Sashe 56
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saifullah da Muhammad Taukif idanuna suka sauƙa akan su suna zaune a cikin falon yayin da suma ɗin ni suke kallo.
"Ku ne daman?". Na yi furucin ina nuna su da yatsana. Ban jira amsar kowa ba na ce"Anty me ye waɗannan mutanen suke yi a cikin gidan nan? Wallahi ba na son ganin wannan mutumin balle har mu zauna inuwa ɗaya da shi". Na ƙare zancen ina musu nuni da Saifullahi.
"Daman kin san shi ne?". Amir ya jefa mini tambayar cike da mamaki. Kaina na gyaɗa kafin na ce"shi ne fa wanda na ba ku labarinsa, shi ne wanda na yi aiki a cikin gidan wansa". Daga nan na ƙara kwashe komai da ya taɓa haɗa mu na ƙara sanar da su a karo na biyu. Tun da na fara zancen Anty Sawwama take ta ƙara jinjina kanta.
"Amatullah duk wani abin da ya taɓa faruwa a baya ki manta da shi ya wuce. Yadda ya tako ƙafa da ƙafa ya zo shi har cikin gidan nan don kawai ya yi mana gaisuwa to mu mutunta juna. Su yi abin da ya kawo su mu watse".
Hawaye ne kawai yake ta ambaliya a fuskana ina faɗin"Anty a duniya babu mutumin da ya taɓa gayyaya mini baƙaƙan maganganuna, ya suffanta ni da abin da ko kusa ban aikata shi ba kamar wannan mutumin. Har yanzu idan na rufe idanuna ina tuna munanan kalamansa gare ni". Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe har na tsawon wani lokaci kafin can na tsinkayo muryar Saif ya sauƙa a cikin kunnuwana.
"Tabbas duk abin da kika faɗa haka ne babu kuskure ko ƙage a cikinsa, na aikata miki abubuwa da dama na zarge akan abin da ba ki aikata ba. Sannan akan idona aka wulaƙanta ki na kasa cewa komai. Sai dai duk da hakan ke ce mace ta farko da ta fara kawo mana ɗauki a cikin rayuwarmu ta warware mana wani babban ƙullin da duk ba mu san shi ba. Ranar da kika sanar da mu wannan abun washe gari na tafi garin Abuja na sauƙa a wannan otel ɗin da kika ba mu bayanansa, haƙiƙa na gane wa idanuna abun mamaki don da idona na kama Yaya Saddam da karuwa su na kwance a cikin ɗakin otel ɗin. An yi rikici sosai har sai daga bisani Anty Muhibbat ta ji komai ta bi mu can Abujan sai dai ga mamakina ko kaɗan ba ta ga laifin Yaya Saddam ba sai ma ƙoƙarin ba shi kariya da take yi ta ko wacce fuska. Hakan ya jefa ni cikin tunanin da na baza ma nemon gaskiyar da yake ƙunshe ƙasan kalaman kariyar da take ba wa Yaya Saddam. Nan na gano cewar kafin aurensu ita ɗin budurwan marigayi abokinsa ne watau Yaya Usman da suka yi wa junansu alƙawarin aure tun suna jami'a, wannan dalilin ya sanya suka mayar da kansu tamkar miji da mata ta hanyar biyawa junansu buƙata ba tare da shakkan kowa da komai ba. A lokacin Yaya Saddam ya san komai aka tsaka da wannan lamarin Allah ya karɓi rayuwar Yaya Usman a lokacin Anty Muhibbat tana ɗauke da cikinsa, a sa'ilin da ta sanar da Yaya Saddam da ake ciki ya shiga cikin matuƙar tashin hankali ya nema a zubar da cikin amma ta nuna hakan ba zai taɓa yiyuwa hasalima ko dai ya aure ta ya rufa mata asiri ko kuma ta je ta bayyanawa ita mahaifiyar Yaya Usman ɗin halin da ake ciki".
Ya dakata ta hanyar jan dogon numfashi ya fesar kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya"idan akwai wanda mahaifiyar Yaya Usman ta yarda da shi ta kuma aminta da shi to a bayan Yaya Saddam yake. Wannan matar ta taka rawan gani a cikin rayuwarmu gabaɗaya, a gidanta ya yi karatu ba ta taɓa nuna masa bambamci tsakaninsa da ƴaƴan da ta haifa ba, hatta ni ta nuna min so da ƙauna lokacin da iyayenmu suka rasu ta ja mu a jikinta ta maye mana gurbin duk wani abun da muke jin cewar mun yi rashinsa. Wannan dalilin Yaya Saddam ya dubae har ya abin ce da auren Anty Muhibbat bayan sun yi yarjejeniyar za a zubar da jikin da take ɗauke da shi. Ba na mance kukan farin cikin da mahaifiyar Yaya Usman ta yi lokacin da ta ji cewar Yaya Saddam ne zai auri Matar da Yaya Usman ya so aura Allah bai yi ba. Ta yi hidima sosai a bikin har Allah ya ƙaddara musu kasancewa a matsayin mata da miji har da rabon haihuwar Aryan da Ayan. Sun yi auren ne kawai amma Anty Muhibbat ta san cewa babu ko da ɗigon soyayyarta a cikin zuciyarsa, tun daga wannan lokacin zuciyarta take ayyana mata cewar za ta jure komai daga gare sa don dai kawai wannan sirrin da suke rufe bai fito duniya kowa ya ji ba. Don ya kasa yarda da ita duk da kuwa mutuwar Yaya Usman ya sanya ta sauya". Al'ajabi da mamaki suka taru suka hana mu magana daga ni har ragowar mutanen da suke zaune a cikin falon. Anty Sawwama ta yi ta jinjina lamarin tare da yi mana nasiha mai ratsa jini da jijiya ta ƙarƙare da jan hankulanmu akan mu ji tsoron Allah a cikin dukkan abin da za mu aika. Har aka gama komai ban ɗago kaina ba balle na ce wani abu aka gabatar da addu'ar neman gafara da rahama ga Ummata kana suka fara haramar tafiya. Ko cira kai ban yi na dube su ba sai jin Muhammad Taufik na yi tana magana da Yaya Alhassan cikin girmamawa.
