← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 72

Sashe 8

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gyara zamanta kafin ta ce"ina nufin akwai maza masu kumbon susa masu hannu da maiƙo da suke neman mata ire-irenku ruwa a jallo. Ba don komai ba sai don biyan buƙatar kansu kuma ba sa ƙyashin kashewa mace ko nawa ne matuƙar za su sama abin da suke so a wajen ta, idan ma tsoronk ɗaukar ciki ne yanzu zamani ya zo da abubuwa da yawa, ana amfani da comdon domin hana ɗaukar ciki. Idan kin yi dace ma wasu mazan ba sai kun kwanta da su ba kawai da zaran sun sama nutsuwa da ke shikenan buƙatarsu ta biya. Sannan idan duk hakan bai yi miki ba kawai wata hanya mai sauƙin gaske, akwai matan manyan mutane a cikin ƙasar nan da kewaye da mazajen suka tara musu dukiyar da ko za su yi shekaru ɗari a duniya ba za su iya cinye shi ba, duk wani nau'in jin daɗi na duniya suna samunsa su ci abin da suke so su sha abin da ransu yake so, su sa suturar da duk suka ga dama sannan su hau duk kalar motar da suka yi ra'ayi, su je duk ƙasar da suka zaɓa, su kashe duk adadin kuɗin da suke so. Sai dai matsalarsu guda ɗaya ce jal ita ce ba sa samun lokaci da kulawa mazajen su. Wannan dalilin ya san da yawa da cikinsu suka soma neman maza a waje sai dai masu wayo a cikinsu ba maza suke bi ba, mata ƴan uwansu suke sawa a nemo musu su yi duk abin da za su yi da mijinsu na aure da ita. Su kan ɗauki dukkan nauyinta su yi mata komai da komai, su jiyar da ita daɗin da ba ta taɓa jin makamancin sa".

Tun da ta soma zancen nake bin ta da ido har ta kai aya. Na numfasa kafin na ce"shin Hajiya aikata hakan yana daga cikin sharaɗin zama a cikin gidanki ne?". Ta watsa mini wani wulaƙantaccen kallo kafin ta amsa mini a taƙaice
"A'a".

"To in dai har hakan ba shi ne sharaɗin zama a cikin gidanki ba. Ina so ki ba ni dama na je na nema aikin da zan riƙe kaina da shi ba sai na bi wannan hanyar da duk kika zayyana ba". Ta yi banza da ni ba tare da ta ce da ni uffan ba haka na ci gaba da zama ba ta ce da ni ci kanki ba. Har sai da na gaji don kaina na ce"Hajiya zan iya tafiya?". Ta yi mini wani kallo ta wutsiyar idonta kafin ta ce"wai dama ba ki tafi ba? Za ki iya tafiya".

"Na gode mu kwana lafiya".

Na furta yayin da nake tashi na fice daga ɗakin, tun kafin na isa cikin ɗakina hawaye suke zuba daga idanuna har na isa, na rufa ƙofar na rufe tare da jingina a jikin ƙofar ina sulalewa a hankali har zuwa ƙasa. Na kifa kai da gwiwana ina saki wani irin gigitaccen kuka mai ratsa zuciya. Na raba dare ina kuka kamar raina zai fita kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ni ban tashi sai da gari ya fara yin gaske, na tashi a firgice saboda mafarkin da na yi da Abba.
Wai ya zo cikin ɗakin sanye da fararen kaya ya taɓo kafaɗana na ɗago kaina ina kallonsa yayin da hawaye yake zuba daga idanuna. Fuskarsa ɗauke da yalwataccen annurin yake share mini hawayen da ya ɓata mini fuska. Bai ce da ni komai ba haka ni ma Allah bai ba ni ikon yi masa magana a cikin mafarkin ba har na farka.

Sai da na sauƙe dogon numfashi kafin na tashi na fito sai a lokaci na tuna ko ruwan alwala ba ni da da shi balle wanda zan wanke fuskana da shi. Duk abin duniya ya taru ya yi mini yawa, na tsaya a ƙofar ɗakin ina tunanin mafita. Ina tsaye La'aniyatu ta fito muka sakarwa juna murmushi ni da ita kafin ta ce"ɗazu na zo ai na ga ba ki buɗe ƙofar ba ya ya jikin nakin?".

"Da sauƙi".

"Kamar wani abun kike buƙata ko?". Na sauƙe numfashi kafin na ce"wallahi kin ga na tashi ne ba ni da ko ruwan da zan yi alwala da shi".

"To bari na kawo miki mana". Har za ta juya na dakatar da ita"a'a indai akwai inda ake É—ebowa ki kwantata mini kawai. Ai ba zan dawwama kullum sai an É—auka an ba ni ba, gwara tun yanzu na fara taimakawa kaina".

"Da nisa fa kuma kin ga har yanzu gari bai gama yin haske ba. Ƙarfe biyar ne da wasu ƴan mintuna". Cikin ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ni dai don Allah ki taimaka mini ki kwantata mini wajen sai kuma ki ba ni bokitin da zan ɗebo a ciki". Ba ta yi musu ba ta koma ciki ta ɗauko mini bokitin ta ba ni ta yi mini kwantancen wajen na yi mata godiya, duk yadda ta so ta raka ni ƙin yarda na yi duk da ba wani gane kwantancen natan na yi sosai, amma na gwammace na fita na nema da kaina.

