Sashe 69
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma hakan ya nufin aure a tsakaninsu ba zai taɓa yiyuwa ba, sa boda ko da an yi auren matsaloli da tashin hankalin da za su biyo bayan auren sai ya tushe duk ginin soyayyar da aka yi ta wargaza komai". Anty Zulaihatu ta yi zancen tana juya farar takardar sakamakon gwajin da yake riƙe a hannunta.
"To sai me ye don dukkan su AS ne? Mu da can a lokacin mu ana wannan gwajin ne amma ba ga shi mun yi auren mun haihu lafiya sumul ba. In sha Allah babu abin da zai hana auren Saifullah da Amatullah". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta yi shigewarta cikin É—akinta, da kallo dukkaninmu muka bi ta kafin Anty Zulaihatu ta saka salati cikin tsananin damuwa da rashin mafita da kuma madafa.
"Anty yanzu ya ya za a yi a fahimtar da ita illan da yake tattare da hakan?". Saifullah ya yi zancen muryarsa har rawa take yi yayin da yake tsayar da idanunsa akan Anty Zulaihatu.
"Wallahi ban san yadda zan yi wa Umma bayani ta fahimta illan wannan abun ba. Amma bari na ƙira Yaya Alhassan na sanar da shi halin da ake ciki".
"A'a kar ki ƙira shi alhalin yana can wajen aikinsa, idan ya dawo kawai ki yi masa bayani ni ma in sha Allah zan ƙira shi mu yi magana a waya".
"To shi kenan duk yadda ka ce haka za a yi".
Sai a lokacin Umar ya buɗe baki ya yi magana damuwa jingim a tattare da furucinsa"ni na ma rasa abin da zan ce, gabaɗaya lissafina ya katse". Dafo kafaɗarsa Saifullah ya yi cikin salon ƙarfafa masa gwiwa ya soma faɗin"haka Allah ya ƙaddara Umar, sannan ko wani Bawa ba ya wuce ƙaddararsa a rayuwa. Wataƙila Allah bai ƙaddara akwai aure tsakanina da Amatullah ba. Mu ƴan Adam ne kawai muke lissafinmu amma tun kafin wanzuwan mu a bayan ƙasa ya rubuta abin da zai kasance da Bawa, mussamman a sha'anin aure ka san an ce wani ba ya auran matar wani". Anty Zulaihatu kam kasa jurewa ta yi ta tashi ta bar cikin falon ta na matsar ƙwalla, daga bisani ma Umar tashi ya yi ya fita.
Ban taɓa zato da tunanin cewa tashin hankali idan ya girmama ba a ma samun damar zubar da ƙwalla ba, sai da na tsinci kaina cikin wannan matsanancin halin. Duk yadda na so na zubar da hawaye na kasa yin hakan idanuna ya bushe ya soye tamkar na soyayyan kifin da aka tsamo daga cikin mai.
Na yi nisa cikin tunanin da na dulmiya a cikinsa na tsinkayo muryarsa dab da ni da hakan ya ba ni tabbacin cewar ya sauya wajen zama ya dawo kusa da inda nake zaune.
"Amatullah kin ga yadda Allah ya yi da mu ko? Aure tsakanina da ke ba zai yiyuwa. Ƙaddara ta shata mana layi a tsakaninmu ta yi mana katanga daga cika burinmu na mallakan juna a matsayin ma'aurata. Sai dai daman kullum a cikin roƙon Allah muke yi ya yi mana zaɓi mafi zama alkhairi a gare mu, tun da hakan ya wanzu a tsakaninmu sai mu ɗauka cewar hakan ne alkhairi a gare mu bakiɗaya da mu da iyayenmu har ma da al'umma".
Ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba daga inda ya tsaya"Allah ne shaida cewan na so ki tsananin son da ban taɓa zato ko tunanin zan iya yi wa wata ɗiya mace ba, na yi burin aurenki na yi ɗamarar kasacewa da ke har ƙarshen rayuwa amma Allah bai nufa faruwan hakan ba, ina yi miki fata da addu'ar samun miji na gari wanda ya fi ni komai da komai wanda zai kula da ke ya riƙe ki amana kuma bisa adalci. Idan ki ka sama wanda zai zo ki ya ƙaunace ki domin Allah tabbas zan kasance cikin kwanciyar hankali a duk inda nake, wataƙila wannan shi ne zuwa na a ƙarshe cikin gidan nan da zummar zuwa wajen ki mu yi hirar saurayi da budurwa, sai dai na zo a matsayin wanda ya zo ziyara da kuma sada zumunci".
Sai a lokacin hawaye suka zubo daga idanuna sa'ilin da na ga ya miƙe na kuma tabbatar da cewa da gaske tafiyan zan yi, tafiyan da yake daidai da tarwatsewar tubalin ginin da na yi wa rayuwa.
"Shi kenan tafiya za ka yi? Shi ke nan komai ya zo ƙarshe a tsakaninmu? Daman haka soyayyar take? Da na san haka ne da ban fara da na san hakan zafin rabuwan yake da ban saki jiki mun saba da kai ba Saif. Sai dai haka Allah ya ƙaddara yadda kake yi mini fatan alkhairi ni ma ina yi maka irin wannan fatan". Sai da na miƙe tsaye na zo gabansa na tsaya mu na kallon juna kana na ci gaba da maganar cikin zubar da hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatan fuskana kamar ana watsa mini garwashin wuta.
"Tabbas na shaida cewar kai ɗin mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, ka sama matsayi a cikin zuciyata irin matsayin da babu wani ɗa na mijin da ya taɓa samun irinsa. Saifullah ina sonka amma ƙaddara ta tsara dole mu haƙura da juna". Kukan da ya gama cin ƙarfina ya tursass mini yin shuru ba don na rasa abin faɗa ba.
