa na ji tamkar ana ɗauɗaure mini dukkan kayan cikina, babu shiri na fita waje da sauri na dinga warara amai kamar zan amar da dukkan kayan cikina. Sosai na galabaita jikina ya yi sanyi ƙalau ko tashi daga wajen na kasa yi.
Ta fito daga ɗakin tana ta jeranta mini sannu ta kawo mini ruwa na kurkure bakina na kwance fuskana kana na yi alwala. Ta riƙe ni muka shiga cikin ɗakin ita ta gyara wajen da na yi aman, ta dawo ta zauna a gefe na har sai da na iddar da sallan asubahin da na yi a makare na shafa addu'an da na yi kana na waigo ina kallon ta. Kafin na yi magana ta riga ni.
"Sannu ya ya jikin nakin?".
Na ƙirƙiro murmushin da iya ka cinsa kan leɓena na dasa a fuskata kafin na ce"alhamdulillah da sauƙi na gode sosai da irin kulawarki gare ni, ga shi kuma ko sunanki ban sani ba".
Tun da na soma maganar take ta kallo na har na kai aya, ta gyara zamanta kafin ta ce sunana"La'aniyatu". Na waro idanuna waje cikin da mamaki na maimaita sunan"La'aniyatu kuma?".
Ta gyaɗa mini kanta"sunana kenan, ba ki taɓa cin karo da irin sunan ba ko?".
"Gaskiya tun da nake ban taɓa jin makamamcin irin wannan sunan ba. Amma kuwa kin san ma'anar sunan?".
"Ina kuwa zan san wani ma'anarsa ni dai sunan da mahaifiyata ta sa min kenan. A cewarta sunan ne ya yi mata daɗi kuma da shi kowa yake ƙira tun tasowa ta har yanzu da nake yi miki wannan maganar".
"Tirƙashi! Ita ma mahaifiyarta kin a cikin gidan nan take?".
"Ƙwarai kuwa, Hajiya Babba ita ce mahaifiyata". Muƙut na haɗiye wani miyau mai ɗaci daga maƙoƙarona ina sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ban san lokacin da zuffa ya keto mini ba na fara fiffita da bakin hijabina.
"Ke kuma me ye sunanki?". Kalamanta suka yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"sunana Amatullah".
"Daga wani gari kike don na ga alamar ke ba Æ´ar cikin garin nan ba ne, tun daga yanayin Hausarki na ga ne haka. Sannan me ya rabo ki da gidan iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi jarumtar faÉ—in"sannu a hankali za ki san komai game da ni. Amma kafin zuwan wannan lokacin ina son ki yi mini wani alfarma guda É—aga".
Ta gyara zamanta alamar tana ji da saurarona hakan ya ba ni damar ci gaba da maganan cikin ƙwarin gwiwa.
"Ina son na san wasu abubuwa dangane da tsarin gidan nan, wanda za su taimaka mini wajen gudanar da rayuwata a cikin gidan nan ba tare da wani matsala ta faru ba". Ta É—an jim tana ta kallona kafin can ta furta"da farko dai kowa da kika gani a cikin gidan nan zaman kanta take yi, mafi akasarinsu iyayensu ne suka kore su ko kuma suka aikata wani mummunan abin kunyan da ya hana su zama a gaban iyayen ala dole suka haÉ—o kayansu suka baro iyaye da danginsu. Wasu kuma sun gagari iyayen ne shi ne suka sallama su suka shigo duniya, da yawan matan da za ki gani a cikin gidan akwai bakin uwa akan su wannan dalilin ya sanya ba sa kunya ko shakkan aikata komai. Abu na biyu shi ne komai na gidan nan na sayarwa hatta ruwan da za ki wanke idanunki da shi, in har ki na son zamanki cikin gidan nan ya yi tsawon rai dole sai kin zama fitsararriya ta buga wa a jarida wacce ba ta bari ko ta kwana, sai kin zama wacce ba ta raina ruwan shuka wacce duk wanda ya É—aga mata É—an Æ´atsa sai ta karya shi komai tsufa ko kuma furfuransa".