← Book details Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 72

Sashe 55

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya É—an yi jim kana ya ce"Amatullah ko da kun je asibiti babu abin da zai sauya daga abin da Allah ya rubuta zai hare ta". Da hanzari na tari numfashinsa"me ye kake nufi?".
"Sai dai haƙuri don ita kam ta riga mu gidan gaskiya, ta riga da ta amsa ƙiran Ubangijinta". Ji na yi komai na duniyar ya tsaya mini cak haka na zube akan gwiwoyina ki hawaye na kasa yi illa kafe Umma da na yi ido jikina ya na rawa, ƙasa-ƙasa nake ji yo sautin muryar Ustazu Abdulwahab sai dai ba na iya tantance abin da yake bakinsa yake furtawa balle har na fahimta. Ina nan kamar gunki na kasa motswa har izuwa lokacin da ya fita ya je ya ƙira matarsa suka dawo tare. Ita ta riƙe ni sa boda yadda jikina yake rawa ina ga ni Ustazu Abdulwahab ya rufe wa Umma idanunta da suka kafe sannan ya lulluɓe ta da zanin da ta lulluɓu da shi.

ÆŠakinta ta kai ni ta zaunar da ni sai na kasa yin komai, ba na iya yi ki da magana ba balle kuka. Idanuna ne kawai suke motsawa. Ban san adadin awannin da na É—auka zaune a wajen ba har zuwa lokacin da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka zo su. Duk kukan da na mutane suna yi akan gawan Umma ni ko hawaye na kasa yi.
Duk wanda ya zo ya ji labarin cewa na dawo gida ni yake tausayawa akan mutuwar Umma, sai dai ni kuma Allah cikin ikonsa ya saka mini wani nutsuwa na mussamman duk abin da ake faÉ—a ina ji sai dai ba na iya mayarwa. Har aka shirya Umma na je na yi mata addu'a ban yi kuka ba, sai da na ga an fito da ita za a fitar da ita waje don a yi mata salla. Ana É—aga makarar na yanke jiki na faÉ—i, sai farkawa na yi na ganni a cikin É—akin Anty Sawwama sai dai har zuwa wannan lokacin maganata ba ta dawo ba. Har aka yi kwanaki bakwai ba na iya yin magana ba na iya yin bacci ba na komai illa na zauna waje guda na yi shuru ni ba tunani nake yi ba, haka nan ni ba nazari ba.

Ranar da aka yi sadakan bakwai ina zaune Yaya Alhassan ya shigo ya same ni. Ya zauna kusa da ni yana kallona yayin da na yi ƙasa da idanuna.
"Amatullah". Ya ƙira sunan cikin sanyin murya mai cike da damuwa, kamar ya kunna wuta haka na ji hawaye suna zuba daga idona bakina ya fara rawa ina ta ƙoƙarin yin magana amma na kasa, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi nasaran faɗin"Yaya Alhassan shi kenan Umma ma ta tafi ta bar ni? Ba za mu sake gana wa ba? Me yasa Allah yake jarabta na da rasa dukkan mutanen da nake so? Allah na tuba na tuba ka yafe mini". Cikin wani irin cushewan amo na yi zancen ina ci gaba da fitar da hawayen da na shafe tsawon kwanaki ba tare da na yi su, bai hana ni yin kukan ba kamar yadda bai dakatar da ni ba illa idanun da ya zuba mini.
[12/21, 12:04 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

_______________________________________

Page 7️⃣5️⃣

Na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina yana sama yana ƙasa tamkar wacce aka sanya igiyan kirtani aka zarge min wuyana da shi. Haƙwarana suna karafɗiya da ruwa tamkar sabuwar haihuwar kazan da ruwan sama ta yi mata mungun bugu.
"Yaya Alhassan duniyar gabaɗaya ta fara ba ni tsoro komai na cikinta ya daina burge ni. Tabbas iyaye daban suke a cikin dukkan jerin mutanen shi kenan Abba ya tafi ya bar ni yanzu ma Umma ta bi shi, ina zan saka raina? Ina zan soma kaina na ji sanyi da sauƙin halin da nake ciki? Wallahi zuciyata zafi take yi mini raina yana tafasa tamkar ƙirjina zai fashe. Na daina samun bacci tunani ya yi mini yawa har ina tsoron zuwan wani rana da za su zo ku tarar da gawata a cikin ɗakin nan, zuciyata ya buga na mutu kowa ya huta".
"Ke Amatullah". Yaya Alhassan ya dakatar da ni cikin kakkauran amo, ban iya ɗaga ido na kalle shi ba illa rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa da na yi wasu hawaye su na ci gaba da ambaliya a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa tudun wuyana.
Sai da ya sassauta amonsa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah ki zama mai tawakkali, haƙuri da miƙa lamuranki ga Allahu malikulƙuddusu mana. Sarkin da ya yi mana alƙawarin komai tsanani yana tare da sauƙi haka nan komai duhun dare hasken alfirjir zai keto ya yi wannan baƙin duhun daren. Allah ba ya taɓa jarabtar Bawa da abin da ba zai iya ba don haka ki lallashi zuciyarki ki ba ta haƙuri akan wannan jarabawan da suka faru da ke. Ki sani Allah ya na tare da masu haƙuri kuma a ko wani irin yanayi su ne da riba. Zuciyata ta kan cika da rauni a duk lokacin da na zo na iske ki a cikin ɗakin nan kin yi shuru ki na tunani, zuciyata ta kan karaya a duk lokacin da na zo na tarar da ke ba kya iya furta komai illa kallo da ido. Amatullah ina jin ki har a cikin ƙasan raina ke ɗin ƴar uwata ce kuma jinina, duk wani abun da ya shafe ki ina ji kai tsaye tamkar ni ya shafa".

