Sashe 26
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yi caraf na amshe zancen kamar ji nake yi ta ce kule na ce cas.
"Hajiya wainar fulawa ne zan soya wa baƙo?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"watau a baƙo kawai ban da mu ƴan gidan ko Amatu?". Na murmusa kafin na ce" har da kowa da kowa ma ranki ya daɗe. Amma Anty Altine ta riƙa da ta shirya abin karin kumallo shi yasa na taƙaita wainar fulawan ga baƙon kawai".
"Ai kuwa ni ma dai ina ga wainar fulawan nan zan ci, don dankalin nan gabaÉ—aya ya gama fita daga kaina zan dai sha shayin. Amma fa sai ki hanzarta don sun kusa fitowa kuma fita za su yi".
Cike da jin daɗin kalamanta na ce"in sha Allah Hajiya ba zan ɓa ta lokaci ba". Murmushi kawai ta sakar mini ta juya ta bar cikin kicin ɗin, ko ido ban ɗaga na ga Altine ba balle na tanka mata sai dai ina jiyo sautin ƙwafan da ta dunga sake wa wani na bin bayan wani na tsawon mintuna.
Har na yi ƙare suyar wainar fulawan ba ta ce da ni da komai ba. Na ɗauko hula na zuba a ciki, can na hango cabbage na ɗauko na yanka na wanke na zuba a gefen a wani plate na rufe shi. Na waiga na kalle ta.
"Ranki ya daÉ—e na gama sai kuma me ye ya rage?".
Ban yi mamaki ko na haÉ—u ba da na ga ta gallo mini wata uwar harara kafin ta ce"a tambayi kaza hanyar zuwa tafi?".
"Tabbas kam ba za a tambaye ta tun da ba zuwa take yi ba"
Daga haka ban ƙara ce mata komai na ɗauko tray na jere su a kai na fita ina jin tsakin da take dokawa yayin da nake ƙoƙarin ficewa daga cikin kicin ɗin.
Ban iske kowa a falon ba sai ƙarar iskan AC da yake aiki a cikin falon na jere su akan dinning table, Ina tsaye a wajen Aryan da Ayan sun rugo a guje suka shigo cikin falon suka nufo inda nake tsaye.
"Wai in ji Uncle Saif an gama abinci? Za su fita da abokinsa".
Kafin na yi magana Hajiya ta sauƙo ta karɓe zancen"babu inda za a kai musu abinci idan ba za su zo nan su ci ba, sai dai su haƙura". Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta ƙira shi ina jin ta abin da take faɗi cikin tsare gida babu alamar wasa a tattare da ita.
"Ku shigo an kammala abincin". Tana gama faɗin haka ta katse wayar ta ƙariso ta zauna, ban bar cikin falon ba ya shigo take na ji ƙirjina ya buga da ƙarfi ta gabana ya zo ya wuce na gaishe shi ya yi banza da ni wanda kuma ina da tabbacin ya ji gaisuwar da na yi masa sarai.
"Hajiya Antynmu tun ɗazu fa abincin nan muke jira, idan ba za a ba mu ba ne sai a gaya mana mu san inda dare ya yi mana". Ya ƙare zancen cikin sigar zolaya yana ɗan sosa ƙeyarsa.
"Ina shi baƙon nakan?"
"Yana can sashina".
"To sai ku fito ku zo mu ci abincin".
"Hajiya Anty kin san Taufik fa da kunya ba zai taɓa iya nan gabanki ya sha ko da ruwa ne ba balle har ya saki jiki ya ci abinci".
Ta harare shi"mace ne ƙarshen kunya kenan ai ko?". Ya marairaice murya"mu dai yanzu Anty ki yi haƙuri a ba mu abincin. Kin san fa an ce koro da yunwa ba shi da kyau kuma ba shi da daɗi". Dariya ta tuntsire da shi kafin ta waigo tana kallona da har yanzu ina tsaya a inda nake ban motsa ba.
"Amatullahi É—auki girkin kika jera ki kai musu. Ayan zai biyo ki da flask din tea É—in".
"To ranki ya daÉ—e".
Na amsa da shi a taƙaice na ƙara jere su akan tray ɗin na fita na nufi sashinsa, ina jin ƙirjina yana tsananta bugu da ƙarfi da ƙarfi. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sanya ƙafata a cikin falon na yi hamdala sa boda iske falon da na yi
babu kowa a cikinsa sai sautin karatun Alqur'anin da aka kunna yana tashi.
Na ajiye tray ɗin akan table na juya da sauri xan fita na ji an tsayar da ni ta hanyar faɗin"baiwar Allah tsaya mana". Take jikina ya soma rawa mussamman da na ji sautin takunsa yana ƙara nufo inda nake tsaye, ban yi ƙasa a gwiwa ba na yi saurin ci gaba da tafiya sai dai ban yi taku huɗu masu kyau ba.
Aka buɗo ƙofar falon Saif da su Ayan suka shigo yana riƙe da flask ɗin tea, Ayan yana riƙe da sacet ɗin madara da milo yayin da Aryan ya riƙo kofuna. Sanƙarewa na yi a inda nake tsaye, tabbas wannan shi ne gaba kura baya ƙura, na rasa inda zan yi gaba ko gaba.