Sharau kan layin babu kowa sai kukan karnuka da ƙwaɗuna, haka na dinga tafiya har sai da na fice daga layin na shiga wani na yi ɗan tafiya kaɗan. Na tsaya ina ta rarraba idanu don ta ce da ni a farkon layin zan hangin fanfon jikin wani masallaci.
Hamdala na yi yayin da na hango fanfon na ƙara sauri na isa wajen na buɗe na wanke fuskana, na kurkure bakina kana na yi alwala.
Na cire ɗan kwalin kaina na shimfiɗa da niyyan yin sallan a kai, na ga an miƙo mini sallaya. Na tsorita sosai don ban ga mutum ba sai kawai gani na yi an miƙo mini abu.

"Karɓi ki yi sallan a kai".

Na ji an furta tare da ajiye mini sallayan a kan É—an kwalin da na shimfiÉ—a, bai jira abin da zan ce ba ya nufi masallacin da saurin don lokacin har an shiga sallan.
Na shimfiɗa sallayan na tada kabbara, a nutsu na gabatar da sallan har na iddar don jam'i na b masalallacin. Ban yi wani dogon addu'a ba na tashi don sa'ilin har an fara fitowa daga cikin masallacin. Na ɗeba ruwa a bokitin na ninke sallayar na riƙe a hannuna. Ina ta rarraba ido ganin ta inda mutumin zai fito amma shuru har aka gama fitowa sannan na ga ya fito. Ya na sanye ne da jallabiya doguwa kalan ruwan ƙasa sai wani ƙaramin hula a kansa fara sol ban ga fuskarsa da kyau ba abu ɗaya zan iya cewa na gani a fuskar sa shi ne sajen da ya kewaye fuskar.

Yana isowa na miƙa masa sallayar bai karɓa ba ya tsaya kallona har sai da na zargu da kaina na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa.
Sai da ya gama yin sa ya sa hannu ya karɓa sallayan bai ce da ni komai ba ya juya ya tafi. Na daɗa gammo da ɗan kwalina na ɗaura bokitin a kaina na bar wajen.
Ina isa gida na zuba ruwa a butan da Aminu ya kawo mini na ajiye shi domin yin alwala. Ragowar na shiga banÉ—aki na watsa a jikina saboda tun da na zo ban ga ruwa ba. Kayan jikina na mayar na fito.

Ina zaune ina tunanin ta inda zan fara La'aniyatu ta shigo ta ajiye mini biredi a gabana na cira kai ina kallon ta"wannan fa?".
"Na ki ne mana".

"Wai ke Ummanki ba ta yi miki faɗa ne na yadda kike ɗauko abubuwa ki na ba ni. Bayan na san cewa kowa shi yake ci da kansa a cikin gidan da samar wa kansu dukkan wasu ababen buƙata".

"Ai ba ta sani zan da nake ɗauko miki". Na waro idanuna waje"to ai kuwa ba zan ƙara amsa ba, don haka wannan ma ki ɗauka ki mayar da shi inda kika ɗauko. Daman ba yunwa nake ji ba kuma fita ma zan yi". Ina dire zancen ma tashi na ɗauko mata bokatin da ta ba ni na bata tare da godiya. Duk yadda ta so na karɓa biredin na tubure akan cewa ba na ji yunwa dole ta haƙura ta bar ni, muka fito tare da ita daga ɗakin na kulle ƙofar na ba ta ajiyar makullin.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_____________________________________

Page 4️⃣6️⃣

Na daɗe tsaye a ƙofar gidan ina ta tunani da nazarin inda zan nufa, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranya daga koramar idanuna ba. Tunawa da na yi irin rayuwar da na yi a baya da kuma Abba sai dai har yanzu ba na dana-sani balle nadamar barin gida da na yi. Na yi imanin tun da uwar da ta ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da wasu kwanaki a jikinta, ta yi wahalar nishin naƙudana, ta shayar da ni daga jikinta na tsawon shekaru biyu, ta raine ni har na girma na yi wayo na zama mutum. Ta iya fito ɓaro-ɓaro ta bayyanawa duniya ba ta buƙatata ba ta ƙaunar ganina ta sallama ni a duniya to babu wanda zai iya jure zama da ni. Komai alaƙa, dangantaka da kuma ƙarfin igiyoyin zumucnin da suke tsakani.
Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kawar da hawayen da suke gudu a bisa dandamalin fuskana, tafiya na soma yi har sai da na bar cikin layin ban yi gigin komawa layin gidajen da na je jiya ba. Sai da na kusa barin cikin unguwan, ƙafafuna sun yi futu-futu da ƙura na gama gajiya tilis sai da na nema waje na zauna na huta kafin na tashi na ci gaba da tafiyan na iso baki gate ɗin wani gida na ƙwanƙwasa ƙirjina yana tsananta bugu.

Mai gadi ya buɗe ƙaramin ƙofan jikin gate ɗin bai ce da ni komai ba ya tsaya tsawon mintuna yana ƙare mini kallo. Na durƙusa har ƙasa na gaishe shi bai amsa ba ya soma zazzage mini buhun bala'i mini kamar zai cinye ni ɗanya.

"Baiwar Allah lafiya za ki zo gidan mutane ki na yi musu irin wannan bugun kamar wanda kike bi fashi ko tara. Wace ce ke kuma daga ina kike?".

"Baba aiki nake nema ko na wankau ko raino".
Chapter 8 · 0% Book details