Shuru na yi ina ci gaba da sauraron zancen da ya ɗaura da su cikin sanyin amo da sigar lallashi"Amatullah ina ji a jikina in sha Allah rayuwarki za ta inganta. Matuƙar ina raye a cikin wannan duniyar ba zan taɓa bari ki yi kukan maraici ba, zan tsaya miki a cikin ko wani irin yanayi na daɗi ko akasin hakan. Zan yi amfani da gumina wajen ganin na faranta miki, ina so ki sama nutsuwa ki yi tunani da zuciyarki ki duba ki ga abin da kike ganin ya dace ki yi wanda zai taimaki rayuwarki, in ma karatu ne, sana'a ko kuma aure" . Babu shiri na ɗago kaina ina bin sa da kallo cikin rawar harshe na furta"aure kuma Yaya Alhassan?". Ya gyaɗa mini kansa cike da tabbatarwa ya ce"aure mana Amatullah me ye za ki zauna ki yi a cikin gidan? Ke fa yanzu ba yarinya ƙarama ba ce kin yi girman da kin mallaki hankalinki kanki. Aure shi ne rufin asirin ko wacce ɗiya mace komai gatanta, komai dukiyarta, komai iko da izzarta ke ko da kuwa uban ne ya fi kowa kuɗi a kaf cikin nahiyar Afrika da kewayenta aure shi ne cikar mutumcinta. Duk wani farin ciki, nutsuwa da kwanciyar hankalin mace ta na samunsa ne a cikin gidan aurenta amma idan ta yi dace da samun abokin zama na gari. Wanda ya san kima da darajarta". Bai gama maganar na dakatar da shi cikin faɗin"Yaya Alhassan to ni yanzu waye ma kake ganin zai iya aurena? Aure fa baban lamari ne alaƙa ce da in an ɗaura ta ake fatan ta ɗaure har zuwa ƙarshen numfashi. Ko Annabinmu cewa ya yi idan ɗayanku a tashi aure ya zaɓi ƴar gidan mutunci, mai kyakkyawan nasaba da asali, mu faɗa wa kanmu gaskiya duk waɗannan abubuwan babu su a tare da ni. Kar ka manta ta fa har ciki na yi ba tare da aure ba, na sa ƙafa na tafi can wata uwa duniya na yi zaman kaina. Idan tarihi da asali za a bi shi ma babu wani kyakykyawan abin da za a tarar, ko ka manta ni ce wannan ɗiyar da duk unguwa suka shaida cewan mahaifinyarta ta raina mahaifinta ba ta ganin kowa da gashi? Shin waye zai iya yin jihadin haɗa zuri'a da mace mai irin tarihina? Yaya Alhassan akwai hanyoyin bautawa Allah wanda duk wanda ka yi daga ciki da ikilashi zai kai ka zuwa aljanna, ba dole sai ta hanyar aure ba".

Tun da na soma zancen ya yi shuru yana ta kallona ba tare da ya ce komai ba har sai da na kai aya. Ya ja dogo numfashi ya fesar kafin ya furta"aure ya zama dole Amatullah. Shi zai goge duk wani mummunan abun da yake cikin tarihinki, aure ne zai ba ki damar hayyafa ta yanda ko bayan ranki za a ga zuri'arki a tuna da ke har a yi miki addu'a".

Cikin zubda ƙwalla na ce"akwai wani burin da nake so na cimma".
"Wani irin buri ne?". Kafin na kai ga ba shi amsa Umar ya yi sallama a ƙofar ɗakin duk muka juya muna kallonsa, Yaya Alhassan ne ya amsa masa sallamar da hakan ya ba shi damar shigowa ciki tare da cewa"Yaya daman baƙi aka yi, sun zo gaisuwa kuma sun ce su na buƙatar ganin Amatullah ita ma su yi mata gaisuwa".

"To koma ka ce ta na zuwa".

"To Yaya". Ya amsa da shi a taƙaice yana juya wa ya fita daga cikin ɗakin.
"Sai ki tashi ki shirya tun da kin ji akwai baƙin da suka zo gaisuwa ko?". Kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi damar tashi ya bi bayan Umar. Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu kafin na goge fuskana na ta saka hijabina na fito falon kaina a ƙasa. Can ƙasan maƙoshina na yi sallama Anty Sawwama ta amsa mini yayin da nake ƙarisowa na zauna kusa da ƙafafunta.
"Amatullah baƙi ne suka zo yi mana gaisuwar Hafsatu, shi ne suka buƙaci ganinki ke ma su yi miki gaisuwa". Sai a lokacin na ɗago kaina don ganin mutanen da ake magana akan su, take na ji zuffa ya keto mini ƙirjina ya buga da mungun ƙarfin bala'i.
Chapter 55 · 0% Book details