"Yallaɓai idan babu damuwa mu na son magana da Amatullah a waje".
Ba tare da nazari ko dogon tunanina ba Yaya Alhassan ya furta"ba komai ai, mu je daga wajen sai ta fito". Daga haka suka fuce. Anty Sawwama ta dafo kaina da na kwantar jikin ƙafafunta"tashi ki je ki ji abin da za su gaya miki".
"Me ye kuma za su ce mini Anty? Duk abin da za su faɗa ai sun faɗe shi a cikin falon nan. Gaisuwar rasuwa suka zo yi kuma sun yi mene ne kuma ya yi saura?". Cikin lallashi ta ce"ki yi haƙuri ki tashi ki je ki ji abin da za su ce da ke kin ji Uwata?". Ba don raina ya so ba na tashi na nufi wajen ina goge guntun ƙwallan da yake ƙoƙ zubowa daga cikin idanuna. A ƙofan gida na iske su tare da Yaya Alhassan da Amir na iso wajen bakina ɗauke da sallamar da suka haɗe baki wajen amsawa. Yaya Alhassan da Amir suka yi musu sallama ta hanyar yin musabaha kana suka koma cikin gidan suka bar ni tsaye da su.
Kusan mintuna biyu cikinmu babu wanda ya yi magana kafin can Saif ya ce"daman godiya nake so na yi miki sannan kuma na ba ki haƙuri akan duk abubuwan da suka faru, haƙiƙa na aikata miki ba daidai ba". Ban bar shi ya ƙarisa ba na ɗaga masa hannu alamar ya dakata.
"Kamar yadda tun a ciki aka buƙaci na manta da duk abin da ya faru, to ka ƙaddara cewa komai ya wuce". Ya sadda kansa ƙasa yana murza zoben dake saƙala a ƴatsun hannunsa kafin ya ce"na gode".
"Amatullah".
Muhammad Taufik ya furta a karo na farko tun bayan da na fito waje, na É—aga idona ina kallonsa yayin da shi É—in ma ni yake kallo, take na ji wasu hawaye su na bin kuncina ba zan iya juran irin kallon da yake yi mini ba don haka na juya na shige cikin gida da hanzari, kai tsaye É—aki na wuce ina shiga na faÉ—a kan katifa ina kuka marar sauti. Haka na wuni a cikin É—akin in a fito waje to alwala zan yi ina yi nake koma wa cikin É—akin.
Washe da safe bayan mun yi karin kumallo ina zaune a É—aki kawai na ji an yi sallama, idanuna a lumshe na amsa sallamar da hakan ya ke daida da ba ta iznin shigo wa.
"Amatullah".
Take na wartsake na tashi na miƙe tsam sa boda amon muryar ba ta kasance baƙuwa ga kunnuwana ba. Na ware idanuna akan ta kafin na ce"Amira ke ce?".
"Ni ce Amatullah". Ban san lokacin da na ji wani ƙarfi da kuzari ya mamaye jikina ba, taku uku na yi na iso gabanta muka rumgume juna ni da ita, muna kukan da takamanmen ba za mu iya bambamcewa tsakanin kukan farin ciki ne ko na akasin sa ba.
[12/22, 3:46 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
__________________________________
Page 7ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Mun ɗauki tsawon lokaci muna kukan kafin na ja hannunta muka isa bakin katifan muka zauna muna fuskantar juna, yayin da muke ta ƙarewa junanmu kallo. Tabbas wannan Amiran da take zaune a gaba yanzu ta sha bambam da ainihin Amiran da na sani a lokutan baya. Wacce na sa ni ƴar gayu ce na buga wa a jaridar Aminiya, saɓanin wannan da take zaune a gabana cikin suturun ba su rufe mata kattara ba. Wacce da na sani ma'abociyar ta'ammali ce da kayan gyaran jiki da ƙamshi ne saɓanin wannan da babu wannan abubuwan a tattare da ita. Wancan da na sani fatarta kullum cikin gyara da ƙyalle yake yi saɓanin wannan da ta yi duhun gaske.
Na kasa jurewa har sai da na furzar da mamakina na ce da ita"Amira yanzu ke ce haka? Me yake faruwa ne? Don rasuwar Umma ban gan ki ba kuma ban sama nutsuwar da zan tambaya inda kike ba".
Numfashi mai dogon zango ta saka kafin ta furta mini dunƙulalliyan maganan da na kasa fahimtar inda ta dosa.
"Amatullah rayuwar ce ta yi min atishawan tsakin barkono, tabbas na fahimci idan ka san farko to ka kiyayi ƙarshe". Na ɗan waro idanuna waje kafin na ce"me yake faruwa ne Amira? Shin ina Mansur? Ina alƙawarin da kuka yi wa junanku?".
Wani murmushin takaici ta saka kana ta furta"Mansur yana nan mun yi aure da shi, yanzu haka maganar da nake yi miki ni da shi miji da mata ne". Na rarumo hannunta na riƙe gam cikin son gaskata abin da ta faɗa.