"Wallahi Amatullah da akwai wani hanyar da mu iya yin aure tabbas da zai na bi wannan hanyar, amma dole mu haƙura sa boda maslahan rayuwarmu da kuma ƴaƴan da za mu haifa har ma da kwanciyar hankali iyaye da ƴan uwanmu. Kar mu bari soyayya da burin mallakan junanmu ya rufe mana idanuna har mun jefa rayuwar ƴaƴan da za mu haifa cikin garari, wallahi cutar nan cuta ce mai matuƙar wahala ga kuma ɗawainiyya. Ina sonki wannan dalilin ya sanya ba zan iya jefa rayuwarki cikin ƙuncin ba, Amatullah ba don ba na sonki zan tafi sai don maslahan rayuwarmu kuma ina fatan Anty ma ta fahimci hakan. Allah ya ba ki miji na gari wanda zai ƙauna ce ki domin Allah".
Yana dasa aya a nan ya juya ya fice daga cikin falon da kallo na bi shi har ya fita kafin na durƙushe akan gwiwoyina ina wani irin azababben kuka mai ciwo. Har sai da Anty Zulaihatu ta fito ta same ni a wajen ita kuka ni kuka haka muka mayar da gidan tamkar gidan mutuwa, sai bayan sallan magrib Yaya Alhassan da Amir suka dawo Anty Zulaihatu ta shaida musu abin da yake faru, lamarin ya jijjiga su ainun don da aka sanar da su zancen Yaya Alhassan sai da ya nema wajen ya zauna sa boda jirin da yake ɗibansa. Sai da suka yi da gaske kafin suka fahimtar da Anty Sawwama illolin da yake tattare da duk wani aure da aka gina shi akan irin wanan turban, daren ranar mun sha kuka har sai da muka goge wa Allah, Anty Sawwama ta ce tun da haka ya kasance Yaya Alhassan ya ƙira gobe gobe su zo su amshi kayansu da suka kawo. Haka kuwa aka yi aka mayar musu da kayan.
Ranar Amira da Mansur suka zo muka wuni muna jajantawa juna lamarin sai bayan sallan magri suka tafi, na shiga damuwa matuƙa mussamman idan na ɗaga wayata ban iske ƙiran Saif sai na ji duk duniyar ta yi mini zafi har na rasa inda zan tsoma kaina na yi salama. Haka zan zagaya na shiga banɗaki na yi kuka na gode wa Allah na wanke fuskana kana na fito.
Tun bayan faruwan lamarin ba ma yin dogon magana da Saif sau ɗaya muke yin waya da shi a wuni shi ma da safe ne sai ƙira ni, mu gaisa ya ce daman ya ƙira don ya ji lafiyata shi kenan kuma sai washe gari, Hajiya Muhibbat ma ta ƙira muka jajanta lamarin sosai har da kukanmu shaɓe-shaɓe tamkar waɗanda aka yi wa wani gagarumin rasuwa.
Haka aka yi sati biyu da faruwar lamarin lokacin da Allah ya nufa saura sati É—aya a yi bikin, a daren wani ranan juma'a Anty Sawwama ta tara mu a falo gabaÉ—ayanmu bayan sallan magrib har da mijin Anty Zulaihatu da ya zo É—aukan ta kasancewar ranar ta wuni a gida.
Amir ne ya buÉ—e taron da addu'a kafin Anty Sawwama ta soma amayar da dalilin da ya sa ta tara mu duka a wajen.
"Na tara ku a nan ne gabaɗaya sa boda na sanar da ku hukuncin da na yanke wanda nake tunani da hashashe zai zamo alkhairi gare mu ba ki ɗaya. Amatullah amana ce a gare ni sannan zan ƙara jadadda muku ko bayan raina ku riƙe ta amana ku yi dukkan abin da zai faranta mata rai don neman rahamar Allah kasacewarta marainiya. Ko a iya rashin iyayenta aka tsaya haƙiƙa Amatu ta shiga jarabawar rayuwa balle kuma a haɗa da ragowar jarabawan da ta faɗa a cikin rayuwarta, ina so na yanke hukuncin da nake da yaƙinin cewar ba zai cutar da ɗaya daga cikin mu, ina so lokacin da aka sanya auren Amatullah kar a ɗaga shi".
"Auren Amatullah kuma? Ta sama wani mijin ne?".
Amir ya yi zancen cikin tsagwaron mamakin da ya bayyana har a cikin furucinsa. Anty Zulaihatu ma ta amshe zancen"Umma aure yanzu kam sai dai mu yi addu'ar Allah ya kawo mata miji na gari".
"Ni ma dai haka nake gani, in sha Allah miji ɗaya dai kam Allah ba zai hana ta ba". Yaya Mu'azzam ya sanya baki cikin maganan a karo na farko, Yaya Alhassan k bai iya cewa komai illa ƙasa da ya yi da kansa har zuwa lokacin da Anty Sawwama ta ɗaura da zancen.
"Ina so a cikin daren nan a É—aura auren Alhassan da Amatullah bayan an an iddar da sallan isha'i. Alla ba shi sai ta tare a lokacin da aka sanya bikin watau sati mai zuwa".
Ina da yaƙinin duk cikinmu babu wanda ya yi zaton abin da zai fito daga bakin Anty Sawwama ke nan, mussamman ni da Yaya Alhassan da muka yi mutuwar zaune tsabar yadda maganar ta daki zuƙatanmu.