Sashe 63
Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abin da ya riga ya wuce ya wuce Amatullah ki fuskanci yau ɗinki da kuma abin da gobe za ta haifar. Rayuwa ta kan zo da abubuwan da mu ƴan Adam ba mu taɓa zato ba balle tsammanin faruwarsa. Duk wani kwanciyar hankali da nutsuwan da za ki sama ba zai kai na cikin gidan aurenki wanda za ki samu daga wajen mijinki ba".
Sai da na jinkirta ba ta amsa sa boda nauyin da bakina ya yi mini kafin can na ce"Anty kin mata da cewar Yaya Alhassan ma ya taɓa zuwa gare ni da irin wannan buƙatan? Shin ina ganin na kyauta masa idan na amince wa waninsa? Ki na tunanin na yi masa adalci na kuma saka masa idan na ba wa wani da muka haɗu da shi rana tsaka kyautar zuciyata alhali shi ya san dukkan ɗawainiyya ta?". Numfashi mai ƙarfi ta fesar daga bakinta kafin ta sama zarafin faɗin"Amatullah idan aka zo batu na aure ba na duba dangantaka, ba a duba kusanci, ba a duba alaƙa daɗaɗɗiya ko kuma sabuwa, haka nan ba a yin kara balle kawaici. Fito wa ake yi a fallasa sirrin da yake cikin zuciya ko da kuwa zuƙata da yawa za su ɗanɗana romon baƙin ciki. Don shi aure da kike gani ba zaman lokaci ɗaya ba ne, ba zan wuni guda ba ne zama ne na dogon zamani da ake fatan ya ɗaure har abada, kuskure mafi girma da mace za ta yi shi ne ta zaɓa abokin rayuwa wanda bai dace da ita ba to tabbas za ta dawwama ne cikin ƙunci da baƙin ciki. Don haka ina mai ba ki shawaran ki yi addu'a ki roƙi Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi tsakanin Yaya Alhassan ɗin da kuma wannan baƙo, duk wanda kika gabatar mana tabbas da shi za a yi mu zo mu sha biki har mu yi rawa da juyi".
Maganarta ta ƙarshe ta jefa ni a cikin kunya, na yi saurin ɗauke kaina daga saman kafaɗanta na rufe fuskana da tafukan hannayena na fice daga cikin ɗakin, ina jin ta tana dariya tare a ƙiran sunana amma kuma waigowa ban yi ba balle na tanka mata. Ina fito wa falo muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana shigowa take na sha jinin jikina na yi wani irin kunyarsa nauyinsa sun lulluɓe ni, na tako na iso cikin falon na gaishe shi yayin da yake zama akan ɗaya daga cikin kujerun da suke jere reras a falon.
"Yaya Alhassan daman ina ta so na yi maka godiya waya, sannan kuma akwai maganar da nake so mu tattaunawa da kai".
"Babu godiya tsakaninmu Amatullah kamar yadda ba zan cire kuɗi na yi wa Amir ko Umar da suke ƙannena ba tare da na yi komai a cikin raina ba, to ke ma haka nake tsintar kaina a cikin irin wannan yanayin a duk lokacin da na yi miki wani abu".
Kaina na jinjina cike da gamsuwa don ni ma katan kaina shaida ce akan irin tari soyyaya da kulawan da yake nuna mini da yau na gaza samun abin da zan saka musu da shi. Sai da na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyi kafin na zama zarafin faɗin"daman na so mu yi magana akan Saifullah da ya zo cikin gidan nan da buƙatan aurena idan har na amince". Ya yi hanzarin katse ni ba tare da na ƙarisa ba ta hanyar faɗin"wani magana za mu yi akan hakan? Ai idan har kin ji ya kwanta miki a cikin ranki to shi kenan kawai an gama magana".
"Na san da haka sai dai idan ba ka manta ba kai ma ta taɓa zuwa mini da makamancinyar irin wannan buƙatan a lokacin baya, sai nake ganin.......". Ya ɗaga mini hannu alamar ba dakata hakan aka yi kuwa na yi tsit tare da sadda kaina ƙasa.
"Wannan kuma wani abu ne da ya riga ya wuce bai dace ki na tuno shi a daidai irin wannan lokacin ba, na yarda duk abin da ban samu ba to haƙiƙa daman Allah bai ƙaddara cewa yana daga cikin rabona ba. Ina miki fatan samun rayuwa mai inganci ko ki na cikin gidana ko kuma ki na cikin gidan wani daban ba ni ba, burina ki sama farin ciki da kwanciyar hankali. Don haka ina ba ki shawaran ki zaɓa wanda hankalinki ya fi samun nutsuwa da shi, kika ji ya kwanta miki a cikin ranki. Zuciyarki ta nutsu da shi".
Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa a cikin ruwan gishiri, hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar da za su kwaranya har ya miƙe ban iya ɗago kaina ba balle na ce da shi wani abu, yana shirin fita daga cikin falon Anty Zulaihatu ta fito riƙe da wayata da take ta faman ruri a hannunta.