[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 5ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
Ina ɗago kai idanuna suka sauƙa a cikin na Saif kallon da ya watsa mini ya sanya jikina yin la'asar tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi na rusunar da idanuna ƙasa yayin da Aryan da Ayan suka ƙarisa shigowa cikin falon suka je suka ajiye abin da yake hannunsa akan teburin.
"Za ki iya tafiya tun da kin gama abin da ya kawo ki ko". Ya yi zancen cikin tsare gida fuskarsa babu alamar wasa balle ya É—auki wargi.
"To ranka ya daɗe". Na yi zancen ina ɗaukar hanyar fita daga cikin falon cikin matuƙar sauti tamkar zan tashi sama, har na kai ƙofar fita na ji an dakatar da ni.
"Wace ce wannan É—in Saif? Ban san ta ba tun da nake zuwa cikin gidan nan".
"Baƙuwa ce".
Ya ba shi amsa a taƙaice da hakan ya ba n damar ficewa da sauri ban sarara ba har sai da na zo ƙofan falon sashin Hajiya Muhibbat na tsaya ina mayar da numfashi tare da daidaita nutsuwata kana na shiga ciki, tana zaune tana shan shayi na iske ta jifa-jifa tana latsa wayarta, na yi mata sannu kana na wuce ɗakin Altine bakina ɗauke da sallamar da ban sama amsa daga gare ta ba illa kallon banzan da ta bi ni da shi har na isa na zauna a bakin katifar.
"Ga can abinci a kula ki ɗauka". Kaina kawai na gyaɗa mata na jawo hular da ta yi mini nuni da shi. Ina buɗe wa na ci karo da farar shinkafa da ta gama shan iska ta bushe ƙararau ga wani ɗan yajin da aka yafa a gefen tamkar wanda aka roƙo daga maƙota.
"Abincin waye wannan É—in? Ko a karnuka za a ba wa?".
"Tun da kike zuwa gidan nan kin taɓa ganin kare ne?".
"To na sani abu a duhu. Don wannan abincin kam ai É—an Adam dai mai rai da numfashi ba zai iya cin sa ya kwana lafiya ba sai dai dabbobin. Hasalima ai na ga ba wannan nau'in abincin aka girka ba". Tun kafin na rufe bakina take bi na da wani irin kallo tamkar za ta rufe ni da duka. Sai da ta tashi ta zauna daga kishingiÉ—ewar da ta yi kafin ta soma amayar da balbalin wutar zancen da yake cikinta.
"Ke har kin isa ki tisa ni a gaba ki na tuhumata akan abin da kika gani a cikin ƙwaryan tuwonki?. Ina da karfin iko a cikin gidan nan fiye da duk yadda kike tunani da hashashe, idan har kika bari na juyo kanki na saka miki ƙahon zuƙa billahillazi hatta numfashi mai kyau ma sai a gagare yi a cikin gidan balle kuma wasu abubuwan".
Na lanƙwasar da murya kafin na furta"tuba nake yi ranki ya daɗe. Ai ni ban isa na sa kafar wando ɗaya dake ba wane ni ubana dillalin Kashi. A yi mini aikin gafara". Wani tsaki mai dogon zango ta saka tana jifa na wani irin mungun kallo kwatankwacin irin kallon da mai dukiya yake yi wa ƙasƙantacce. Na sakar mata da wani lausassan murmushin da har sai da haƙwarana suka bayyana na jawo kulan abincin gabana na sa hannu na soma ci. Duk da yanda shinkafan yake sukan wuyana ina jin suna tsayiwa a maƙoƙarona hakan bai hana ci ci gaba da tura abincin ba. Na fahimci matuƙar ina son na cimma buri da muradina akan ta sai na kwantar da kai na yi mata biyyaya domin sunkuyawa gwada bai taɓa zama gajiya wa ba. Sai da na cinye abincin tas na ɗauki kular na fito waje na kai ta kicin inda a nan na sama ruwa na kwankwaɗa na sama sauƙin tsayuwar ƙayan kifin da shinkafar ta yi mini a hanyar wuya.
Na ji wani abu ya taso mini cikina ya murɗa tae na ji amai ya taso mini da hanzari na fita ta ƙofar baya na dinga kwarara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina. Sai da na gama na tashi na je na kwance baki da fuskana na zo na gyara wajen da na yi amai ɗin, gabaɗaya jikina babu ƙwari haka na baro cikin kicin ɗin na dawo ɗakin Altine ban iske ta a cikin ɗakin ba hakan ya ba ni daman kwanciya akan katifar ina mayar da numfashi jin jikina nake yi gabaɗaya ya mutu tamkar wacce aka yi wa ɗan banzan duka.
Muryar Taufik da na ji É—azu a sashin Saif ya soma dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan na lumshe idanuna da hakan ya ba wa hawaye da suka ciko mini koramar idanuna damar kwaranya a bisa fuskana.
Wata zuciyar tana raya mini ina ma da na tsaya na laɓe na ga ko da fuskarsa ce, duk da muryarsa ma kaɗai ta tabbatar mini da cewa shi ɗin ne dai, na ja dogon numfashi na fesar kafin na gyara kwanciyata na kwanta akan gadon bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama mini shamaki tsakanina da sararin samaniya. Na yi nisa a cikin tunanin nake yi da har ban san lokacin da Altine ta shigo cikin ɗakin ba balle tsayiwar da ta yi a kaina kamar wacce ta haɗiye taɓarya babu alamar ranƙwafawa a tattare da ita.