Sashe 44
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da mamakin da ya bayyana har a cikin furucina na ce"sanar da ni abin da yake faru wa cikin gaggawa kar ki bari zuciyata ta buga. Don fargaba". Ta ja dogon numfashi kana ta soma zayyano mini zancen daki-daki wani yana bin bayan wani.
"Na isa masauƙina a cikin babban otel kuma mafi tsada da tsaruwa a cikin garin Abuja, na ci mai kyau na sha mai kyau sannan na kwanta na yi baccin huce gajiya. Washe gari na shiga hidimar tarban Ogana da zai biyo jirgin yamma daga ingila zuwa ƙasa Najeriya. Ƙarfe shidan yamma ya ƙira ni ya shaida min ya iso har ma ya ɗauki hanyar zuwa otel ɗin da nake. Tabbas na cika da murna da har sai da ya sa ni na tashi na taka rawar daɗin jin kalamansa a gare ni. Ya Kawo min tsarabobi masu yawan gaske mun faranta ran junanmu a wannan ranar, sa boda mun yi marmarin juna sosai muna kwance da rana kwatsam na ji ana mana buga mana ƙofa. Lokacin bai tashi daga bacci ma don haka na tashi na je na buɗe ƙofar ina buɗe wa na ga wani Saurayi tsaye. Muka yi kallon-kallo da shi kafin na ce da shi Bawan Allah lafiya za ka zo ka na buga mana ƙofa? Waye kake nema?. Bai amsa min ba sai da na ga yana ƙoƙarin shiga cikin ɗakin na ƙi ba shi dama muka soma hayaniya da shi, da hakan ya sanya Ogana tashi daga baccin da yake yi ya zo shi wajen a nan na fahimci sun san juna ƙarshen sanayyana ma saurayin ƙaninsa ne na jini da suka fito daga ciki ɗaya. An yi rigima sosai sun yi musayar yawu da shi ainun na fusata na ɗauki kwalbar giyan da ya sha a daren jiya na je da nufi rotsawa saurayin a kansa ya zame na sama Saddam a goshinsa, take kwalbar ta tarwatse jini ya soma malala daga goshinsa take a wajen ya yanke jiki ya faɗi ba ya ko motsawa. Na gigice na rasa abin da zan yi kawai na ɗaura hannu a ka ina rusa kuka, ma'aikatan otel ɗin suka shigo su suka ƙira ƴan sanda suka zo suka tafi da ni aka rufe ni ban ƙara sanin halin da Saddam yake ciki ba sai da na yi kwanaki biyar cur a ofishin ƴan sandan kafin Saurayin ya zo shi a bakinsa nake jin mummunan halin da matar shi Saddam ɗin take ciki. Kuma ita ta buƙaci a yi min afuwa ta ƙara cewa idan halina ne wataran zan kai kaina inda ba zan iya fita ba, haƙiƙa na ji tausayinta ainun kuma na jinjina halin girma da dattakunta, ba ni da wani wajen da zan je haka nan ba ni da kuɗin da zan dawo gida sa boda ATM ɗina yan can ɗakin otel ɗin. Haka nan ma wayata ban san duniyar da take ciki ba".
Ta tsagaita kafin ta ci gaba da cewa"da ƙafata na yi dogon tafiya har na isa gidan wata ƙawata da na muka haɗu da ita sanadiyyar bariki. Sai dai ita ta tuba har Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta. A gidanta na zauna ta ba ni mafaka sa boda lokacin mijinta bayan cikin garin, a cikin gidanta na yi waɗannan tsawon kwanakin ina ta fafutukar yadda zan yi welcome back ɗin layina ko don kuɗaɗena da suke kwance a cikin akawuna. Da ƙyar hakan ya yiyu a cikin azurkinta ta taimaka ta ba ni ƙaramar wayar da na saka layin, ana cikin hakan mijinta ya ƙira ta a waya yake sanar da ita cewar yana hanyar dawowa lamarin da ya fara haifar da matsala a tsakaninmu ke nan, ta dade akan sai dai na bar cikin gidan don mijinta ba zai dawo ya iske ni a gidan ba a cewarta ba ta yarda da ni ba ta san zan iya zagayawa na ci amanarta ta hanyar keɓewa da mijinta. Duk kwantar da kai da rantsuwar da na yi mata bai ɗaɗata da ƙasa ba haka ta koro ni ta ba ni wasu kuɗaɗe wanda da su na yi kuɗin mota na dawo garin nan".
Sosai na jinjina girman iftila'i da masifar da ta faÉ—a, na cira kai ina kallon ta sai dai kafin na yi magana ta ri ga ni.
"Har yanzu ina mamakin yadda aka yi ƴan uwan Saddam suka san mu na tare da shi a cikin otel ɗin nan, har suka zo suka yi mana tijara. Bayan kuma shii da kansa ya ba ni tabbacin bai sanar da kowa cewar ya shigo ƙasar ba ciki kuwa har da matarsa uwar ƴaƴansa". Na ja dogon numfashi na fesar ina jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri.
Lokacin sallan magrib da ya kawo kai shi ya tursasa mini tashi na fita na je na yi alwala na dawo na gabatar da sallan, ban tashi daga wajen ba sai da na yi sallan isha'i. A lokacin Zinariya ta jawo ledar da ta dawo da shi ta ɗauko wayar ta kunna ta, kamar jira ake yi ta kunna sai kuwa ga ƙira ya shigo ta. Ta ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa ta kwanta akan bayanta ta ɗaura wayar akan ruwan cikinta yayin da ta lumshe idanunta.