"Kin ga wayarki sai ƙira ake yi tun ɗazu".
Na amshi wayar cikin sanyin jiki tare da ɗaga ƙira na kara a kunnena yayin da nake koma cikin ɗakin na zauna a bakin katifan. Sallama ya yi na amsa muryata a dushashe daga haka gabaɗayanmu muka yi shuru.
"Daman na ƙira ne na ji ya ya kike da kuma yadda kika wayi gari". Kamar ina gabansa na gyaɗa masa kaina kafin na ce"lafiya ƙalau".
"To alhamdulillah a gaishe da mutanen gidan".
"Za su ji". Ban jira abin da zai kuma cewa ba na katse ƙiran tare da ajiyar wayar na fita daga cikin ɗakin. Kowa na tunkara da zancen Saifullah magana guda yake furta min shi ne na yi addu'a sannan na bi abin da zuciyata ta nutsu akan ta. A haka har aka cinye sati guda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da Saifullah ya riƙa ni ba duk ranar juma'a kuwa sai ya niƙo gari ya zo takanas ta kano gaishe da Anty Sawwama haka za su sha hiran su kafin ya tafi. Haka kawai ranar na tashi da kewan Amira na tambayi Anty Sawwama ta yarje mini zuwa gidan Amira tun da safe na buga shirina na zauna zaman jiran Yaya Alhassan don shi zai kai ni da mashin ɗinsa, da taimakon kwantancen da ta yi mini ranar da ta zo ta muka sama gidan. A ƙofar gidan Yaya Alhassan ya tsaya na shiga ciki na yi mata magana ta fito suka gaisa kana ya tafi bayan ya shaida mini cewar bayan sallan magrib zai zo ya ɗauke ni mu koma gida.
"Matar mijinta ki na sha'aninki a cikin gidan nan". Na yi zancen cikin sigar zolaya yayin da nake cire hijabina. Murmushin ta yi kafin ta ce"duk da tun da kika shigo annuri bai gushe daga kan fuskarki ba, amma hakan bai hana ni fahimtar cewar akwai abin da kike ɓoye wa a cikin ranki ba, Amatullah shin akwai wata matsalar ne?". Numfashi mai nisan zango na ja na fesar daga bakina kafin na cira kai ina kallonta na ce"Amira ke ma kin sa matsaloli ai ba ya ƙare wa, in dai da rayuwa to tabbas akwai jarabawa". Ta shimfiɗa masa tabarma a waje muka zauna kana na kwashe komai na sanar da ni don na yarda abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa haka nan abokin cin mushe ba ya ɓoye masa wuƙa.
Ta jajanta mini sosai kafin ta ce"ni fa Amatullah ina ganin kamar ki amince masa kawai, inda gaske yake sonki ya zo a yi auren a wuce wajen. Don kin gan ni nan wallahi yanzu ba na goyan bayan dogon soyayyan nan da ake yi a waje da za a shafe shekaru ana buga wa, gwara a yi auren duk soyayya da kulawan da za a ba wa juna ku yi shi a cikin gidanku".
Bushashshiyan murmushi na saka da ba shi da alaƙa da nishaɗi kafin na yi ƙarfin halin faɗin" ba na jin zan iya soyayya a yanzu haka, sai dai zan amshe shi ne kawai don cikar wani burina wanda a yanzu shi kaɗai zai iya taimaka mini". Babu shiri ta waro idanunta"wani buri ke nan?".
"Me ye abin da tada hankali haka? Sanin kanki ne dai ba zan aikata abin da yake na haramci ba ko?". Kanta ta jinjina cikin sanyin jiki ta soma cewa"haka ne kam to Allah ya shige mana gaba".
"Amin ya Allah" Na amsa da shi yayin da muka ci gaba hirar mu cike da kewar rayuwar da muka yi a gaba da takaicin yadda rayuwa ta yi mana atishawan tsakin barkono. Mun ba wa juna shawara akan abubuwa da yawa na rayuwar yau da kullum.Tare muka wuni da Amira da hakan ya yi mini matuƙar daɗi har na manta da tari damuwar da nake cikinsa sai da aka yi sallan magrib kafin ƙiran Yaya Alhassan ya shigo cikin wayata na ɗaga ya shaida mini cewar yana ƙofar gida, na tashi na miƙe tsaye ina faɗin"kin ga ni kam bari na wuce Yaya Alhassan yana waje yana jira na".
Cikin rashin jin daÉ—i ta furta" ga shi har za ki tafi Mansur bai dawo ba, na so a ce ya zo ya same ki wallahi".
"Ba komai kar ki wani damu ai zan dawo wataran. Yarinya ta Mansur sai na tuna irin zumuɗin da kike a da idan ya ƙira ki ya ce miki yana hanyar zuwa gida, ranar walwala da farin cikinki na daban ne. Haka ranan in muka je talle za ki ta zuba masa kamar kyauta".
Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"rayuwa fa ke nan ga shi yanzu komai ya wuce har ya zama labari".