"Yau ina kika shiga ne kwana da kwanaki? Ina ta ƙiran layinki ba ya tafiya. Ko dai wani harkar kika saita ne kika juya mana baya? Don na san halinki kamar yadda na san yunwar cikina".
A taƙaice ta ce"wannan wani dogon labari ne mai zaman kansa. Amma dai yanzu fara sanar da ni dalilin neman da kake yi min".
"Malamin da kuke son ganin yanzu haka maganar da nake yi miki yana cikin otel É—in mu. Ya zo shi bikin Æ´ar gidan mataimakin gwamna da za a yi don na ji a wata majiya mai tushe cewar shi zai ba ta auren yarinya, ma'ana shi ne waliyinta. Ku na da damar da za ku iya ganinsa daga nan har zuwa ranar da za a É—aura auren".
Babu shiri ta tashi ta zauna tare da buɗe idanunta"Oga Deeno mu bar wasa shin da gaske kake wannan maganar?". Ta ja wata doguwar tsakin haushi da takaicin ta da ɗura masa kafin ya ce"ta yaya zan yi miki wasa da irin wannan zancen? Na yi miki abin da kike so yanzu ni ma lokaci ya yi da za a rama wa kura aniyarta". Dariya ta fashe da shi"kar ka damu Oga zan zo takanas na same ka". Da hakan suka yi sallama ta katse ƙiran ta zo ta ƙanƙame ni.
"Burinki ya kusa cika Amatullah. Sheikh ya zo cikin garin nan kuma ina da tabbacin Oga Deeno zai share mana duk wani hanyar da zai sada mu da ganinsa". Wani sanyi na ji a cikin zuciyata na ji tamkar an warware mini ƙullin da ya tokare mini ƙirjina ban san lokacin da na ɓanɓare ta daga jikina, na kai goshina ƙasa na yi sujudul shukur ga Ubangijina ba ina hawayen farin ciki.
[12/15, 5:32 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
Â©ï¸ Maimuna Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 7ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
Duk yadda na so tsayar da hawayen da suke sarrafa kansu wajen zuba daga cikin koramar idanuna, na kasa samun wannan damar. Sosai nake kukan irin kukan da na daɗe ban yi makamancinsa ba, sai dai na yarda hakan yana da nasaba da abubuwan da suka taru suka yi wa zuciyata ƙawanya. Ban san sama zarafin zubar da ƙwallar ba sai yanzu ta dalili ya yi dalili. Zinariya ta tsaya ta yi sakeke tana kallona. Ta kai hannunta tana share mini hawayen da suka ɓata mini fuska.
"Ke kuwa mene ne abin kuka? Wannan ai abin farin ciki ne da ya kamata ki tashi ki yi tsalle har ma ki tada rawa tun da daman buƙatar maji hajji ai salla ne".
Ban iya tanka mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa murmushin da na yi ƙoƙarin sakar mata ita ma ta mayar mini. Na rungume ta tsam a jikin ina ta faman jeranta mata godiya wani na bin wani kai ka ce kyautar kujerar hajjin bana ta ba ni a lokacin nake tsanani da buƙatar hakan.
"Ba kuka ya kamata ki yi ba Amatullah murna da murmushi ne ya dace da fuskarki a irin wannan lokacin na tsananin farin ciki da taka tsanin cikar buri da muradin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjinki. Ki goge idanunki ki nutsu mu tsara yadda abubuwa za su kasance har su tafi daidai da tsarinmu. Ba tare da an sama wani matsala ba".
Numfashi mai nauyi na furzar daga bakina tare da gyara zamana ina fuskantarta kafin na yi magana ta tari numfashina ta hanyar faÉ—in"to yanzu me ne tsarinmu na gaba?".
Na ɗan yi jim tamkar mai nazarin kafin na ce"idan na gan sama ganinsa to dukkanin burina ya cika sannan haƙata ta cimma ruwa". Ta yi mini wani kallon da na kasa fahimtar inda ta dosa.
"Me ye hakan yake nufi ke nan? In kika gan shi kawai shi kenan komai ya zo ƙarshe? Babu wani abun da za ki yi? Kin san ba shi ma ba zai zauna haka nan dole ne ya kasance da shirinsa na ko ta kwana".
"Ba a suffar Amatullah ɗin da kika sani zan je masa, zan je masa ne a suffar irin matan da yake harka da su duk da cewar kuwa duniya ba ta san wannan ɓoyayyan halin nasan ba". Ta yi caraf ta amshe zancen"ta ya ya za ki yi hakan?".
Ta murmusa kana na ce"Allah ya kai mu gobe idan muka je cikin otel ɗin za ki ga ne wa idanunki. Bayan mun haɗu da shi mun zanta zan naɗi sautin muryarsa sannan ban shayar da shi abin maye ta yarda zai fita daga cikin hayyacinsa. Hakan ne zai ba ni damar yin abin da na yi niyya zan ɗauki hotona da shi, wanda su zan riƙe a matsayin makaman da zan yaƙe sa da su. Har na kawo ƙarshen baƙi hali da mungun nufin da yake yaɗawa a tsakanin al'umma a ɓoye".
"Kuma ki na ganin bayan faruwar hakan ba zai sa a bazama nemanki ba ruwa a jallo?".